← Book details Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 95

Sashe 50

Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ce mata ya yi ta turo yaro waje ya zo ya kar
a mata sa
Ya jira kusan minti biyar kafin wasu yara su biyu suka zo wajen motarsa.
*ZEEY*
Lokacin da Amir da Mu'azu suka kawo mini sa
on Jalal ina kwance akan gado na yi rub da ciki na sa pillow a ta cikina.

"Kaka, miye a ciki?" Na tambaya dan ita ta kar
i ledan.

Ita ta kira min yaran ma dan ruwa ya hanasu shigowa sashenmu su ci tuwon dare.
an matso da kaina bakin gado ina kallon abinda Kaka ke fitarwa.

Ta fito da gwangwanin Milo, Madara...

Subhanallahi!.

Na tashi da sauri na sauka a gadon na
au pack
in Always da Kaka ta fitar na mayar cikin ledar.

"Kaka a gaban yaran nan fa"
"Ku wuce ku tafi" na fatattakesu.

Wato so suke su ga abinda aka kawo su kai wa Iyayensu gulmata.

Sai da yaran suka fita sannan na
au ledar na hau gado da shi.

Da wayar hannuna na dinga haska ledar ina duba kayan ciki.

Kaka tana min tsiya wai idan akwai Kaza in fito da shi za ta ci.

Wai Ango ya iya dubiya.

Ni dai ban kulata ba.

Uban wa ya ce masa ya siyo min pad har kala uku?.

Uban wa ma yace masa ya siya min pad?.

Haba dan Allah.

Sauran kayan shayi ne a ciki.

Madara, Bournvita da Milo.

Manyan slize bread guda biyu.

Sai wani packet na dabino.

Uban wa ya fa
a masa idan ina period ina iya cin abinci.

Sai kuma wata zuciyar ta ce mini.

But Ziyada it means he cares...

He cares about me... sai na ji na yafe masa laifin siyo mini Pad da ya yi.

Yau Jalal ya nuna damuwa a kaina.

Tun a cikin mota da ciwon mara ya sani a gaba na ga ya rikice da halin da nake ciki.

Har da shiga cikin ruwa ya siyo min pain reliever.

He cares...

Amma kuma da farko ya bani haushi.

Nufinsa bai san me mace take nufi ba idan tana ciwon ciki ta bu
aci shan pain reliever?

Wata zuciyar ta ce
ila Baturiyar matarsa bata yi.

And Maybe Janan ma baya mata haka.

Amma duk da haka.

Ya kamata a ce ya sani tunda shi ba yaro bane.

Sai wajajen goma saura na dare da aka gama ruwa sannan na saka ruwan zafi a gas na je na yi wanka.

Anty Red bata iso ba, amma ba mamaki ta min saukar tsakar dare ko Asuba.

Bayan na yi wanka sai na yi Alwala na zo na gabatar da sallolin da suka wuce ni.

Abincin dana zo da shima ba iya ci na yi ba.

Kaka ce ta ci.

Sauran kuma ta adana sai da safe.

Kiran Jalal ne ya tasheni da sassafe bayan Asuba.

Na yi mamaki da na ga period
ina bai zo cikin dare ba.

Lokacin dana
auka sai ya min ya jiki, na ce masa da sau
"Ki zauna a gida ki huta.

Zan kira Jide na fa
a masa sai next week za ki cigaba da aikin"
"Amma fa yau ne
arshe.

Kuma ba jimawa za a yi ba"
"Zeeyaadah" ya kira sunana da serious voice.

"Iya abinda kuka
auka ya isa.

Daga baya idan akwai bu
atan hakan sai ku cigaba"
"To, na ji" na fa
a a hankali.

"Kin ga abinda na tura miki jiya?"
"Ni Dan Allah ka dena sakani jin kunyar ka.

Kuma kawai sai ka je ka siyo abinda ba a sakaka ba.

Ce maka aka yi bani da shi"
Sautin murmushinsa na ji kafin ya ce"ki duba Whatsapp
inki"
"Aww!

Ashe..." na cire wayar a kunnena na kunna data na shiga Whatsapp.

"Ki duba videos
innan da kyau.

And please take care of yourself, kin ji"
Rufe bakina na yi ina girgiza kai.

Na fara scrolling videos da articles da Jalal ya tura mini duk akan abubuwan da mace za ta yi idan tana ciwon cikin period.

Har da tutorial na yadda za ka ri
a compressing cikinka da ruwan zafi.

Lallai kam!

To an gaya masa ban san duka wa
annan bane.

Ya wani kama ya cika min waya da tarin videos da rubutu.

Inama na ke da lokacin karanta wani article akan period cramps.

Abun da tun sama da shekara goma ake fama da shi kam ai na san ya nake managing kaina.

Na tashi daga inda nake kwance.

Muna da class guda
aya yau da safe.

Tunda an ce ba zan
arisa aikin shooting content ba, zan je class
in kawai.

Sannan dama ina so na je na ga project Supervisor na dan har yanzu bai approving min topic ba.

Cikin kayan tea da Jalal ya aiko jiya na ha
a tea mai kauri babu sugar na sha.

Na sha pain reliever guda biyu na saka sauran a jaka.

Da shirina na fito in case Anty Red ta kawo mini ziyara ina cikin school.

Na sake saka extra pad, a jaka just incase.

Kun san dai wannan abun shegen abu ne.

Yana iya baka mamaki a koda yaushe.

Na yi sallama da Kaka na fito zan wuce school.

Ina cikin tafiya na ji muryan yaro na kirana.

"Adda Ziya, Adda Ziya" na juya na ga Faru
ne
an Baffa Zakari.

"Wai ki je Baba Babba yana kiranki"
Baba Babba, Baffa Lawalli kenan.

