Sashe 64
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Nima haka na ga ya dace gaskiya, zan sa abincika mana a kadunar amman ka sama mana addirensa ta yadda zamu san ta inda zamu fara”
“Zan samo inshallah, kuma ina son a sallami Isma'il yau”
“Na yi tunanin yin hakan tuntuni, kawai dai bana son maka katsa landan ne shiyasa na kyale”
Ya tashi tsaye tare da nufar kofar fita yana fadin.
“Ina da aiki a ciki”
Kwantawa Zain yai jikin kujerar yana kallon air conditioner dake tsaye ta can farkon shigowa katon office din.
*** *** ***
Tana tsaye jikin windows ta hango shigowarsa, a gurin ta kasa ta tsare saboda mugun kudirin da take da shi har ya gama abunda zai yi ya fito ya shiga motarsa ya fita. Sai ta dawo kuryar dakin ta bude bedside drawer dinta ta dauko wani abu a gora mai kamar rubutu ta saka a kugunta sannan ta dauki Hijab dinta ta saka ta fito daga dakin ta sauko kasa cikin rashin natsuwa da faduwar gaba ta bar part dinsu ta nufi Part din Zain, wata zuciyar na raya mata ko dai ta koma ta ba Abida ta zuba mata? Sai kuma ta tuna shirmenta zata iya cewa tana jin tsoro ko kuma ta ce Farhat din ta hanata shiga.
A waje ta tsaya tana kallon bakin kofar kamar ta zuba abun a nan, sai kuma taji tsoro wani ya ganta kasancewar duka dakunansu sama suke duk wanda ke sama zai iya hango na kasa ko da ba a part din yake ba. Musamman ma su da suke kusa sosai da part din Zain, idan ta watsa a nan wata kila daya daga cikin sisters dinsa su gani. Hakan yasa tai knocked din kofar sai waiga waige take kamar mai tsoro a tararda ita a gurin ta kusan minti goma tsaye a gurin har zata sake knocked sai kuma ta kai hannu ta tura kofar falon sai ta bude, ashe daman abude take, ganin falon babu kowa yasa ta jidadin hakan sai dai tana fargabar karta fito ta ganta wata kila ma tana kitchen ko dakinta.
Ko da Hameeda ta shigo falon Farhat na ciki tana wanka, taji lokacin da akai knocked din hakan yasa tai saurin fitowa daga wankan, bata tsaya shafa komai ba ta zira zane da riga ta nufo kofar fita domin taji lokacin da aka turo kofar falon, a bakin kofar bedroom din ta tsaya tana kallon Hameeda wacce take ta aikin barbada wani abu a hanyar Kitchen tare dayan hannunta rike da gorar rubutu mamaki ne ya hana Farhat motsin kirki bare har tace wani abun. Juyawa tai ta koma dakinta ta dauki wayarta ta shiga message tana tsara sakon da zata aikatasa zan.
_Ka yi sauri ka zo ga Hameeda nan tana zuba magani a kofar kitchen amman bata san na ganta ba_
Har zata tura sai kuma ta fasa ta saka sakon a draft, ta fito daga gurin message din ta shiga contacts sai ta tuna bata da number Zain daman can bata da number barre yanzu da aka mata welcome back na line wasu numbobin basu dawo ba.
Hakan yasa ta yanke shawarar daukar ta a video da sauri ta shiga, camera ta danna video recording ta fito rike da wayar tana dauka har lokacin Hameeda na nan tana zubawa sai dai yanzu a dinning area take watsawa. Takun saukowar Farhat ne ya dago da ita tai saurin kallon stairs din.
“Me kike aikatawa Hameeda? Magani kike zuba mana bayan sherin da kika ma Zain? Hakan be isheki ba sai kin kara da magani? Wai ana so dole ne? Yace baya ra'ayinki miyasa ba zaki kyaleshi ba?”
Farhat ta fada tana kara sauta wayarta tana daukarta da kyau. Hameeda kam ta tsaya a gurin kamar an dasata.
“Yanzu Kan komai ya kare, kowa sai yasan abunda kike aikawata, sai na fallasa komai tun daga kan siyar da yarinyar kauyen nan da kika yi? Da kuma sherin da kika bi Anty Ummi da shi na cewar ta sace yarinya, da kuma sherin da kika ma Zain kika zuba masa abu a fuska kika sumar da shi kika cw yayi raping dinki, sai na tona miki asiri a cikin gidan nan, sai Dada da Mai Martaba sun gane Wacece ke, kuma sai masarautar nan ta san zamanki a tare da su hatsari ne, kin ga wannan video da nake dauka sai na nuna kowa abunda kika aikata shi zai zama shaidata, kin ga dole ne Mai Martaba zai zama zaman lafiya da kwanciyar hankalin dansa ko kuma zama da mace makira irinki, Dada ma da kanta sai ta kyamace ki dan ba zata taba son abunda zai cutar da Zain ba, tana miki kallo mai kirki bata san ke makira ba ce”
Muryar Farhat kamar tana fada da Hafsatu manga taji ne yasa tai saurin fito daga dakin ta zo bakin kofa ta tsaya tana kallon Farhat din wacce tuni ta kai kasa hannunta rike da waya tana dauka Hameeda, Hafsatu manga na hango Hameeda gabanta ya fadi sai kallon tsoro take mata duk kuwa da kasancewar ita Hameeda bata ganta ba, ba zata taba manta fuskarta ba, ita ce wanda ta tsareta tare da dan sanda nan a lokacin da suka laka mata iyayen karya.
