← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 93

Sashe 1

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*HAFSATU MANGA
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

Assalamu alaikum Habibaties, fatar duk kuna lafiya 😍 Na sake dowowa da labarin kauye kuma labarin sarauta mai suna HAFSATU MANGA 👌
Labari ne mai cike da kauyanci, ban dariya, sarauta da kuma makirci.

Happy reading 😍

_____________________________________

1⃣

A hakali ta sauko saman Motar fuskarta ɗauke da damuwa.

"Na gode"

Ta furta murya ƙasa-ƙasa kamar mai shirin yin kuka. Dattijon da ta yi ma godiyar ya ciro wata tsohuwar naira ɗari ya miƙa mata yana faɗin

"Karɓi wannan ki siye abinci"

Sai da ta share hawayen da suka zubo mata sannan tasa hannu biyu ta karɓa tana masa godiya

"Na gode Allah ya saka maka da alheri"

"Babu komai Allah yayi miki mafita"

Cewar Dattijon, mutanen da ke cikin Motar suka amsa da

"Amin"

Sannan Dattijon ya tashi Motar suka hau titin unguwar Gada biyu, titin da zai sada su da tsakiyar birnin Gusau.
Da kallo ta bi Motar itacen, hawaye na bin fuskarta, sai da ta daina hango Motar sannan ta maida dubanta gurin manyan gidajen da suke gabanta, wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da kuka mai ƙarfi, kukan da bata san ta ina yake fito mata ba, kukan da ba ta san ranar tsayawarsa ba, hawayen da babu mai share mata su, sai Ubangijin daya ƙaddaro mata rayuwar da ta tsinci kanta ciki.
Ba ta damu da rashin takalminta ba, ta cira ƙafafunta cikin rashin kuzar tana ɗingishi ta nufi wata ƴar kwarkwaɗar data hango wadda ke tsakankanin gida da gida, cikin kwarkwaɗar ta shige ta zauna saman simintin dake gurin sai ta fashe ta sabon kuka muryar a daƙishe saboda majinar data kama maƙoshinta.

Kuka take mai tsuma zuciyar mai sauraro, kuka mai ban tausayi, kukan rashin Uwa da Uba, kukan rashin ƴan'uwa da abokan rayuwa, kukan rayuwar da ta samu kanta da kuma wanda zata zo mata nan gaba, kukan rashin sanin makomarta, kukan baron duniyar jindaɗi, duniyar dake cike da masoyanta da abonkan rayuwarta, lokaci ɗaya komai ya tsarwatse mata ta rasa komai nata, yau gata cikin duniyar da bata san kowa ba.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga uku na bani na lalace, wayyo ni Allah na"

Ta furta hakan yafi a ƙirga kamin kuka ya ci ƙarfinta, ta ɗauki tsawon lokaci a gurin tana kuka ba tare da kowa ya kula ba, kasancewar unguwar manyan mutane ce, ba kasafai za ka ga mutane a unguwar ba, sai Motacin dake kai da kawo suma kuma ba sosai ba, mutane dake tafiya da ƙafa kuma tsinta-tsinta ne kowa na sha'anin gabansa, ba kowa ba ne zai kula da gurin da take zaune balle har a iya gano da mutun a gurin kasancewar yamma tayi sosai.

Hakan ya bata damar tausayawa kanta, ta ci kukanta har ta gode Allah ba tare da kowa yaji ba.
Kiran Sallah Magariba ne ya saukar mata da natsuwa har ta samu damar jan numfashi ta lumshe ido tana sauraren Ladani tana girgiza kai. Yau Magariba tayi mata ba'a gida ba, wasu zazzafan hawaye ne suka fito daga idonta dake rufe suka gangaro zuwa kumatunta.
A she kayi kuka a kula da kai a baka haƙuri gata ne, ji take kamar wani ya zo ya dafata ya rarrasheta kamar yadda mahaifiyarta take mata a duk lokacin da take kuka, amman ina! Yau ta rasa wannan gatan, lokaci ɗaya haske ya zame mata duhu, fari ya koma mata baƙi duniyarta ta barkace ta zo mata bai-bai, ji take kamar ita kaɗai ce ta rage a duniya, jikinta na bata wani yanayi na daban komai ganinsa take kamar mafarki.

Sai daf da ƙare Sallah Magariba sannan ta fyace majinar data ɓata mata fuska, ba ta damu da share hawayen ba, ta fito daga kwarkwaɗar tana cigaba da ɗingishi.
Hanyar dake damanta ta kallah kamin hagu, sai shawartar zuciyarta take gurin zuwa, ga kanta babu ko ɗankwali, zane da rigar dake jikinta ma ko wanne daban-daban ne kamar wata sabuwar haukaciya.
Cikin unguwar ta kutsa kai, ba dan tasan inda za ta ba je ba, ita dai tafiya kawai take tana kalle-kallen manyan gidaje. Tafiya ta riƙayi har ta kusa kaiwa ƙarshen unguwar bata ga gidan da zata iya shiga roƙon mayafi ba balle abinci, a ƙofar wani ƙaton gida ta tsaya tana ƙare masa kallo, babban gida ne da aka ƙawata shi da ƙwayaƙwan lantarki, a gefen gidan kuma an yi masa kwalliya da fulawoyi masu kyau da ɗaukar hankali.

