← Book details Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 95

Sashe 22

Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin dana fito yara sun fara shigowa za su ci
umame.

Gaba
ayansu babu wanda uniform
insa ke wanke.

Wai fa yau safiyar Monday, amma ji yaran nan da dau
a kamar an korosu daga bola.

Dole Baffa Lawalli ya yi ta zuba 'ya'ya mana, tunda ga Kaka Altine nan za ta ciyar masa da su.

Ga su nan
ananan duk safiya za su yi zuga su shigo mana sai Kaka ta basu
umame ko Kunu sun karya kafin su wuce Makaranta.

A baya har ku
in tara take basu, yanzu nema ta dena.

A hakan idan yaro ya yi mata kukan bashi da ku
in tara haka za ta shiga
aki ta
auko ta bashi.

Kar ku ce abincin safiya kawai suke zuwa ci.

Da rana idan ba su
oshi ba, Kaka ce wajen zuwansu su yi mata kuka ta bu
e tukunyarta ta basu.

In da a ce Kaka tana da ba
in halina ko, to da ko kukan mutuwa yaran nan za su yi sai dai su mutu amma ba zan basu abinci ba.

Ubansu da ya zubo su duniya ya ciyar da su su
oshi.

Amma Kaka akwaita da kawaici da tausayi.

Yanzu za ta fara wa'azin "wanda ka ciyar ai shine naka.

Wanda ka ci a cikinka kashi ne".

Shinkafa gwangwani biyu dan ni da ita dai zai ishemu, amma idan Kaka za ta dafa shinkafa sai ta dafa mudu guda (gwangwani 8).

Idan kayan abincinmu ya fara
arewa ne za ka ga ta dafa gwangwani hu
u ko shida.

Idan yara suka shigo sashenmu da rana aka ce babu abinci, to sun san ni Ziyada ce na yi girkin a ranan.

A da can baya, Maman Suwaiba ta ta
a kawo yaranta Ummiyo da Zainabu wai su ri
a kwana damu.

Ai tuni na koresu na ce
akin ba zai ishemu ba.

Kaka ta ce na barsu a shimfi
a musu wata
aramar katifa a
asa su ri
a kwana, na ce Wallahi bata isa ba.

Idan ta ce sai sun zauna a
akin zan bar gidan na koma Kaduna wajen Ummana.

Daga jin haka, sai ta ha
ura ta cewa Maman Suwaiba ba za ta kar
i yaran ba.

A hakan sai da suka yi ta ganin ba
in Kaka.

Wai mu biyu mun yi kane-kane a
aton
aki.

Oho dai ba za su zo su takura mana ba.

Ina ganin yadda yaran suka yanyame abincin da Kaka ta zuba musu suna ci kamar wanda suka yi 48 hours ba su ci abinci ba, na ja tsaki na shige
aki yunwar da ke cina ma na ji ya koma.

Ga munafukin Ubansu ya je ya ciwo bashi a gurin Alhaji Nafi'u, yana so ya muzgunawa rayuwata ta
arfi.

Wallahi idan kuka tambayeni wace sana'a Baffa Lawalli yake har ya auro mata uku, ban sani ba.

Gara Baffa Zakari gadi yake a Banki.

Baffa Adamu da ke Katsina
an Kasuwa ne yana siyar da su Hatsi da Masara.

Baffa Mamman Non Academic Staff ne a ABU.

Shi ka
ai ne cikinsu ke kar
an Salary.

Shi Baffa Lawalli da can muna yara na san dai yana gyaran Takalmi da Jaka a Kasuwa.

Daga baya har wankin hula yana yi.

Ya zo kuma wai yana dillanci.
arshe dai kame-kame kawai yake ba shi da sana'a guda
aya da yake.

Shi yasa kullum cikin cin bashi ya ke, da kuma maula.

An ce Kakana Malam Haruna Manomi ne sosai.

Da noma ya sayi babban fili ya gina gidan da muke ciki.

A
arshen rayuwarsa jinya ya hana shi yin noma.

Ya yi jinya sosai, dan Kaka ta ce ya kusa shekara shida yana kwance kafin Allah ya masa rasuwa.

Ya rasu ya bar gonakai da yawa, amma duka yaransa sai suka siyar suka
i yin noma.

An ce Manomi ba ya rasa abinda zai ci.

Tunda kuwa suka ce ba za su yi noma ba, shikenan suka
ulla ala
a da bauta kafin su samu abinci.

Hakan kuma akwai wahala, musamman ga mutum kamar Baffa Lawalli da zuciyarsa ta riga ta jima da mutuwa murus.

Har
aki Kaka ta kawo min
umame ganin ban fito ba.

Na kar
a na fara ci ko taste
insa bana ji saboda zuciyata a jagule ta ke.

Wajajen
arfe goma na kira Baffan Katsina na gaishe shi.

Kafin ma na fara masa bayani sai ya ce mini yana Kasuwa wai sun yi magana da Baffa Lawalli tun jiya,
arshen sati zai shigo Zaria a zauna a tattauna maganar.

Na sauke nannauyar ajiyar zuciya bayan na kashe wayar.

Ba zai fa sa
u ba.

Ba za su ha
e min kai su ce za su bayar da ni wa Alhaji Nafi'u ba.

Wannan zalincin ba zai yiwu ba...
*JAYKAY*
"Dad!" Junior ya kira ya nufo shi da gudu.

"My Birthday Boyyy" Jalal ya fa
a yana shafa gashin kan yaron.

Gobe ne Birthdayn
ansa Muhammad Junior, kuma Antynsa Janan ta shirya masa Birthday Party da yamma.

Ofcourse sai da ta billing
insa ku
in party.

