Sashe 18
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Na san yar'uwarka ce Muhammad, Hameeda ma yar'uwarka ce kamar dai ita, a gidan nan ta tashi da kai ta bude ido bata da uwa da uba a yanzu shim idan bata samu farinciki a cikin gidan nan ba ina kake tunanin zata samu? Bata da sakewa idan tana jin motsinka, bata iya walwala idan kana kusa da ita, bayan acan baya ba haka kake da ita ba, kai kanka baka iya zama sai ka nemeta, wannan rashin fahimtar dake tsakaninku yana taba min zuciyata sosai da ace kasan abunda nake ji da ko harara junanku ba zaku yi ba...”
Dada Yalwa ta karasa idonta na cika da hawaye irin nasu na manya, gaskiya ta fada har cikin ranta take jin damuwa idan suka samu wani rashin jutuwa, duk kuwa da irin fadan da take masa tana dora masa laifi, idan ta gama fadan sai abun ya dawo mata a rai ya tsaya mata.
Tashi yai tsaye yana sauke ajiyar zuciya, maganganunta sun taba shi, musamman ma kwalla da suka cika masa ido.
“Zan je gurin aiki a can zan kwana saboda akwai aiki da yawa a asibitin.”
“Allah ya tsare”
“Amin”
Ya nufi kofa bayan ya amsa mata da amin din. A falonta ya samu Hameeda kwance saman doguwar kujera idanuwanta a lumshe hawaye ya sauko mata ta gefen ido. Kamshin turarensa da taji ne yasa tai saurin bude idon ta tashi zaune ta share hawayen ta nufi dakin Dada Yalwa.
Ya dade tsaye jikin kofar falon kamin ya bude ya fice, jikinsa duk yayi sanyi da damuwar da ya gani a fuskar Dada da kuma hawayen Hameeda, hakan yana nufin tayi nadama kenan kuma ta daina son shi, domin idan har zai iya tunawa rabon daya ga hawaye a idon Hameeda da sunan damuwa kamar haka tun mutuwar Haleema.
Har ya shiga part din Mai Martaba tunanin yake ta yi, A falon ya samu Mai Martaba zaune yana kallon labarai, Hajiya Hadiza na zaune gafensa tana masa fira kasancewar ita ke da girki yau. Kasa Zain ya fadi ya kwashi gaisuwa sannan ya gaisheda Hajiya Hadiza, sai kuma yai shiru yana kallon tv.
Shirun da yai ne yasa Hajiya ta kalleshi ta ce
“Kana da bukatar wani abun ne?”
“Aa daman zan fadawa Mai Martaba ne cewar yau a asibiti zan kwana saboda aiki yayi min yawa”
A hankali Mai Martaba ya juyo ya kalleshi shi kuma sai yai saurin sadda kansa kasa ya kasa hada ido da Mai Martaba, kallonsa sosai Mai Martaba keyi yana karantarsa, a iya saninsa Zain be saba masa karya ba, sai dai yau alamu ya nuna babu gaskiya a cikin maganarsa.
“Tashi kaje kar dare ya maka...”
Mai Martaba ya fada bayan ya dauke kansa daga kallon da yake masa. Cikin hanzari Zain ya tashi tsaye yana fadin
“Na gode Mai Martaba Allah kara maka lafiya”
Hajiya Hadiza ce ta amsa da Amin, shi kuma ya fice daga falon ba tare da ya sake kallon Mai Martaba.
Sai da ya busar da iskar bakinsa sannan ya bude motarsa ya shiga ya dauki hanyar asibitin. Sai da ya biya gurin masu kayan marmari ya siya sannan ya karasa asibitin, a gurin da aka tanada dan aje motarsa ya aje motar ya fito ya nufi sashen da zai sadashi da dakin da Hafsatu manga take ciki. A tunaninsa zai samuta a farke ne kuma tare da Doc Hafsat sai ya sameta tana bachi Doc Ibrahim yana tsaye jikin gadon.