A tunaninta babu mutane a gidan haka zuciyarta ta nasalta mata, gurin da fulawoyin suke ta nufa, kasancewarsu ba masu tsawo sosai ba, ya bata damar tsallakawa ta shiga ɗan filin dake tsakanin fulawoyin da kuma ginar gidan, zaunawa tayi a gurin zuciyarta cike da rauni da zullumin abunda zai same ta.

Ɗaya bayan ɗaya tunanin ƴan gidansu ya soma dawo mata, nan take kanta ya fara sarawa tana son kuka amman ba hawaye, a haka ta gaji ta kwanta a gurin sauro na bin ƙafafunta da hannayenta, ba a ɗauki dogon lokaci ba bachi ya yi gaba da ita.

Bachinta bai kai na mintuna ashirin ba, aka buɗe ƙofar gidan da ƙarfi, hakan yayi sanadin tashinta a firgice har tana ƙoƙarin yin ihu, a zatonta mutane da suka kawo musu wacan harin ne suka sake dawowa, ɗan bachin da ta yi yasa ta manta da inda take, da sauri ta fito daga cikin fulawoyin tana haƙi.
Daga mai gadin har yaran gidan sakar mata ido suka yi, kowa kallon mahaukaciya yake mata, bama kamar mai gadin da ya haske ta da fitilar hannu.

"Ke bar nan gurin"

Mai gadin ya faɗa a tsawace. A maimakon tayi magana sai kawai ta fashe da kuka ta juya a firgice ta nufi sashen wasu gidajen, ba dan tasan inda zata ba sai dan kawai tayi nisa da gurin da mai gadin yake dan ta tsorata da yanayinsa sosai.
A ƙofar wani gidan ta zauna tana cigaba da kukan, bata tuna ta jefar da naira ɗarin dake hannunta ba, har sai da cikinta ya fara kukan yunwa da ƙishin ruwa a lokaci ɗaya, wani irin murɗa cikin yake mata hanjinta na kukan yuwanwa, ji take idan bata ci abinci a yanzu ba za ta iya mutuwa, duƙawa ta yi a gurin ta matse cikinta ta rumtse ido.

______________________________

Labarin Masarautar Rishim da kuma Kauyen Kufawa. Labarine mai cike da sarkakiya, ban dariya, kauyanci, kurciyar Hafsat, tausayi, tashin hankali da dai sauransu

[2/19, 9:46 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

2⃣

Komawa tai can gefe ta zauna hawaye na bin fuskarta, kuka take son yi amman babu muryar kukan saboda rashin kuzari dake tattare da ita. Dama ta fara dubawa kamin ta duba hagu kamar mai tunanin inda zata je. Tana haka aka bude katon gate din take gefenta ta firgita sosai abun ka da bakauye sai kawai ta ranta cikin na kare ta koma can bayan kwarkwadar ta buya tana lekon mutumen daya fito daga cikin gidan ya doshi wata hanyar daban dan shi be ma kula da ita ba. Sai ta tabbatar yai nisa sannan ta fito tana tafiya a hankali sai waige waige take har ta isa bakin gate din, baki sake ta kai hannu ta tura kofar gate din sai ta jita a bude sai dai tai kara lokacin da ta turan din, hakan yasa ta sake arcewa kai kace ma biyota aka yi, babu komai a cikin zuciyarta sai tsoro da fargaba, cikinta kuma dauke da yunwa da kishin ruwa.

Ganin babu sarki sai Allah yasa ta sake komawa duk kuwa da irin abunda zuciyarta take raya mata na cewar kille mata kai za'ayi a wannan gidan dan yai mata kama da na yan yankan kai, a hankali ta saka kanta ta leka harabar gidan, a yadda ta hango compound din sai yasa idanuwanta suka fiffito kamar wata zarrariya baki sake take kallon motocin dake harabar gurin.
Tabbas gidan yan yankan kai ne, haka zuciyarta ke raya mata, sai dai hakan be sa ta zata iya komawa ba tare da ta nemi abunda zata jefa a cikinta ba duk da bata dan inda zata samoshi ba. Kamar ance ta juyo tana juyowa ta hango kofar Kitchen bude sai dai ita din bata iya banbance kitchen ne ko kuma wani abun na daban.
Hango mutum na kallonta ta window yasa ta juyo har tana kokarin faduwa ta fita da gudu tana haki.

“Na bani na lalace wacan aljanin nasu ya hango ne”

Ta fashe da kuka sosai tana gudu iya karfinta duk da babu wani kuzari a tare da ita. Bayan wacan kwarkwadar ta sake komawa ta buya tana kuka babu hawaye, kwarkwada ce dake tsakanin gida da gida baka jin sautin komai sai iskar da ke kadawa, hakan ya bata damar tausayawa kanta da kanta tai kuka iya wanda take jin zai isheta amman ko kadan hawaye be zubo daga idonta ba. Lokaci lokaci tana shafa fuskarta wai ko zata ji saukar hawayen tun da bata ji sanyinshi ba, amman sai taji babu komai.

“Hawayena ma har ya kare... ”

Ta fada tana kara fashewa da kukan still babu hawaye.

YARIMA ZAIN POV.
Chapter 1 · 0% Book details