← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 177

Sashe 98

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Khadeeja Candy*
Page 4
Aliyu yayi hanzarin saka wayarsa aljihu tun kamin Turhan din ya karaso inda yake, ya zaro handkerchief ya lullubawa fuskar Fatima duk da ya san ba lallai ne a ganin farko Turhan ya gane fatima tana da alaka da shi domin ba zai yi tunanin Emily zata samu ta bangaren Aliyu ba, and he would never think Aliyu zai iya boye masa babban abu kamar wannan.
"Abun mamaki, Aliyu kai ne a nan?"
Aliyu yayi murmushin karfin hali yana ala ala kar Fatima ta farka, domin ya san karamin aikinta ne ta labarta masa waye ita ko be tambaya ba.
"Ni ne, Turhan taya muka hadu?"
Turhan yayi murmushin kasaita yaje zai rumgume abokinsa daman al'adar larabawa ce rumgume juna da sumbanta idan suka hadu da wanda suke so, haka Turhan yayi yunkurin aikatawa cikin murna da farincikin ganin abokinsa sai dai babu dama saboda babyn dake hannun Aliyu.
"Ohhh Baby waye haka ta hana ni rumgumar abokina, ban jidadi ba"
Aliyu ya fadada murmushinsa abubuwa biyu suka zagaye shi, yadda Turhan yake murnar ganinsa ya saka shi jin wani iri na gaskiyar daya boye masa gashi kuma yana fargabar kar Fatima ta farka.
"Baka santa ba, daman wai tun da muka yi waya kace min zaka zo baka zo ba?"
"Ban samu zuwa ba, daman na so mu zo tare da Reem ne amman haka be samu ba"
Ya fada cikin wani yanayi na rashin jindadi.
"Toh ya jikin Ammy?"
"Da sauki take cewa sai dai naje na gani, muje ma tare ai sai ka duba ta ko? Daman ina neman mai raka ni kasan kullum idan zan je gurin Ammy tsoronta sabo yake zame min, saboda maganganu da kuma fuskar da take karba ta da ita, ta daina murna da zuwa na yanzu"
Aliyu can't say no to his friend kuma ya san ba zai yiyu ya tafi tare da Fatima gidan ba hatsari ne ma babba ya tafi da ita gidan.
"Yeah amman na yi waya da direba na ce ya zo ya dauki a nan"
"Malam ba wani babban abu ba ne direbanka ne fa, karkashinka yake ai zaka iya fada masa ya koma kawai, direban da zai dauke ni yana waje yana jirana mu je kawai kasan dai ba zan barka Airport din nan ba"
"Bata zan yi?"
"Aa amman dai ba zan barka ba i miss you Aliyu sosai fa"
"Okay fine mu jira Direban ya karaso sai ya tafi da wannan yarinyar kar mahaifiyarta ta damu, ni kuma sai na bika mu kaika gida tun da ka zama amarya"
Yayi dariya tare da kai hannu ya taba Fatima dake ta bachinta cike da sha'awar yara.
"Yar waye wai"
Hannunsa na kaiwa a jikin Fatima ta zabura da karfi ta sauke ajiyar zuciya a cikin bachin da take.
"Oh Sorry"
Turhan ya fada yana dauke hannunsa da sauri gudun kar ya tasheta, Aliyu ya kalleshi jiki a sanyeye ya juya yana fadin.
"Mu tafi waje mu jira shi"
Turhan ya jera tare da shi suka fito suna dan taba hira, sun tsaya harabar for like 10min direban Aliyu ya kira Aliyu ya kwatanta masa inda yake direban na isowa Aliyu yayi hanzarin nufar motar ya bude baya ya kwantar da Fatima a hankali bachi take sosai kamar wanda ta yi wani katon aiki, Aliyu ya rufe motar a hankali be taba jin ya aikata wani abu na rashin kyautata kamar kin fadawa Turhan Fatima yarsa ce a yanzu ba. Sai yake jin kamar ya ci amanar abokinsa duk da yake yana da laifi.
"Ka tafi da ita gida ka shiga da ita ciki ka kwantar da ita"
Ya saka hannunsa alijihu ya ciro keys ya mika masa.
"Toh ranka ya dade"
Ya karbi keys din sannan ya dauki kayan da Aliyu ya zo da su ya saka bayan mota, sai a lokacin Aliyu ya sami relief ya nufi gurin da Turhan yake tsaye jikin motar da za su shiga, yana isowa Turhan ya ware hannu Aliyu ya ware suka rumgume juna.
"Na jidadin zuwan nan yaushe rabon da na saka ka ido Aliyu"
"Ni ma na yi marmarin ganinka, fatan kana lafiya"
"Da sauki dai ina lafiya ga mutumen da uwarsa ke fushi da shi?"