Baya baya Hameeda ke yi tana hawayen tashin hankali Farhat kuma na kara matsawa kusa da ita tana cigaba da daukarka, duk da irin sanyin ac da falon yake da shi hakan be hana Hameeda hada gumin tashin hankali ba, gaba daya ta rikice numfashinta har sarkewa yake. From head to toe Farhat ta sake daukarta sannan ta juyo tana fadin.
“Yanzu kam asirinki ya tonu ba zan kyaleki ba wannan karon abunda kike yabisa haka”
Hameeda ta bude baki ta saki abunda ke hannunta sai kuma ta daga hannun kamar zata kira Farhat sai ta kasa, ta hade yawun bakinta tana wani irin wahaltaccen numfashi wanda ya ki shiga sai dai ta fitar da wanda ke ciki, waiga tai bayanta ta kalli dinning din, idonta ya sauka kan wukar dake gurin da sauri ta kai hannu ta dauka ta yo kan Farhat.
“Bayanki bayanki”
Hafsatu manga ta fada tana ihu tare da rike kai. Farhat na juyowa Hameeda ta suka mata wukar iya karfinta ta jata, ba shiri Farhat ta saki wayarta ta fadi kasa ita tama ta fadi baki bude tana fada hannu saman dayan hannunta kuma na kan wukar. Hameeda ta yi saurin daukar wayar ta tsallaketa ta fice da gudu daga falon.
Wani irin kara Hafsatu manga ta saka ta dafe kanta ta duke a gurin, sai kuma ta sauko da gudu ta yo kan Farhat, duk irin tsoron hawa da sauka stairs da take yau kam ta manta da shi, hawayen da taga suna zuba a idon Farhat ne yasa ta kai hannu tana kuka zata cire nata wukar....
Cikin rashin natsuwa da kwanciyar hankali ta dawo part dinta, bakin gadonta ta zauna tasa hannayentata rufe bakinta tana hawayen.
“Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, na shiga uku, na sake kashe rai na kashe *RAI BIYU* asirina zai tonu”
Tayi saurin daukar wayar ashe har yanzu video kunne yake, cikin sauri ta danna red button wato stop ta video ya daina dauka sai ta shiga gallery da zimmar goge video but unfortunately suka nuna mata ta saka password.
“Na shiga uku”
Ta jefar da wayar, sai kuma tai saurin daukar wayar ta kashe ta daga katifarta ta aje wayar a gurin, sannan na nufi windows tana leken part din Zain, gumi sai zubar mata yake cikinta na mugun murdawa, jinginawa tai a gurin.
“Mi na aikata na shiga uku, na bani na lalace wayyo Allah na”
Ta fada tana kuka. Kamar an tsikareta sai kuma tai saurin tashi ta nufi inda wayarta take ta dauka ta kira Abida tana kokarin daidaita muryarta.
“Ki shiga gurin Farhat tana son ganinki Yanzun nan”
Bata jira abunda Abida zata ce mata ba ta kashe wayar, ta fashe fashewa da kuka....
[3/21, 8:54 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660*
I repeat don't read my novel if you didn't pay.
46.
Ganin ba za ta iya cire mata wukar ba, yasa ta tashi da gudu tana kuka ta nufi kofar fita, bata karasa ba Abida ta turo kofar falon ta shigo, sai Hafsatu manga ta kasa magana sai nuna mata Farhat take tana hade yawu da karfi numfashinta na tashi sama sama. Abida bata fahimci abunda Hafsatu manga take magana akai ba, har sai da ta karasa kusa da ita sai ta dora hannu saman kai ta kurma wani uban ihu.
“Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, na yi mugun gani, kasheta kikai?”
Ta karasa tana kallon Hafsatu manga, kai Hafsatu ta girgiza mata tana kuka. Sai Abida ta fita da gudu tana ihu da kiran jama'a, can bayan kujeara Hafsatu manga ta koma ta rabe ta yadda ba za a ganta ba, ta fashe da kika. Kururuwan Abida ce ta fito da kowa dake cikin gidan fito waje ciki har da Hameeda wacce ta gama fita natsuwarta. Sai a aka dunguma aka nufo part din Zain.
Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un kowa ke fadi, Hajiya Hadiza ce ta sa a dauki Farhat a kai asibiti, Sapna kuma ta kira Zain ta sanar da shi halin da ake ciki.
“A kira police su tafi da ita, wannan yarinya annoba ce”
Cewar Dada idonta na cika da hawaye, wasu na mamakin yadda Hafsatu manga za ta cakawa Farhat, yayinda wasu kuma suke mamakin ita din wace irin yarinya ce daga kawo ta jiya jiya yau tai wannan aika aikar, dukan wasu kananan maganganu a tsakanin yan gidan yake tashi. Mai Martaba ne ya aiko da kansa cewar kowa ya watse, a dole kowa ya kama gabansa, aka ja kofar part din aka rufe Hafsatu manga na ciki.