“Ina Hafsat taje...?”
Ibrahim ya kalleshi ya ce
“Aikin Hafsat kula da marar lafiya ba jinya ba, ya kamata ka san da wannan, amman duk da haka ta tsaya ta kula maka da ita, kiranta akai hakan yasa ta kirani ta fada min kuma ta bukaci na zauna da ita kar kazo baka tararda ita ba kace zaka koreta ko ka mata wani abun...”
Hannunsa ya kai ya taba gefen fuskarta.
“Yanzu yarinyar nan ta zame maka lalura Yarima wa zai kula maka da ita...?”
Bayan kamar minti uku da yin tambayar sai Zain ya amsa masa.
“Ni zan kwana a nan...”
“Baka saba kwana a asibiti ba, komai dare sai ka koma gida, ko kuma ka taso tsakar daren kaxo nan kai aikinka, baka tunanin zasu zargi wani abu idan kace musu zaka kwana a nan, kasan yadda gidanku suke saka idonka akanka fa”
“Na fadawa Mai Martaba aiki ya min yawa”
“Be kamata ka masa karya ba Yarima”
“Saboda...?”
“Zata rushe wani percentage na aminci da yarda da kima da ke tsakaninka da Mai Martaba, kar kuskure yasa ka rushe wannan ginen da ke tsakaninku, ina ji maka tsoron abunda zai biyo baya”
Sai a lokacin Yarima Zain ya dago ya kalleshi.
“Baka tunanin na yi girman da zan rika yin gaban kaina? Am old enough to decide my future, a kullum Mai Martaba da Dada suna min kallon karamin yaro ne, su suke zartarmin da abunda zanyi, Mai Martaba yana samin ido sosai hakan yasa ya hanani zama a gidana bayan na yi aure ya cilasta min zama a masarautarsa”
“Amman kuma sai ka masa karya?”
Zain ya karaso ya dafa kafadar abokinsa.
“Akwai inda karya ta halatta Ibrahim, na san ni kadai ne da namiji a gurin Mai Martaba amman bana jindadin yadda yake controlling dina kamar mace, kuma yarinyar tana bukatar wanda zai zauna da ita”
“Amman ai yafi dacewa ka fada masa wata yarinya zaka kula da ita...”
Zain ya yi murmushi irin wannan dake tsayawa a fatar baki.
“Kai kadai ka kai haka Ibrahim, kai kadai ka isa na fada ka fada, kai ma kasan haka, a tarbiyar gidanmu idan Mai Martaba ko iyayenmu suna magana bama cewa uffan har sai sun gama, baya su kuma babu wanda ya isa ya mana fada sai dai mu yi masa, kuma dole ya sauraremu ba zai tanka ba har sai an masa izinin haka, balle kuma har ya yi sa'inda da mu ko ya gardanta min akan wani abu”
Hannunsa yasa aljihu ya ciro keys din motarsa ya mika ma Ibrahim.
“Ka ba wani ya shigo min da kayan Marmarin dake cikin mota ta”
Kallonsa kawai Ibrahim yai ya karbi makullin ya dauke kai, a yadda ya fuskanta ran Zain ya soma baci matukar ya cigaba da maganar ba zasu kwashe lafiya ba, ko da yake sun saba fadansu kuma su shirya kansu idan ya fada masa wata magana da bata masa dadi ba, yana jin rashin kyautawa a abunda Zain yake kokarin yi ko ma yai, domin zai taba kamarsa a gurin Mai Martaba matukar ya gane gaskiya.
AUWAL POV.
