← Book details Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 95

Sashe 81

Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maimakon ya sake fa
a mini cewa yana sona.

Ya sake cewa "INA SON KI, Zeeyadah" saboda na ji sassaucin abinda na ke ji a raina sai ya ja baya.

"Ban san me zan yi ki yarda dani ba, Zeeyadah" ya fa
a muryasa a karye.

Ka ce kana sona.

Ka ce na yafe maka.

Ka ce na yi ha
uri.

Ka ce ba ka son Cassandra, ni kake so.

Bai fa
i ko
aya daga cikin abinda nake tunanin zai fa
a ba.

Bai ce komai ba.

Sai ya juya ya je ya fara saka kayansa.

So nake na je na rungumeshi na bashi ha
uri.

Amma sai ga
aina suka
i motsawa.

Ba ni ce zan bashi ha
uri ba.

Shi ya kamata ya bani ha
uri.

Shi ya kamata ya lalla
ani.

Ko juyowa bai yi ya kalleni ba ya saka kayansa ya fita daga
akin.

A karon farko sai na sake jin so da
aunarsa yana shigata.

Ina son Jalal, har yanzu ina son Jalal.

Kwanciya na yi a bakin gado ina jinyar zuciyata da kuma tsakiyar cinyoyina dake mini zogi...
*JAYKAY*
Iya gaskiyarta ya gani lokacin da take zarginsa da cewa zai tafi ya barta saboda Cassandra.

Bai san da wani yare zai bayyana mata irin soyayyar da yake mata da za ta fahimce shi ba.

He's madly in love with her.

Wata
ila soyayyar ce bai iya ba.

Wata
ila kuma ya gaza ne wajen nuna soyayyar ta sa a fili.

Ba ya so ya cigaba da sauraron maganganunta masu
aci shi ya sa ya yi shiru ya bar mata
akin.

Ta ya za ta zarge shi da kawai son jikinta yake?.

A shekarunsa ya fi
arfin ya yi mata
aryar abunda ba shine a zuciyarsa ba.

Bai fa
a mata kalmar SO ba har sai da ya gama tabbatarwa kansa cewa soyayyar da yake mata ba ta sha'awa bace.

Shi yasa tun da aka
aura musu aure ya ke binta a sannu saboda ta nitsu da shi ta san cewa ba jikinta ne ya saka shi aurota ba.

Bai san yaushe ya fara sonta ba.

Wata
ila ta samu shiga zuciyarsa ne a ranan da ta masa masifar ita 'yar Ghetto ce kuma tana alfahari da inda ta fito.

Wata
ila kuma a ranan da ya kaita kallon Hawan Sallah ne.

Wata
ila ma a ranan da ya fara ganinta ne.
e kansa ya yi da ke mugun sara masa.

Mummunan fahimtar da ta masa ya fi komai
aga masa hankali yanzu.

Wata
ila lokaci take bu
ata da za ta huce.

Zai bata lokaci.

Shima kuma zai je London ya yi maganin matsalar Cassandra once and for all.

Ya sani idan har Kotu ta tabbatar da SAKI tsakaninsa da Cassandra to tabbas Ziyada za ta yarda da gaskiyarsa.

Duk da yana son komawa
akinta ya rungumeta ya bata ha
uri, ya cuddling
inta ta ji sau
in wahalar da ya bata
azu sai ya hana kansa hakan saboda kada komawarsa
akin ya sake sakata hawaye.

Hawayenta kuma yana mugun
ona masa rai.
arfe shabiyu na rana bayan ya gama shiryawa sai ya wuce
akin Ziyadah, bacci ta ke yi saboda dama ya samu kira daga Jide akan ta kira ta ce ba za ta samu fitowa ba su yi handling Gidan Girki da kansu.

Ajiye mata wani envelope ya yi a gefen wardrobe dake gefen gadonta ya manna mata light kiss ya fita daga
akin.

Direbansa ne ya wuce da shi Abuja inda daga nan zai hau Jirgi ya tafi London.

A halin yanzu ba zai iya fuskantar Hajiya ba tareda ya dawo da Muhammad ba.

Sannan ba zai iya fuskantar Ziyada ba tareda ya saki Cassandra ba.

Lokacin da jirginsu ya tashi gangan jikinsa ne ke cikin jirgin amma zuciyarsa tana Nigeria.

Tunaninsa yana Zaria, sannan farincikinsa yana gurin Ziyadah..
*ZEEY*
aran waya ne ya tasheni daga baccin da na yi bayan na sha kukan tafiyar Jalal.

Hajiya ke kirana.

Yanayin muryata da ta ji a dashe ya sa ta tambayeni ko lafiya?

Na ce mata kaina ke ciwo.

Ta min sannu sannan ta ce za ta shigo ta duba ni.

Jama'a in sau
o da
afata in mi
e sai fa tashi ya gagareni.
afafuwana ne suka yi tsami.

Sai yanzu aikin Jalal ya fara tasiri a kaina.
azu da safe ban ji wahalar tashi sosai ba.

Da
arfina na shiga ban
aki na yi wanka.

Ikon Allah!

Na mi
e da
yar ina tafiya ina
an bu
afafuna kamar wacce aka yiwa kaciya.

In zauna in yi fitsari sai na ji wani zogi ta
asana.

Innalillahi!

Da
yar na yi tsarki ina
an rintse idanuna saboda zafi.

Na yi Alwala na fito.

Sallaya na shimfi
a na yi sallar Azahar a tsaye da
yar.

Na zauna ina Istigfari.
arfe biyar saura na sauko
asa lokacin da Hajiya ta kirani wai ta iso.

Sai dana sauko
asa sannan na gyara tafiyata saboda kar Hajiya ta gane akwai matsala.

Na ajiye murmushi a fiskata na bu
ofar.

