Sashe 30
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
waya? Me ye hadinki da wannan? Ina zaki je? Shi ne kawai abun da ka iya Ta matsa kusa da shi cikin ihu ta fara fashe mata kurcin dake mata ciwo a zuciya. Ni ba ni da ikon kaina, da wa zan yi mu'amala, su waye masu aikina da masu gadina, su waye makota na, a ina zan zauna, duk kai kake zaba min, ka hana in yi abota da kowa, ka hana na yi mu'alama da mutane kamar kowa, takamarka saboda ina zama a karkashinka ne, takamarka saboda ka tsamo ni daga rana zuwa inuwa ne, idan na yi magana sai kace kana so na ne? Taya ina aka soyayya da son kai? Miye banbancinka da sauran ne? Miye banbancinka da Khaleefa sa ya cusa yarda da soyayya a zuciyata ya aureni saboda kawai ya yaudare ni? Banbanta min banbancinka da Turhan mutumen da ya aureni saboda cika umarnin mahaifiyarsa ya maida ni kaskantacciya a cikin bayinsa, sai yaushe ni zan samu yancin kaina? Sai yaushe zan yi farinciki na har abada? Yin sa'insa da ita ba abu ne da ya saba yi ba, musamman idan ta ci galaba akansa da hawayenta, saboda haka ya zubar da makaman yakin da ya zo da su ya karasa gurin da take tsaye ya rumgume ta. Sai ta cigaba da zubar da hawayen da take. Ina tsananin sonki Emily, ban taba son wata mace ba sai ke, kina da kyaun da maza ba za su iya dauke miki ido ba, shiyasa zuciyata ta kasa natsuwa da wasu abubuwan, ina kokarin baki kariya ne, saboda ina jin cewar ke kadai ce mace a duniyar nan, bayan ke babu wata Ta daga kai tana kallonsa ta san yadda yake ji domin ta taba tsintar kanta a makamancin halin da yake ciki a yanzu, a lokacin da ta yi soyayya da Khaleefa bata ji bata ganin kowa sai shi. Ya sumbancin tsakanin girarta guda biyu sai ta lumshe ido tana tausayinsa da kuma kanta. ALIYU POV. Da abincin dake gabansa yayi feeding dinta daman ba wani son cin abincin yake ba a safiyar nan. Sai da suka gama sannan ya hada kayan ya dauka ya kai kitchen, kamar jira ake ya aje plates din sako ya shigo wayarsa kasancewar data sa kullum a bude take. Ciro wayar yai daga aljihunsa ya duba sakon da ya shigo yanzu. Sakon Emily ne da take gargadinsa tare da shimfida masa dokokinta. Bayan ya gama karantawa ya bata amsa, ta sake rubuto masa wani ya aika mata da tambayar abun da ya fi damunta, ta zayyana masa kadan daga sanin wacece ita, sai ya yi mata matashi da dalilinsa da kuma damuwarsa akanta. Ya dauki dakiku yana jiran amsarta amman be samu hakan ba, maybe mata shiryawa hakan ba, ya raya a zuciyarsa, kamin ya ji takun tafiyar Kameela a bayansa, da sauri ya juyo sai yayi hanzarin saka wayar aljihunsa yana mata murmushi. Me kike bukata Na ga ka dade a kitchen din ne, na dauka ko wanke wanke kake ma Ta fada da dan mamakinta na rashin yarda, mo matter how Aliyu zai mata rantsuwa, zuciyarta bata natsuwa saboda tsananin kishinta. Ya juya ya kalli kayan da ya aje sannan ya juyo ya kalleta. No, bari na je na yi wanka yau da wuri nake son tafiya aiki Kamin tace komai ya fice daga kitchen, ba dan komai ba sai dan gudun ta zargi wani abu, duk da haka kuma be tsira ba, domin hankalin matarsa be kwanta da yadda yayi sammakon fita dazun ba, da kuma yadda yake chat a kitchen dinta ba, ita dai ganin take sheidan zai iya zuga shi ya karya alkawarin da ya daukar mata. A take ta ji ta kwadaitu da son ganin chat dinsa, ta san mijinta ba zai mata karya ba, amman dai yadda mata suke ta zillo akan maza kamar za su aurar da kansu, ai wata zata iya tankwasashi ya fara halayen da ba nasa ba. Ita kam dai ba zata yarda mijinta ya lalace da kara aure ba, kara ta duba chat din ta ga koma miye ko hankalinta zai kwanta. Falo ta dawo ta zauna tana ta sake sake kamin zuciyarta ta fi karfinta har ta tashi ta nufi dakinsa