← Book details Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 95

Sashe 39

Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na fi jin zan saka sunan Kaka.

To amma wannan wajen temporarily ne.

Ba zan samu mallakarsa gaba
aya ba har sai aurenmu da Jalal ya shekara kuma na gina wajen ya zauna da
afafunsa.

So saka sunan Kaka a wajen ba zai yiwu ba.

Balle ma yadda Jide ke ta nanata min mutanen da suke so su attracting masu ku
i da middle class mutane ne.

Dan haka na san ba za su yarda a sakawa wajen suna Fatima Altine ba.

Amma Insha Allahu watarana zan bu
aramin restaurant da sunan Kaka.

Jide yace tunda local cuisine za a ri
a serving mu nemi sunan da zai tafi da hakan.

Shi gogan aiki da calls kawai yake ta yi tun
azu.

Ni ban ma san me yasa ya biyo mu ba, dan duk bayanin da muke bai sa mana baki ba.

Occasionally dai za ka ga ya
ago ya kallemu.

Sunan GIDAN ABINCI ne ya zo mini.

Ina fa
a Jide yace perfect, sunan ya yi.

Sai kuma ya ce ba ri ya duba ko akwai restaurant mai irin sunan saboda kar a samu matsala.

"Shit!" Ya
an daki table
"Akwai irin sunan ko?"
"Wasu sun rigamu" ya fa
a yana girgiza kai dan sunan ya masa da
"What of GIDAN GIRKI?"
"Zeey, your brain is sharp ooo" ya
aga min thumbs up.

Na yi dariya.

Dariyar dana yi ya jawo hankalin Jalal ya bar wayar da ya ke a can gefe ya taho inda muke zaune.

Ya wani tambayi Jide cike da authority wai a ina muka tsaya?.

Jide yace masa mun samo sunan restaurant.

"So, what did you come up with?"
"GIDAN GIRKI" na fa
a da
arfi dan ya san nina za
i sunan.

"And sunan is available, Sir" Jide ya jaddada masa.

Ya kalleni sannan ya kalli Jide ya ce "Ku chanja"
Mu chanja?.

Mu chanja a wani dalili?.

"Sir, I think the name is unique, and it's suits the restaurant's core idea" Jide ya fara masa bayani.

"Gidan Girki yayi fa.

Ko Jide?" Na kalli Jide da ya fara rarraba ido tsakanin ni da Jalal.

Da gangan na yi hakan.

Akan me muna ta lissafi tun
azu bai sa mana baki ba yanzu kuma ya wani shigo wai a chanja sunan.

Jide ya ce "I think za mu iya tsayawa zuwa Agnes ta zo gobe before we decide, hope it's okay by you Sir?" Ya fa
a yana kallon Jalal.

Jalal ya
aga masa hannu.

Raina sai ya sake
aci.

Ni fa ban gane deal
innan ba.

Ta ya zai dinga yi mana katsalandan a duk abinda muke yi.

Idan bai yarda da ni ba, kuma bai yarda da staff
insa Jide ba, ai shikenan sai ya zauna yayi kayansa.

Haushinsa ya sa na mi
e na cewa Jide ni zan tafi.

Ma ha
u goben idan Agnes
in ta zo.

Jide yace ba matsala.

Har na fita bai yi kaman ya ji me nace
ba.

Ni anya ma za mu wanye lafiya da shi kuwa???.
*JAYKAY*
Jalal yana gani Ziyada ta
au jakarta ta fita.

Me yasa take da taurin kai ne.

Why the fuck is she so comfortable with Jide, daga ha
uwar kwana
aya.

First ta sake da shi suna ta
i a office.

Then yanzu kuma sun ha
e masa kai.

Shifa gani yake kaman sunan yayi local dayawa.

So yake ta tsaya ta masa bayani kaman yadda ta za
e tana yi da Jide but sai ta
au jakarta ta fita.

To wai mi yasa yake jin haushin sakewarta da Jide ne?.

Jide dama ko a office haka yake faran-faran da mutane.

Ita kuma she's just doing her job.

But aiki yace ta yi ba murmushi ko dariya ba.

Aiki ka
Bin bayanta yayi dan ba zai bari ta tafi gida ita ka
ai ba.

Da sauri ya fito ya shiga mota ya bar Plazar ya hangota tana tsaye tana jiran Keke.

Dai-dai inda take ya tsaya.

Yana gani tanata wani tsuke fuska irin ba zata shiga
innan ba.

He waited.

Patiently, ya jirata.

Tun da ya ha
u da yarinyar nan take saka shi jira.

Minti
aya ta yi tana masa jan aji kafin ta bu
ofar ta shigo.

Tana shiga ta fara magana.

"Na shiga motan kane ne dan kawai kar mu tara jama'a, amma da ba zan shiga ba.

Ehe"
Bai ce mata komai ba ta gama surutu har ta yi shiru ta juyar da fiskarta tana kallon window.

So yake ta cigaba da magana dan hakan yana saka shi nisha
"Gidan Girki sounds nice" ya fa
a yana
an kallon gefenta.

"Kan buhu.

Sai yanzu ne ka san sunan is nice.

Ba cewa ka yi mu chanja ba.

Tun da safe sai wani masifa kake ta mana sai ka ce wani 'ya'yanka.

Ai Wallahi
an Yarabawa nan ma na ga ha
urinsa.

Sai fa
a kake masa kaman wani
aramin yaro.

Har da cewa sai wata Agnes ta zo kafin a tsayar da magana.

Ba Agnes ba Agatha".