Haka yawanci 'yan yara-yaran gidan ke kiransa.

Na ja
aramar tsaki dan na san sai ya
ata min lokaci.

Na wuce sashensu.
an waken siyarwa na ga
aya daga cikin matansa tana yi.

Ko yaushe ma aka fara a gidan ni ban sani ba.

"Ina Ziyadatun take ne?" Baffa Lawalli ya fa
a yana le
o kai daga
ofar
akinsa.

"Gata nan zuwa" 'yarsa Ummiyo ta fa
"Ina kwana, Baba" na gaishe shi lokacin dana shiga
akinsa.

"Lafiya" ya amsa fiskarsa babu fara'a.

"Gobe Wakilan yaron nan Jalal za su zo.

A yadda muka tsara za su kawo sadaki ne da abubuwan da ake bu
ata na al'ada sai a saka rana."
aga murya ya ce "Amma ni ban gane al
iblar mutumin da kika kawo mana ba"
Didish!

Wani irin magana ne wannan?

Ana gobe Asabat wakilan Jalal za su zo Dan Allah.

"Yaron nan har office
insa na je na yi masa wata magana mai mahimmanci amma duk sadda na kira shi baya
aukar wayata.

Haka yake so mu bashi ke.

Bayan bai san darajar Iyayenki ba"
Ya Subhanallahi!

Ba dai ku
i ya je ro
an Jalal ba.

Shi ya sa na yi mamaki da ranan Jalal ya tambayeni ko akwai ku
in da Alhaji Rabi'u kamar yadda yake kiran Alhaji Nafi'u yake bina.

Na fa
a masa babu.

Amma kaman ya ce yana bin su Baffa Lawalli ku
i masu yawa, kusan dubu
ari biyar.

Bai ce komai ba bayan na masa bayanin.

Nima kuma ban kawo komai akai ba.

"Alhaji Nafi'u mutumin nan hannunsa a bu
e yake.

Alkhairi kan Alkhairi idan ya zo gidan nan.

Amma shi wannan sai dai ya barka da dubu biyar ku
in mota.

Uban me dubu biyar zata mini.

Ga shi zai zo gidan nan yana cikin mota ba zai sauko ya zo ya gaishe da mutane ba.

Amma ya iya kiran yara ya saka su kwaso mishi leda su kai miki cikin gida"
To, to, to.

Wato har an masa gulman abinda ya faru jiya.

To ma wai Fisabilillahi ana cikin ruwan zai ce a kira masa mutanen gidan zai gaishesu ne?.

Babu kowa fa a waje sanda ya kawoni gida jiya saboda ruwa.

"Ko ce masa aka yi ke ka
ai ce a gidan.

Ba ki fa
a masa kina da
anne bane?.

Duka yaran gidan nan
annenki ne fa.

Ke ce babba a cikin yara mata a gidan nan"
Na yi shiru ina danne maganar dake taho mini.

"Ko ba ke bace babba?"
"Ni ce" na fa
a a hankali.
an yi shiru ya sosa kansa sannan ya ce "yanzu dai nawa kuka yi da shi zai kawo sadaki?"
Nawa muka yi da shi zai kawo Sadaki kuma?.

Abin ciniki ne?

"Baba, na barshi ne ya kawo abinda ya sawwa
a" na fa
a ina kallon fiskarsa.

Mutumin nan dai ya rantse sai ya kunyata gidanmu a wajen Jalal.

Allah ya sa kar ya yi abin kunya a gaban mutanen da za su zo gobe.

Ga shi 'yan'uwan Jalal manyan mutane ne.

"Abinda ya sawwa
a kuma?.

Ke ba ki san kina da damar da za ki fa
i adadin ku
i ko dukiyar da kike so a matsayin Sadaki bane.

Idan ma baki sani ba shi mai arzi
i ne.

Dan haka tun yau ki fa
a masa gobe fa Sadakinki kada ya gaza Miliyan
aya.

Kina jina?"
Dariya ne ya taho min.

Yo maganarsa ai abar dariya ce.

Haka kawai sai na kira Jalal na ce "Hello, Jalal.

Wai in ji yayan Babana kada ku kawo Sadaki
asa da Naira Miliyan
aya".

"Kina jina dai?" Ya sake maimaitawa.

"Na ji Baba.

Zan wuce Makaranta" na mi
e tun ma kafin ya sake
aro wata maganar da zai sa na
ura masa ashar.

Na ga alama idan ban masa hakan ba ba zai fita a harkata ba.

Dama na san saboda ya ga Jalal ya fi Alhaji Nafi'u ku
i ya saka shi ha
ura da batun Alhaji Nafi'un.

To yanzu kuma ya je ya yiwa Jalal maula bai kulashi ba.

Shine yake cewa Alhaji Nafi'u ya fi Jalal alkhairi.

Na fito daga sashensu raina a
ace.

Da
acin rai na isa school.

Ban san wace tsiyar Baffa Lawalli zai kawo ba idan Wakilan Jalal suka zo gobe.

Duk da dai Baffa Adamu ne zai jagoranci zaman amma ina tsoron abinda kwa
ayayyen tsohon nan zai iya yi.

Ku ji fa.

Wai na ce kada a kawo sadaki
asa da Miliyan
aya.

A'a, su siyar dani kawai na san cewa aurena da Jalal shi zai kawo masa
arshen Talauci.

Mtssw!

A da na yi niyyar yau zan fa
awa Faty za a kawo Sadakina.

Sai kawai na fasa.

Gara na bari idan an kawo
in komai ya tafi lafiya sai na fa
a mata.

Kai ciki bai kar
i Faty ba.
Chapter 50 · 0% Book details