← Book details Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 95

Sashe 32

Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suma fa na fahimci kamar kallon na tsufa a gida ban yi aure ba suke min.

Ba su dai furta min ba, amma shawarwarin da suke bani ne ya nuna hakan.

Ban ma fa cika 25yrs ba fa.

Sai nan da wata uku masu zuwa zan cika.

Umma kam har da cewa idan akwai wanda na amince da shi to na ce ya fito
in kawai.

Ba sai su Baffa Lawalli sun min auren fin
arfi ba.

Allah Sarki, Umma bata san bani da saurayi ba.

Ga shi har Sallah ta
arato, lokacin dana yanke zan bawa Jalal amsa ya matso amma har yanzu zuciyata bata gama tsaida matsaya ba.

Auren Jalal na nufin za mu iya rabuwa a duk lokacin da bu
atar hakan ta taso.

Shin na shirya yin aure wanda ke da deadline?

Mi su Baffa Lawalli za su fa
a idan Jalal ya sakeni bayan shekara
aya ko biyu da aure?

Na sani idan na yi auren aka sakeni ba ni ce farau
in yin zawarci a agidan ba.

Adda Suwaiban Baffa Lawalli aurenta na uku kenan.

Aurenta na fari tana budurwa shekara hu
u ta yi ta fito.

Aure na biyu ko shekara bai yi ba aka saketa.

Wannan da ta yi na uku shine kuma Allah ya sa ta jima.

Dan ina ga za ta yi shekara goma a gidan.

Aishan Baffa Zakari ma saki biyu ne tsakaninta da mijin da suke tare.

Yanzu ne da ya saura igiya
aya tsakaninsu ta nitsu ta dena yin yaji.

Dan haka idan na yi aure aka sakeni ba sabon abu bane a gidan namu.

Amma duk da haka.

Shin na shirya ma Aure da kuma Zawarci?.

Ban san ya aka yi wani
angare na zuciyata ya fara kwa
aita mini auren Jalal ba.

Ba dan ya min al
awarin zai bani restaurant ba.

Ba dan ina gudun auren Alhaji Nafi'u ba.

Sai dan akwai wani
an mitsitsin lungu a zuciyata da ya ke jin wani abu akan Jalal.

Irin abin da na jima ban ji irinsa ba tun bayan rabuwarmu da yaya Aminu.

A ranan da zan koma Zaria Umma ta min kitso.

Wata 'yar Mama kuma ta min lalle.

Ban je park bama sai
arfe hu
u na yamma.

Na shiga mota sai Zaria, ina murna zan je na ga Kakata.
*JAYKAY*
Tun daga Azumin farko har yau Azumi 29, wato jajiberin sallah Jalal Maiya
i bai samu kwanciyar hankali ba.

Irga kwanaki yake yana lissafin saura kwana nawa Ziyada ta bashi amsarsa.

Wani lokaci sai ya ji kamar ya kirata ya tuna mata, sai kuma ya fasa.

Wani lokaci kuma kawai so yake ya ji muryarta amma sai ya basar ya hana kansa kiranta.

Amma rashin kiranta bai hanashi bibiyarta a duka shafukanta ba.

Duk content
in data
aura sai ya je ya kalla.

Ta wannan hanyar yake jin muryanta, koda kuwa bayani take akan abincin Iftar da take dafawa.

A cikin wa
annan kwanakin ya sa aka masa
aramin bincike akanta.

Yanzu ya san cewa mahaifinta ya rasu.

Ya san sunayen Uncles
inta da sana'ar da suke yi.

Ya san a ina ta yi karatun Primary da Secondary.

Ya san sau nawa ta rubuta JAMB kafin ta samu admission a ABU.

Ya san course
in da ta ke karantawa, ya san idan sun dawo daga hutu ajin
arshe za ta shiga.

Jalal sai da ya piling duka information
inta ya zubasu a kansa ya ke
e musu waje na musamman.

Hatta ranan birthday
inta, ya sani.

Wani abu da ya fara fahimta shine.

Tun rasuwar Jamal wannan ne karo na farko da ya ji ya damu da rayuwar wani.

Wannan ne karo na farko a rayuwarsa da ya ke bibiyar lamarin wata mace.

Ba zai iya fassara me yake ji akanta ba.

Amma ya san wani abu
aya, ita
in ta kawo masa wani haske a rayuwarsa bayan duhun da ya ke fama da shi shekara uku da suke wuce tun daga rasuwar
aninsa da kuma ajiye aikinsa da ya yi.

Ita
in SUNSHINE
insa ce.

And tabbas, zai yi duk abinda ya kamata domin ganin ta shigo rayuwarsa.

Ba kuma dan Hajiya ka
ai ba, sai dan genuinely yana so ta shigo rayuwarsa
in...

Safiyar ranan Sallah Jalal ya sake tsintar kansa da bibiyar shafin Ziyada.

Amma bai ga ta
aura komai ba.

Ya ji kamar ya kirata amma sai ya hana kansa aiwatar da hakan.

It's too early, maybe tana shirye-shiryen fita idi ne.

Ba a jima ba shima ya sauko
asa cikin shigar wata luxury white Wagambari da ta sha aikin hannu.
inkin babban riga ne amma bai saka babban rigan ba ya ri
ota a hannu.

Saboda yau Sallah shi yasa zai saka babbar riga, da sun dawo daga Idi zai cireta.

Shi idan ka ga ya saka Jumpa ma to ranan Jummu'ah ne.

Itama kuma saboda Hajiya za ta yi magana ne idan ya sa
ananan kaya ranan Jummu'ah.

Mata da rashin shiryawa da wuri 5&6 ne.

Shi da Junior sun riga sun shirya sun sau
asa, inda yaron shima ke sanye da shiga irinta Jalal
in, har da
an hulansa.