Ta yi shiru ta sake juyar da fiskarta.

Cikin
asan ransa murmushi yake.

He loves to see her talk, koda kuwa masifa take.

Those cute lips.

Watarana sai ya yi maganinsu...

CZ 27
*Paid Book.

Tsakani da Allah, ka biya kafin ka karanta*
*ZEEY*
Finally mai girma Yalla
ai Jalal Maiya
an Hajiya Layla ya amince mu yi amfani da sunan dana za
a, wato GIDAN GIRKI.

Yau kwana uku kenan ni da team
ina muna ta aiki.

Agnes ta zo, kuma itama tana jin sunan da muka za
a ta ce ya yi.

Ai dama na san son nuna mulki da iko yasa Jalal yace wai a chanja sunan.

Jide, shine aka barshi da bin procedure na registering sunan da CAC, da kuma trade marking
insa.

Ita kuma Agnes ita ce take handling designing logo na restaurant
in da kuma setting social media pages da sunan, saboda a nan zamu ri
a tallata restaurant
in idan aka bu
Ni kuma aka barni da creating Menu.

Dukkanmu mun yarda akan Menu
inmu na breakfast da lunch dama dinner ba zai yi yawa ba.

Za mu fara da ka
an, sai a gaba idan wajen ya kar
u sai mu
ara wasu abincin a Menu
Tunda Agnes ta fara zuwa Jalal ya dena biyo mu restaurant.

Da safe dai zai aiko min Direbansa
arfe tara ya
aukeni ya kaini Plaza.

A nan za mu ha
u da Jide da Agnes mu yi aiki.

Kwana biyun nan ma har yamma muke kaiwa saboda aiki.

Keke na ke hawa in koma gida duk da kuwa Jalal yace min idan na gama in kira shi zai saka Direbansa ya zo ya mayar dani gida.

Amma ban ta
a kiransa ba.

Jide, Agnes kawai yake
auka a motarsa.

Wai ba zai
aukeni a motarsa ba kar Oga Jalal ya koreshi a aiki.

Na ce masa akan me zai koreshi a aiki dan ya rage min hanya.

Ya ce babu ruwansa, ai nima na san dalili.

Ni kam ban san dalili ba.

Har Agnes ta shiga maganar tana tambayata miye tsakanina da Jalal?

Na ce mata babu.

Nima ban matsawa Jiden ba wani lokaci ma ni nake rigasu tafiya.

Ba yau na fara hawa Keke ba.

Mu mutanen Ghetto dama ai Keke shine Jeep
inmu.

Yau na kawo draft
in Menu da za mu yi amfani da shi a restaurant
in.

Muka ha
u dukkanmu uku aka tattauna yadda komai zai kasance.
arshe aka cire wasu daga ciki, wasu kuma aka pairing
insu da wasu side dishes
in saboda zai fi kawo ku
Next abinda za a yi shine Food testing.

Zan girka duka abincin da muka selecting a Menu
inmu saboda su Jide da kuma anonymous tasters
in da aka za
a su yi rating abincin.

Za su rating komai, tun daga taste
in abincin, har zuwa plating da presentation
insa.

A wannan wajen ake so na nuna bajintata.

Dan idan aka bu
e restaurant
in, abinci mai da
i shi zai tafiyar da wajen.

Ina da confidence akan na iya girki.

Amma duk da haka sai da na ji wani
ar da aka ce za a yi Food tasting
innan.

Muka rabu akan gobe za a kawo ingriedients zan dafa first batch na Menu
in sai na serving mutanen da za a gayyato su ci abincin.

Food tasting
in zai
auki kwana uku.

Dan haka kafin na tafi sai dana rubuta musu list
in abubuwan da nake bu
ata da zai covering girkin da zan yi na kwana uku.

Ina fitowa daga Plazar wayar Faty na shigowa.

Ta fara
orafin wai gashi har an kusa resuming school amma ban kawo mata ziyara ba kuma ta ce na zo na mata
anwake a gidanta na
i zuwa.
uri na bata na buge da tsokalarta Babynmu dai ke son cin
anwake ba ita ba.

Yadda ta fara dariya tana wallewa ita bata da komai na fahimci da gasken ciki ne da ita.

Na mata fatan alkhairi na ce ta yi ha
uri wani aiki ne ya ri
eni ba zan samu zuwa ba.

Amma zan sa Kaka ta mata
anwaken sai na sa yaro ya kai mata har gida.

Ta ce ba matsala.

Idan ba haka na yi ba kam bani da lokacin zuwa gidanta a yanzu da muke shirin kafa GIDAN GIRKI.

Da dare ina kwance akan gado amma bacci ya
aurace mini.

Kaka kam ita har ta fara bacci, amma ni gaba
aya tension ya sakani gaba.

Sai lissafi nake.

What if aka samu matsala suka ce ban iya girki ba.

Tabbas idan wa
anda aka gayyato suka ci abincina suka ce bai yi ba na san Jalal sai ya yi min dariya.

Cewa zai yi dama alfarma zai min amma ba zan iya running wajen ba.

"Kaka" na kira a hankali.

"Kaka" na
aga muryata ina ta
"Kaka dai"
"Na'amm" ta fa
a da muryan bacci.

Matsowa na yi jikinta sosai na ce "Kaka, miye sirrin sana'ar abinci?".

Na yi tambayar ne saboda for the first time a rayuwata da nake dab da jagorantar restaurant, ina jin tsoro.

What if experience
ina har yanzu bai kai na kar
i wannan aikin ba?.
Chapter 39 · 0% Book details