← Book details Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 95

Sashe 24

Chef Zeey Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar Jamal kusa da ita shi ya hanata shiga damuwa na tsawon lokaci bayan rasuwan Daddyn su.

Amma, lokacin da Jamal ya rasu.

Tamkar ya tafi da wani
angare na rayuwarta ne da shi Jalal ba zai sake gani ba.

Bayan rasuwan Jamal, sai Hajiya ta cire hannunta daga komai ta bar masa jagorancin kamfanin.

Janan tana aiki a wajen, amma aikin da take is more of jeka na yika ne ba wani abin kirki ta ke ba.

Shi yasa ma aka bata wani
aramin position a wajen.

Idan ta Janan ne, bata
i kawai ta dinga kwana tana tashi bata komai ba, sai danna waya, online shopping da kuma yawon duba sabbin wajaje a ciki da wajen Zaria.

Ganin Hajiya a haka sai ya breaking
insa, musamman da ya tuna cewa akwai yiwuwar abinda ya faru jiya akan Cassandra ne ya
ata mata rai.

Amsa gaisuwarsa ta yi sannan ta kira sunansa a hankali da dasashshiyar muryar da ta fi kama da kuka ba wai mura ba.

"JALAL"
"Yes, Hajiya" ya amsa cike da tsoron abinda za ta fa
a masa
"Aure nake so ka yi Jalal" ta fa
a ko
yaftawa bata yi daga kafe shi da ido da ta yi ba.

AURE.

Ya maimaita a ransa.

"Musulma, 'yar Nigeria, kuma Bahaushiya" ta jero masa sharu
a uku.

A baya ta kan ce masa zai iya auro kowacce yare ma ya kawo in dai Musulma ce kuma 'yar Nigeria.

Amma yanzu tura ta kai bango, abubuwa ukun nan take so a cikin mace
aya.

Shiru ne ya biyo bayan abinda ta fa
a.

Kowannensu da tunanin da ya ke a zuciyarsa.
*ZEEY*
"Hajji Jibrin, Mutanen Lagos"
Kaka ta fa
a ganin mutumin da ya shigo wajenmu.

Na
ago kaina dan a kwance nake ina karanta handout
in course
in da za mu rubuta Friday.

Jiya Laraba exams
in ta yi sau
i dan elective course ne, amma ta gobe gaskiya sai a hankali.

Ga shi Doctorn da ya ke
aukanmu course
in ya tara mana manya-manyan handouts guda uku har da text book biyu wai duk materials
insa ne mu je mu karanta.

Yaya Jibrin ne ya shigo.

Sai nima na washe fiska ina gaishe shi da Hajji mutanen Lagos.

Zama ya yi a dakalin
ofar
akinmu, ya fara gaishe da Kaka.

"Jibrin tashi a wajen, bari Ziyadatu ta
auko maka kujera a
aki"
"Barshi kawai, Kaka Altine.

Makanike ai babu inda baya zama "
Na mi
e da sauri na shiga
aki dan na kawo masa kujera.

Wajen da ya zauna akwai
an rana ta gurin.

Dana fito masa da kujeran sai na ajiye jikin gini kusa da Kaka na ce masa Bismillah.

"Nagode, Ziya.

Ya girke-girke?.

Ai kafin a sace mini Andiroyid
ina ina kallon duka bidiyon da kike
aurawa a Fezbook"
"Allah Sarki!

Ai yaya Jibrin Alhamdulillahi kawai.
aura girki a social media ya yi mini rana.

An fara samun alkhairi"
Yaya Jibrin ya ce "Masha Allahu"
Yaya Jibrin yana
aya daga cikin wa
anda suke bibiyana tun farkon fara food content
ina, lokacin ma a Facebook ka
ai nake yi.

Jibrin
an Baffa Lawalli ne.

Shine babba a cikin maza.

Suwaiba ita ce 'yar fari, sai Hajara, sai shi Jibrin
in.

Ya jima da barin gida.