"Mom zata zo gobe"
"Mom?, Your Mom?" Ya tsare yaron da ido dan in dai Mom
insa Cassandra ya ke nufi, to abin da Mamaki.

Tun da ya yi mata fa
a ranan ba su sake magana ba.

Junior yana da waya.

Ofcourse an yi customizing wayar saboda ta zama kids friendly.

Kuma daga wayar Jalal akwai application da aka saka masa zai iya accessing wayar Junior ya dinga monitoring duk abinda ake da wayar.

Musabbabin bashi wayar ma saboda ya samu damar magana da Cassy ne a duk lokacin da ya ke so.

Amma Hajiya ta saka masa screen time, dan haka duk dare wayar tana wajenta sannan bata barinsa ya tafi da ita school.

"Cassandra, za ta zo gobe?" Ya sake tambayar yaron, to be sure.

"Yes" yaron ya gya
a kai cike da farin ciki.

"She promised me she'll come for my birthday"
Jalal ya shafa fiskar yaron ya ce "that's good" Cassandran da ya sani ba zata bar business
inta ta zo Nigeria saboda Birthdayn
ansu ba.

Amma ba ya so ya
atawa yaron rai shiyasa yai shiru.

Wucewa ya yi
akin Hajiya ya gaisheta sai kuma ta tambayeshi yana da labarin Cassandra za ta zo gobe?.

Ba ya so ya nuna mata bai sani ba, sai ya ce mata e ya sani.

Idan Cassandra bata zo goben ba, ya san
aryar da zai fa
a mata.

Hajiya ta ce "Allah ya kawota lafiya"
"Amin" ya amsa
asa-
asa.

Jin bata sake cewa komai ba sai ya mi
e ya fita.

Yana shiga
aki suit
insa kawai ya cire ya ajiye akan gado, ya zauna a gefen da ya ajiye suit
in ya shiga kiran numbar Cassandra.

Jin bata
auka ba sai ya yi tsaki ya ajiye wayar ya cire kayansa ya shiga ban
aki ya yi wanka.

Bayan ya fito sai ya saka comfy black shirt da grey wando ya sake jawo wayarsa sai ya ga ashe Cassy ta tura masa sa
o ta email
insa.

Yana bu
ewa sai ya ga ticket
in jirgi daga London zuwa Abuja tareda gajeran sa
o wai ya turo mata Direban da zai zo ya
auketa daga Abuja ya kawota Zaria.

Da gaske kenan za ta zo
in.

Gara ta zo
in saboda su samu damar tattauna al
iblar aurensu.

Sake duba time
in da flight
inta zai sauka ya yi saboda anjima idan zai fita sallah ya fa
awa Direbansa zai je Abuja gobe.

Washegari kuwa shi ya tu
a kansa zuwa office saboda ya aiki Direbansa Abuja.

Lokacin da zai fita sai da ya yiwa Junior al
awarin zai dawo da wuri saboda Birthday Party
in da aka shirya
arfe hu
u ne.

Zuwa
arfe sha
aya na safe Sakatariyarsa ta masa maganar meeting da ya ke da shi da Chef Jonah.

Chef Jonah, wanda ake kira da Chef Joxxy a social media, shine Chef
in da Jalal ke son ya musu aiki a restaurant.

Ba yan ya bawa Sakatariyarsa go ahead akan ta shigo da shi, sai wani
angare na zuciyarsa ya tuno masa da Ziyada.

He did the right thing da bai
auketa aiki ba.

Ya sake jaddadawa ransa.

Chef Jonah ne ya fi dacewa da restaurant
insa in dai har yana son wajen ya bun
asa da kyau.

Chef Jonah ya fi Ziyada yawan experience.

Ya yi aiki a manya-manyan hotels dake Kaduna.

Ya yi aiki har a Government house da ke Jos a matsayin Assistant Chef.

Chief Financial Officer
insu wato Mr Munir ne ya recommending
insa, saboda
warewarsa a national da international cuisine.

Chef Jonah yana kan nuna masa sample
in menu da za su yi amfani da shi a restaurant
in, amma
walwarsa sai maimaita masa maganganun Ziyada yake.

Particularly, wajen da ta ke cewa
"Da kake cewa idea ta bata dace da restaurant
inka ba, kada ka manta bani na kawo kaina nan ba.

Hajiya ce ta nuna tana so na yi aiki a nan saboda ta yarda dani".

Idea
inta na da kyau, amma for a small scale restaurant, ba irin wanda suke son bu
ewa ba.

He's right.

Aiki da Chef Jonah shine dai-dai, ba wai aiki da Chef Zeey ba.

Ya sake fa
awa kansa.

Ganin hankalinsa ya rabu biyu sai kawai ya sallami Chef Jonah akan za su sake zama akwai inda zai je.
an'uwanka is more open to new ideas" ya tuno kalaman Hajiya.

Tunani ya fara, idan Jamal ne, wanne zai
auka?...

Bai samu ya shigo gida da wuri ba sai
arfe biyar saura.

Bai so haka ba.

Ya so a ce da shi aka bu
e partyn.

Already yara sun cika gidan.

Sai wasanninsu suke yi.

Hannunsa
auke da gift
in da ya siyo ya nufi wajen da Junior ke tsaye yana magana da wasu yara.

"Dad!" Ya zo wajensa da gudu Jalal ya
aga shi sama yana bashi ha
uri kan bai zo da wuri ba.

"Look, Mom ta zo" ya nuna masa inda Cassandra ke tsaye tana waya.

Kallon wajen da ya yi sai ya yi dai-dai da juyowarta.

Tana ganinsa ta fara tahowa fiskarta
auke da murmushi.

Ajiye Junior ya yi wanda ya kar
i gift
in hannunsa ya yi wajen abokanansa da gudu.
Chapter 22 · 0% Book details