Ya bude motar ya shiga baya Aliyu ma ya zagaya ya shiga baya, mutumen da suke tareda Turhan ya shiga front seat direba yaja motar suka fara tafiya, suna taba hira har suka isa gidan. Turhan da Aliyu a tare suka fito motar Aliyu ya wuce gaba ya shiga cikin falon Turhan na bayansa, Mai aikin Ammy ta amsa musu ta gaishesu, Aliyu ya karasa gurin da Ammy take zaune ya zube kasa yana gaisawa da ita Turhan ma ya karasa ya zauna kusa da Aliyu. Cikin murna da farinciki take kallon Aliyu.
"Madallah Aliyu ne a gidan na mu yau?"
"Ni ne Ammy ya jikin na ki"
"Jiki Alhamdulillah Aliyu ina samun sauki, ashe ka samu shigowa"
"Eh kin san daman na ce zan shigo na duba ki, sai gashi kuma wani uzurin ya taso aka yi daidai, a airport na hadu da Turhan ai sai muka zo tare"
"Maa Shaa Allah, haka fa ka fada min zaka zo ai ka huta baka tsaba alkawari uwarka ta yi farar haihuwa Aliyu"
Ammy ta fada har lokacin bata kalli inda Turhan yake ba. Turhan ya sauke kansa kasa yana jin wani iri, Aliyu ma ya ji babu dadi domin Ammy tana kokarin muzanta abokinsa ne a gabansa which it's not fair.
"Amman dai jikin da sauki sosai ko Ammy?"
"Na samu sauki Alhamdulillah, ai na ma fadawa abokinka ba sai ya zo ba, kawai be ji magana ta ba ne daman be saba ji ba"
"Haba Ammy taya baki da lafiya kuma ki ce kar ya zo? Ai ba zai yiyuwa ba, ke fa mahaifiyarsa ce Ammy ki rika duba wannan"
"Zuwansa ba zai rage ni da komai ba balle ya kara ni, rabin ciwon nan ba shi ne silarsa ba? idan ya zo ai ba da lafiya zai zo min ba, kuma ina da masu kula da ni nan yayan yan'uwa sun ce wadatar, idan za amin allura kullum sai Nurse ta zo, Likita kuma kullum yana zuwa duba ni, saboda na fada masa ni bana son asibiti ko da mutuwa ce a bar ni na mutu a gida, kaga shi kenan abokinka ya huta ba sai ya sake zuwa kasar nan ba sai yayi zamansa a can daman haka ubansa yake so"
Turhan ya kalleta felling hopeless cikin murya mai rauni ya ce.
"Wani dan kirki ne zai yi fatan mahaifiyarsa ta mutu ya huta? Ammy ya kike magana haka kamar mai magana da makiyinta? Danki ne fa ni jininki, na rasa ya zan yi na kawar da wannan bakin shatin dake a tsakaninmu, Ammy kina tunanin all this while abun nan dade yake min? Ko tafiya kika yi kika bar ni wannan abun ba zai barni na samu salama ba, Ammy ni ma ina cikin damuwa gaba daya yanzu bana jindadin rayuwar da nake, abun da a aikata kuskure ne kuma ni dan'adam ne aziji"
Ammy ta girgiza kai.
"Aa abun da ka aikata ganganci ne ba kuskure ba, da gangan ka aikata, saboda baka kallo da daraja irin ta uwa, kuma abun da ka yi min ai ka kyauta tun da ka samu tukuici, Allah ya maka albarka Turhan na gode"
Aliyu ya ce.
"Ammy ki yi hakuri dan Allah ki yafe masa abun nan ya wuce"
"Na yafe masa, amman wucewar wannan abun? Sai na koma ga Ubangijina, ni kadai na san me nake ji, yaron nan shi kadai Allah ya ba ni, idan kai ka manta mahaifiyarka ba zata manta ba Aliyu, irin fadi tashin da na yi akan na samu ganin yaron nan, na wahala a gidan mahaifinsa kuma na wahala kamin a bar shi ya zo gurina, na dauki yar mutane na aura masa da tunanin hakan zai saka na samu dana da zuri'arsa a kusa da ni, amman ya watsar ya karyata duk wata halayya tasa dana fadawa yarinyar nan, marainiya ba uwa ba uba, yanzu Allah kadai ya san halin da take ciki idan ma tana raye, bata da kowa sai Allah bata da wani wanda zai nemi ya san halin da take ciki tun da bata da dangi, yarinyar nan ta yarda da ni amman Turhan ya rusa duk wannan ya nuna ba ni da muhimmanci a garesa kamar yadda ubansa ya nuna min"
Ammy tana maganar hawaye ya sauko idonta, Turhan yayi kasa da kansa ya saka hannunsa ya rike goshinsa idonsa suka cika da hawaye, ba na tausayin Emily ba na bakinciki daya saka mahaifiyarsa har ta zubar da hawaye akansa gaban abokinsa.