Tun ma kafin ya tafi Lagos ba a gida yake kwana ba saboda sun yi fa
a da Babansa.

A lokacin an ce wasu ku
i yaya Jibrin
in ya bashi ajiya, shi kuma Uban ya cinye.

Jibrin Makaniken mota ne.

Kafin ya tafi Lagos yana
ashin wani Ubangidansa ne a nan Zaria, daga baya dai sai ji muka yi wai ya bi babbar mota ya tafi Lagos.

Sai da ya yi shekara biyu bai dawo ba.

Da ya zo gida kuwa ya taho da ku
i masu yawa ya fara gini.

Ashe dama ku
in da Baffa Lawalli ya cinye ku
in da ya ke tarawa zai fara gini da shi ne, dan ya jima da siyan fili.

Muna chatting da shi Sama-sama ta Facebook idan ya min magana.

Bayan shekara biyar a Lagos kwanaki da ya zo ya ce mana yanzu yana da garejin kansa.

Abubuwa sun bun
asa masa gaskiya, dan the last time da ya zo an gama komai na gidansa saura fenti. 3 bedroom ne mai kyau dai dai gwargwado babu laifi.

Ni da Kaka ya kaimu muka shiga gidan muka sa albarka.

Har yanzu tsakaninsa da Babansa sai a hankali.

Musabbabin rashin jituwarsu
in dai still maganar ku
i ne.

Zai turo masa ku
i daga Lagos dan ya yiwa Maman Suwaiba da
annensa hidima amma sai ya cinye ku
in Maman Suwaiba ta dinga damunsa wai baya turo musu komai.

Har machine ya ta
a siyawa wani
aninsa akan ya ri
a hawa yana Aca
a amma ko wata shida machine
in nan bata yi ba Baffa Lawalli ya je ya siyar ya biya bashi saboda an ce za a kai shi Police Station.

Tun daga lokacin yaya Jibrin ya dena tura masa ku
i ko yi masa kyauta.

Duk abinda zai yiwa Mahaifiyarsa sai dai ya turo sa
o ta hannun wasu.

A hakan fa wani abun sai dai ya siyo ya aiko dan idan ku
i aka turo Baffa Lawalli ya ji labari haka zai bi gefe ya kar
e a hannun Maman Suwaiba.

Idan yaya Jibrin ya tafi Lagos sai an ganshi kawai.

Shi yasa muke mamakin ganinsa rana tsaka a gidan namu.

Sama-sama na ke jinsu yana yiwa Kaka ta
in maganar aurensa ne ya kawo shi gida.

Wai ashe har an saka rana.

Yarinyar 'yar Kano ce kuma Baffan Katsina ne ya shige masa maganar auren ba Babansa ba.

Ban yi mamakin haka ba, dan har yanzu basa ga maciji da Babansa.

Kuma duk inda Baffa Lawalli zai yi maganar yaya Jibrin zaginsa ya ke ya ce ya tafi bariki Lagos ba ya taimaka masa da komai.

Kuma fa tsakani da Allah yana taimakawan dai-dai gwargwado.

Ko lokacin da Mardiyyah za ta sake zana jarrabawar NECO, na ji an ce shi ya biya mata.

Shi dai Baffa Lawalli tunda yaya Jibrin ya dena tura masa ku
i ta hannunsa ya ke jin haushinsa.

Ni da Kaka muka masa fatan alkhairi da addu'ar Allah ya sa a yi biki lafiya.

Wai auren za a yi shi kwana uku bayan sallah dan haka yana nan a Zaria har sai bayan biki kafin ya koma.

Sai da ya yi lissafin saura kwana nawa bikin nefa na tuna cewa ashe fa ana ta maganar Azumi saura kwana biyar ko shida.

Ko jiya sai da Ummana ta tambayeni ko zan zo na yi musu Azumi na ce mata ban sani ba sai dai mun kammala exams na gani.

Yaya Jibrin ya jima a sashenmu kafin ya tafi har da bawa Kaka dubu uku wai ta sayi goro.