Uba da
an duka sun fito sun yi kyau.

Hajiya ce ta fara fitowa, Janan kuwa sai da aka buge da cewa za a tafi a barta tukunna ta fito da gudu ko
ankwali bata
aura ba.

Shi da Janan ne a gaba, yayinda Hajiya da Junior suke zaune a baya.

Throughout tafiyar tasu zuwa Masallacin Idi, Janan ta yi shi ne wajen
aura
ankwali da kuma recording vlog
inta tana bada bayanin ga su nan ita da favourite people
inta za su je Eid.

Da aka taso daga masallaci sai suka wuce Family House dan su yi gaisuwa kafin su koma gida.

In between gaishe da Uncles da kuma cousins da suka zo sallah a Zaria daga wajaje daban-daban na
asar, ya samu damar sake le
a wayarsa.

This time whatsapp status
inta ya fara dubawa kota
aura wani abu.

Yana neman anything daga gareta.

Rubutu.

Hoto.

Murya.

Kai anything da zai nuna masa cewa ta yi sallah lafiya.

Yana ganin ta
aura hotuna biyu a status ya ji wani relief.

At least zai ga hotonta.

Hotonta ne ita da wata tsohuwa a filin idi, ta rubuta NI DA KAKS MUNA MUKU BARKA DA SALLAH
.

Ya riga ya san Kaks da ta rubuta ba typing error bane.

Kwana 29 da ya
auka yana bibiyar videos
inta ya fahimci haka take kiran Kakarta.

Infact zai iya mimicking yadda ta ke kiran KAKS
in ma.
an binciken da yasa aka yi masa akanta da kuma FBI Agent
in da ya zama a pages
inta, ya fahimci cewa tana tsananin son Kakarta.

An ce masa a hannun Kakarta ta taso.

So, they are very close.

Hoto na gaba hotonta ne ita ka
ai, tana ri
e da Sallaya fiskarta
auke da murmushi, ta mi
a hannunta as if tana so ta kar
i wayar.

Daga caption da ta sa ya fahimci Kakarta ce ta
au hoton.

Hoton a kaikaice yake saboda ba a
auka da kyau ba.

Amma ya yi kyau.

Ta yi kyau.

Lokacin da suka koma gida bayan an gama gaisawa a Family House ya riga ya za
awa kansa zai je gidansu Ziyada ya je ya ganta.

No.

Zai je ya ji shawarar data yanke.
arfe biyar da rabi ya shiga
akin Hajiya bayan ya sake wanka ya saka light blue Jumpa da ta sha aikin hannu da hula.

Hajiyar ma bata jima da shiga
akinta ba dan tun da suka dawo gidan itama take ta kar
an ba
an gyara hularsa ya yi dan saka hula ba
aramin damunsa yake ba.

A cikin
asa da shekara uku da dawowarsa Nigeria ya koyi sakawa dan a baya zai yi wuya ka ganshi da hula a kansa.

Ko ya saka saboda wani dalili to ka bashi minti talatin za ka ga ya cire ya ajiye.

Idan Jamal ya masa magana sai ya ce hula na saka masa ciwon kai.

Yanzu da ya ke tsaye gaban Hajiya sai yake sake jinsa cewa shigarsa ta yi tunda Hajiya ta yaba.

"Hajiya, bari mu fita hira"
"Hira?" Hajiya ta tambaya da mamaki.

Ta san dai dan zai je wajen abokansa ko 'yan'uwa ba zai ce mata zai fita hira ba.

Idan abinda ta ke tunanine to kuwa Alhamdulillahi.

Bata ma
auka zai
au maganarta da mahimmanci da wuri haka ba.

Amma ta ji da
in hakan.

Kuma tana masa fatan Allah ya ha
ashi da mace ta gari.

A dawo lafiya ta masa tareda addu'ar Allah ya shige masa gaba.

Ya amsa da Amin ya fita yana jin da
in yadda ya ga farinciki ya wanzu a fiskar Hajiya lokacin da ya tabbatar mata wajen mace zai je.

Har ya yi nisa da gida sai ya tuna bai ri
o komai ba.

To mi zai ri
e mata?.

Flowers?, No.

Nan ba London bane.

Wani cousin
insa Ibrahim ya kira wanda suka
an ta
a hira da shi yau da safe a Family House.

Ya tambayeshi me ake kaiwa 'yanmata ranan sallah.

Sai da Ibrahim ya masa dariya yana masa sha
iyanci wai ya gaji da Baturiyarsa kenan zai nemi ba
ar fata, sannan ya fa
a masa abubuwan da zai iya kaiwa.

Ibrahim
ani yake a wajensa amma tsakaninsu bai cika shekara biyu bama.

Yana cikin wanda suke
asawa da Jalal
in.

Dan Jalal ba shiga cikin mutane yake ba.

Lokacin da ya gama siyayyar da zai yi a wani Mall ya fito ri
e da ledoji a hannunsa sai ya fara mamakin kansa.

Wai shi Jalal ne yau yake duka wannan zirga-zirgan saboda yana neman attention
in yarinyar da bata kai Janan ba.

No.

Duk abinda yake yi saboda ya samu ta amince da tayinsa ne, and in return ya samu Hajiya ta yi farinciki da shi.

Ba wani abu serious bane.

Ya kwa
i kansa.

Har ya iso
ofar gidansu Ziyada bai kirata ba.

Sai da ya kashe mota sai kuma ya ga wautar yin hakan.

What if bata nan?

Ko kuma ta
i fitowa.

Ya sani, it's bad manners ka zo gidan mutum ba tareda ka nemi izinin zuwa ba.

Wannan duk daga baya ne.
Chapter 32 · 0% Book details