"Wane irin muhimmanci Aisha take da shi a gurinki har haka Ammy? Da har zaki zubar da hawaye akan abun da ya faru?"
"Irin muhimmanci da baka da shi"
Ta amsa masa kai tsaye da kakkaurar murya.
"Indai saboda ni ka zo, toh ka hada kayanka ka koma bana bukata, ka bari idan na mutu sai ka zo jana'iza"
"Subhanallahi Subhanallahi"
Ya maimaita har sau uku sai Aliyu ya dafa shi.
"Turhan fita waje ka jira ni"
Ya tashi cikin wani irin yanayi na bakinciki da ya fice falon, sai da ya fita sannan Aliyu ya ce da Ammy.
"Ammy bana son na tunatar da ke abun da kika riga kika sani, na san kin so Emily da Turhan kin tsara zamansu, amman haka be samu ba baki tunanin wata su din ba alheri ba ne ga junansu? Kuma haka Allah ya tsara shi da ita babu dogon zama, kuma Ammy karki manta duk yadda zaki so Emily Turhan danki ne, na san be kyauta ba amman fushinki a kanki da damuwarki zai iya janyo masa matsala a rayuwa ko ba yanzu ba a nan gaba, kuma Ammy Turhan yayi nadama sosai yanzu haka zancen da yake min yana son ya saka kudi mai kauri akan nemo Emily, abun ya dame shi ma, ki yi hakuri Ammy"
Ammy ta yi murmushi.
"Allah ya maka albarka Aliyu, ka san muhimmanci uwa shiyasa ka fadi haka, tafi ka tafi na gode"
"Shi kenan Ammy Allah ya kara sauki ya baki lafiya"
"Ameen Allah ya maka barka"
Ya mata sallama ya fito falon a jikin motar da suka shigo ya samu Turhan ya jingina fuskarsa dauke da damuwa. Aliyu ya saka hannayensa aljihu yana sauke ajiyar zuciya ta dayan bangaren abokinsa ya ba shi tausayi, sai dai kuma idan ya tuna labarin da Emily ta ba shi sai ya ji kamar be tausaya masa ba.
"Turhan am sorry iyaye sai lallabawa"
"Haka take fada min maganganu marasa dadi a duk lokacin da na zo, kuma ta sani na yi iya kokarina gurin neman yarinyar nan, ban same ta ba toh ya zan yi? Kana jin tana fadin bata san halin da Aisha take ciki ba, ni kuma da nake cikin wannan halin bata jin tausayina na rasa ya zan yi"
"Da sannu komai zai zama daidai In Shaa Allah, wai taya ka yi Aisha ta subuce maka.?"
Madadin ya amsawa abokinsa sai ya ce
"Ita ma fa yarinyar ta jefa ni a matsala, miyasa ta amince da auren nan tun farko fisabilillahi"
"Allah ya kawo sauki, ni zan wuce abun da zan fada maka shi ne ka yi hakuri da mahaifiyarka kuma ka yi ta addu'a"
"In Shaa Allahu, ma gode Aliyu, bari na yi ma direban magana sai ya kaika gida"
Aliyu ya shiga motar Direban yaja shi zuwa gidansa, a mota Aliyu ya gwada kiran Number Emily ya jita a kashe sai ya aika mata sako.
"Are you okay?"
Domin ya san ya kamata ace ta kira shi bayan riskar sakonsa, and maganar Ammy ta taba shi na cewa bata da wanda zai damu ya san halin da take ciki tun da bata da kowa. Bayan direban ya aje shi ya juya shi kuma ya shiga gidan da yayi datti yana mamakin taya haka ta faru domin yana da mai gyara masa gidan every week. A falo ya samu Fatima na ta bachi har lokaci akan kujera hannu ya kai ya taba jikinta yana mamakin wane irin bachi ne take haka, sai ya ji shi da dan zafi kadan. Mai kula da harabar gidan ya shigo yana masa sannu da zuwa Aliyu ya amsa yana tambayar ina mai gyara gidan.
"Tun da ta tafi bata dawo ba, bata fada maka komai ba tace dai zata je ganin gida ta bada keys a aje maka"
Ya saka hannunsa aljihu ya ciro keys din ya bawa Aliyu da hannu biyu. Aliyu ya mika masa Atm dinsa ya fada masa code sannan ya fada masa inda zai tafi ya samo musu abinci mai kyau...
Sorry ku yi hak'uri gobe zan yi long page in Shaa Allahu.
[7/2, 6:50
PM]
ABOKIN RAYUWA
Chapter 98 · 0% Book details