Daren ranan wuni na yi ina karatu har
ayan dare kafin na kwanta lokacin dana ga idona ya fara ganin bibbiyu.

Exams
inmu da safe ne dan haka da Asuba tashi
aya Kaka ta mini na mi
e.

Ashe bacci ma waje ya samu.

Wanka na yi sannan na
auro alwalar sallar Asuba.

Ai ina idar da sallah sama-sama na yi Azkar sannan na sake jawo handouts da
an jotings
in dana yi na fara bita.

Bakwai na safe har na fita daga gida.

A school na ha
u da Faty Amarya idanunta sun
wala-
wala saboda rashin bacci.

Hijabi ta zum
ula har
asa, ta ce mun na sallarta nema tsabar sauri ta jawo ta saka.

Na ce mata me ta ke yi bata tashi da wuri ba ta fara bani labarin yadda mijinta ya zo ya hanata karatu jiya da dare.

Ina jin ta fara zancen Ma'aurata na dakatar da ita na ce mata Allah dai ya bamu sa'a kawai.

Da aka fara shiga hall muka shiga da addu'a a bakunanmu...

Na riga Faty fitowa daga exams.

Ban san me ta tsaya rubutawa ba amma har sai da aka fara threatining
insu akan saura minti biyar a
are jarrabawa sannan ta submitting ta fito.

Ni kam tunda na iya amsa questions biyu masu kyau sauran kuma na rubuta abinda zan iya, na ce ya isa haka.

Allah na gani ni ban iya tambayar mutane Answer a hall ba.

Ko irin ka
aga mini na kwafa
innan bana yi.

Idan muka zauna da Faty na samu dama ina
aga mata ta kwafa, amma bana iya magana a hall dan tsoro nake ji.

Ina isa
ofar gidanmu dana ga tsohuwar motar Baffan Katsina a
ofar gidan sai na sawa raina ko dai na samu Jummu'ar Alkhairi, ko kuma na samu Jummu'ar Allah Sarki!.

Na shiga gidan zuciyata a sanyaye.

Sashenmu na fara shiga na kuwa samu Kaka ta ce Baffa Adamu ya iso a nan garin ma ya yi sallar Jummu'ah.

Ko cire kayan jikina ban yi ba jakata kawai na ajiye na yi cikin gida.

Gidan Baffa Mamman na wuce bayan Yakubu ya ce min suna can.

Su uku na samu a falon.

Da alama Baffa Zakari yana wajen aiki.

Na tsugunna har
asa na gaishe da Baffa Adamu sannan na gaishe da Baffa Lawalli da Baffa Mamman da ke latsa wayarsa.

Baffa Adamu ya tambayeni ya karatu na ce masa Alhamdulillahi jarrabawa ma nake rubutawa.

Daga wannan, ajin
arshe za mu shiga.

Ya min addu'ar Allah ya bada sa'a na ce masa Amin.

Lokacin dana mi
e zan tafi sai Baffa Lawalli ya ce " tunda kin zo, Adamu, mu yi mata maganar yanzu kawai a wuce wajen"
Sai na ji zuciyata ya buga da
arfi.

Baffa Adamu ya kalleni ya ce "ZIYADATUN dawo ki zauna, akwai maganar da za mu yi da ke".

Yau dai, Jumma'ar Allah Sarki ce...
*Pay 500*
5921536136
RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN,
Moniepoint MFB
Evidence to: 08137311900
CZ 17
*Paid Book.

Tsakani da Allah, ka biya kafin ka karanta*
*ZEEY*
Ina ga babu wanda bai maimaita kalmar "mu iyayenki ne" sau biyar ko fiye ba a cikinsu.

Tunda naga sun dage da bayyana mini abinda na sani tun tasowata, na san cewa wani fin
arfin suka shirya min.

Sun bu
e maganar ne da tarihin haihuwata.

Yadda Babana yai ta yi mini addu'ar tsawon rai.
Chapter 24 · 0% Book details