Hannu biyu ya saka ya dafe kansa, idanuwansa sun kade sun yi masa ja sosai kansa sai sarawa yake, sai a yanzu zuciyarsa ke raya masa abunda yai ma Farhat be kyauta mata ba, tun daga lokacin daya samu labarin mutuwar Yayarta sai tausayinta ya rufe shi, ya kasa misalta irin halin da zata shiga idan babu shi babu yayarta a rayuwarta, ya san irin son da take masa yasan yadda ta dauke shi a rayuwarta, shi ma kansa karya yake ya ce baya son ta wata mace bata taba shiga ransa kamar yadda farhat ta samu guri a zuciyarsa ta zauna ba.
“Auwal... ”
Ya dago ya kalli Momy data kira sunansa.
“Daman can kai kaso ka saka kanka ciki matsala tunda kasan mahaifinka ba zai taba canja alkawarinsa ba, amman kaje ka dinga soyayya da yarinyar nan ka yaudareta, haka ka zo ka cilasta mana zuwa gidansu kuma a dauko ta a kawo ta”
“Nayi tunanin Abbah zai canja ra'ayinsa ne, ban dauka abun zai kai haka ba”
“Taya zai canja ra'ayinsa bayan yasan kai da Sanaya kuna son junanku, kuma wannan alkawarin ya dade fa tun uban yarinyar nan yana da rai, yanzu kuma dan ya rasu sai mahaifinka ya canja alkawarin? Kai kanka ai mai taimaka masa ne ya cika ko”
“Amman Momy nafi son Farhat Wallahi, tafi dacewa da ni mun gama tsara komai, kuma na ce ki nema min alfarma ki sake roka min shi ya yarda na auresu tare”
“Yace ba zai yi ba, mi zaisa na cilasta masa? Ni bana da wani abun da zan iya ce maka bayan abu daya, kaje ka lallabata idan ta yarda zata jiraka nan da shekara daya sai ka aureta”
Baki ya saki yana kallon Momynsa, sai kuma ya maida dubansa gurin Doc Hafsat data shigo yanzu.
“Tsabar iskanci tun dazu nake jiranki shine kika samu guri kika zauna ni kika barni nan ko?”
“Wallahi aa Dsp na tsaya wani dan aiki ne wata yarinya ce aka sa na kula da ita, amman ga takardun na kawo”
Wani banzan tsaki yaja ya fisgi takardun a hannunta ya fice a fusace. Ita dai da kallo ta bishi tana ta mamakin wannan fushin nashi na yau.
“Momy lafiya danki yake kuwa?”
“Kyaleshi haushin tsohuwar budurwarsa ne yake son ya sauke a kanki”
Ta tabe baki daman tana cikin mutanen da basa son ya auri Farhat.
ANTY UMMI POV.
Tun da safe Abban Amal ya bar gidan, daman ya kanyi fitar safe but ba kamar wannan karom ba, domin ya fita da bacin ran matarsa wato Anty Ummi sakamakon maganar dawowa da Farhat a gidanta ta tai masa, ita ma dai ta tashi cikin damuwa da tunanin yadda zata samawa Farhat mafita, har ga Allah abun ya dameta sosai domin tana yi ma Farhat daukar yar'uwarta ne ko kuma ma yar cikinta gaba daya. Hakan yasa yaranta ma gaba daya basu gane kanta ba, bata wani sake musu fuska ba har suka shirya motar makaranta ta wuce da su.
Da taimakon Mai aikinta suka shirya abinci mai yawa aka bawa Malam Adamu ya kai, ita kuma ta shiga ciki tai wanka ta shirya cikin wata shudiyar atamfa. Zuwa tai falo ta zauna da zimmar karyawa amman ta kasa sai tunani take. Tana haka taji tsayawar motar Zain agogon falon ta kalla 10:38am ya nuna, dan haka ta san daga gida yake daman kamar kullum ko ya karya a gida sai ya zo gidan wani lokacin kuma sai ya baro gidansu ya xo nan ya karya.
Da sallama ya shigo falon ta dago ta kalleshi tare da amsa masa cikin yanayin damuwa.
“Yanzu nake tunaninka Zain”
“Ni...?”