ta tura kofar dakin ta shiga, ko da ta shiga ta samu yana bandaki yana wanka, farkon abun da ta fara neman shi ne wayarsa ta wurga idonta a ko'ina na dakin bata ga wayar ba har sai da ta daga fillon da suke kwanciya. Sai ta samu wayarsa a kasan fillon ya kifeta hakan kuma ba karamin mamaki ya bata ba domin ba halinsa ba ne boye waya, wannan ya saka ta san password dinsa kuma take shiga ko'ina a cikin wayarsa tana masa bincika son ranta. Zaunawa ta yi gefen gadon rike da wayar da bude password dinta ba zai mata wahala ba domin ta saba budewa, kai tsaye ta tafi messenges dinsa wato sakon kar ta kwana ta duba bata ga wani abun ba, ta fito ta shiga WhatsApp dinsa, bayan chat biyu da aka masa dayan na group dinsu na makaranta dayan kuma na abokinsa na ukun ne na Emily mai dauke da kyakkyawan hotonta. Kai tsaye ta tafi kan dp Emily tana kallon yadda Allah ya tsara kyakkyawar halittar kyaun a fuskarta, a take hankalinta ya tashi. Sabon chat ne da aka yi shi da number ta da be yi saving ba, sai da ta karanta sakon da ta turo masa ta karanta wanda ya aika mata sannan ta sauko daga kan gadon ta zauna a kasa hannunta daya a kanta. Miyesa mijinta zai shimfidawa wata mace kalaman ya damu da ita yana son sanin rayuwarta har haka? Watan ma kuma kyakkyawar kamar Emily. Bata san lokacin da ta jefar da wayar ba ta kwala wani uban ihu zuciyarta da mararta suka hau murdawa lokaci daya. Wayyo Wayyo...wayyo... Zuciyata... Marata... Bayana... Na shiga uku zan mutu Aliyu be gama daure bathrobe din jikinsa ya fito da sauri daga bandakin cikin tashin hankali ya rikata. Meya faru? Ta rike mararta tana kallonsa son take ta yi kuka ko ta yi masa magana amman azabar ciwon marar da take ji ta hanata aikata hakan. Jini ya fara yi mata zuba da sauri Aliyu ya saketa ya saka tufafi ya saka mata hijab ya dauketa ya fice da ita daga dakin. TURHAN POV. Ya dora hannunsa yana karon addireshi da kuma sunan mutanen da suka karbi Emily a wacan lokacin. Amman kana da tabbacin idan muka je zamu same su a gurin Turhan ya tambaya da hausa sai Faruk ya fadawa mutanen da yaren Yarba. "Ban sani ba, amman tun da har sun taba zama a gurin ko da baka same su ba zaka samu wani bayani a kan inda suka koma da zama ai, ni na gama aikina sai ka salleme ni yanzu "Emi ko m n niwon igba ti w n ti gbe ni aaye t , paapaa ti o ko ba ri w n, iw kii yoo ni alaye eyikeyi lori ibi ti w n gbe l ati gbe. Mo ti pari i mi, nitorina o le fi mi sil ni bayi." Yadda ya bukata haka aka yi, Turhan ya biya shi 20k yayi copy din files din ya maida masa da original. Turhan be yarda sun kara minti talatin a gidan ba ganin sun samu abun da suke nema suka kama hanyar address din da ya ba su, sai kuma suka yi rashin sa'a mutanen sun tashi daga gidan sai yan'uwansu suka tarar, a nan ma addireshin sabon gidan da masu gidan suka koma Turhan ya karba, sannan suka kama hanyar Ikorodu daya daga cikin unguwanin da suke da nisa sosai a birnin Lagos. Sun isa da yamma sosai, suka buga kofar gidan mai gadin ya leko ya tambaya su waye su. "A wa lati okere lati ri oluwa ile." Faruk ya fada musu da Yoruba cewar mun zo ne daga nesa muna son gani mai gidan. "Ya sunan mai gidan? Mai gadin ya tambaya, Faruk ya duba takardar copy dake hannunsu. Mr Chibuike Adanna okay ku jira ina zuwa Ya shiga cikin gidan babu jimawa ya fito yana tambayar daga ina suke. Arewa Faruk ya amsa masa, babu jimawa aka musu izinin shiga cikin gidan aka kaisu falon matar gidan kasancewar mai gidan baya kusa a lokacin. ________________ Maganar gaskiya Kameela fa tana da gaskiya akan mijinta Me kuke hangowa idan Turnan ya samu haduwa da Emily? [4/20, 10:01 AM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL ABOKIN RAYUWA