"Ya jikin naki?" Ta tambaya lokacin da muka zauna.

"Da sau
i, Hajiya" na amsa ina murmushi amma ni ka
ai na san ciwon da nake ji a jikina.

Na tambayeta me zan kawo mata ta ce ba sai na yi wahala ba.

Anjima ka
an ma Hassana za ta kawo min abinci.

Na yi mata godiya.

"A can Restaurant dai babu wata matsala ko?"
Na ce mata lokacin dana kira Jide dai yace babu matsala.

Ta ce mini Alhamdulillah, Allah ya
aro kasuwa.

"Jalal, ya wuce ko?"
Na yi shiru dan ban san ko yana nan ko ya tafi ba.

Sadda na tashi daga barci ta kaina na yi ba ta tasa ba.

"Na san tafiyarsa ba zai miki da
i ba.

Amma dole ne ya je ya kar
o Muhammad kuma ya warware aurensa da Cassandra.

Idan ba rashin hankali irin nasa ba, wani irin zaman aure ne yana zaune a Nigeria tana can London sai ta ga dama ta zo.

Allah ka
ai ya san me ta ke yi a bayan idonsa dan yarinyar kwata-kwata bata da kamun kai"
Jin Hajiya na
orafi akan Cassandra sai na ji da
i a raina.

Ashe dai ina da tudun dafawa.

Haka dai ta yi ta kwantar min da Hankali ta ce mini idan ba zan iya zama ni
aya ba in tattaro in dawo gidanta.

Na yi shiru dan gaskiya bana so in je gidanta a halin da nake ciki.

Tunda Jalal baya gidan gara na zauna na yi jinyar kaina ba tareda takura ba.

Da ta ga kamar bana so sai ta ce babu matsala in zauna
in dama Jalal
ya mata magana za ta sa a kawo min 'yar aiki da za ta ri
a tayani kwana.

Na yi mata godiya amma na ce ba sai an kawo 'yar aiki ba, tunda a Gidan Girki zan ri
a wuni ma.

Gabanin Magariba Hajiya ta tafi.

Da za ta wuce na tambayeta ina Janan ta ce tana can tana ta shirye-shirye Mijin da za ta aura zai shigo Nigeria a satin nan.

Na ce mata ta gaisheta.

Bayan tafiyarta ban bar falon bama na zauna ina
an kallo sai can ga Hassana ta iso.

Ta gaisheni sannan ta kai min kwandon abincin kan dining.

Bata wani tsaya ba ta tafi.

Daga nan na je dining na bu
e kulolin abincin na
ebi abinda zan iya ci na zauna a wajen ina ci ina tunanin Jalal.

Ko ya isa London
in?.

Ko sun ha
u da Cassandra?.

Ko da gaske rabuwa zai yi da itan?

Allah ne ka
ai masani...
*JAYKAY*
"JLove" Cassandra ta fa
a lokacin da ta bu
ewa Jalal
ofa.

Wani kallon tsana ya mata.

"Where's my Son?" Ya tambaya da
arfi.

Juyawa ta yi ta barshi a bakin
ofa tana fa
in idan Junior ya zo nema to baya nan.

Sake tambayarta ina yaron yake ya yi amma ta shareshi.

Ya wuce upstairs da sauri ko bin bayansa ba ta yi ba.

Jalal ya bu
akin Junior ya ga wayam babu yaron.

Ya je
akinsa da suke kwana da Cassandra nan ma babu kowa.

"Where is he?" Ya fa
a da
arfi lokacin da ya sau
asa ya samu Cassandra tana zaune a kujera ta
aura
afa
aya akan
aya.

Ka shirya magana kenan?

Ta fa
a ko a jikinta da yadda ya haukace da bai ga Junior a gidan ba.

Ta ce masa ai ba zai ta
a ganin yaron ba har sai ya dawo hayyacinsa.

"Stop playing games with me, Cassandra.

Where's my Son?".

Ya daka mata tsawa.
an ja da baya ta yi a tsorace.

Ganin haka sai ya dam
e hannunsa yana furzar da iska.

Tunzura shi Cassandra ke son yi saboda ya yi abinda zai
ata komai.

Ba a Nigeria suke ba.

Kira
aya za ta yi Police su zo gidan.
ura ya yi da tambayarta ina Junior ya fita ya bar mata gidan.

Gidansu na London ya wuce wanda a yanzu ya koma Masauki ga duk wani
an Familyn Maiya
i da zai zo London.

Wani lokaci ko ba a cikin Family ba idan aka nemi alfarma suna bada aron gidan wa ba
i 'yan Nigeria.

House keeper
insu ka
ai ya samu a gidan.

Dake tsohuwar tana aikinta yadda ya kamata duk da bai fa
a mata zai shigo ba tsaf-tsaf ya samu gidan.

Gidan yana da dogon tarihi a gareshi.

A gidan suka taso shi da Jamal.

Daddynsu ya sayi gidan ne lokacin yana shekara 7 a Duniya shi kuma Jamal yana shekara 4.

Haka za su yita wasa shi da Jamal a gidan suna rigimarsu.

Idan ka ga suna wasa sai kace 'yanbiyu ne ba wa da
ani ba.

Kwatsam bayan sun gama tunanin su biyu ne ka
ai a wajen iyayensu sai Hajiya ta haifo musu Janan.

Ba zai ta
a manta ranan da Daddynsu ya fa
a musu Hajiya tana da ciki ba.

Ya dawo daga Makaranta ne ya samu Hajiya bata da lafiya sun je Asibiti.

Da suka dawo kuma Daddy ya musu Albishir da cikin Hajiya.

A lokacin Hajiya sai
ata fuska take har tana cewa me yasa zai fa
awa yaran daga zuwansu.
Chapter 81 · 0% Book details