Sashe 90
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi min maganarki, duk da yake bata fito min a fili ba, amman na san karshen zagayen zai dawo akan ki ne" Ya ciro wayarsa yana tabawa. "Kamin ke Ammy ta hada ni da mata da yawa na fada mata ba su min ba, amman ke na ga alamar da gaske take, dan haka ina son idan ta tunkare ki da maganar ki fada mata na fi karfinki kina tsoron aurena, domin na fi karfinki din ina sa matata kyakkyawa marar jiki, ke kuma kin zama wata uwar mata mace mai kiba bata burge ni, kuma ni sarauta ne idan Ammy bata duba wannan ba ke ya kamata ki duba, kaskanci ne a gurina na auri wacce ba yar sarauta ba balle kuma tubabbiya macen da musulunta ta yi ba wai ta tashi a cikin addinin ba ne, and you're not my type, kuma ga ki da yaron da da Allah kadai ya san gaskiyarsa, and Aisha baki da dangi ba ki da kowa, ni kuma dan dangi ne jinin sarauta mai asali kuma musulmi gaba da baya, irinku sai dai kawai su zo mana a matsayin masu aiki ko kuma bayi, amman ba sa aka ko matar aure ba, mahaifina ma ba zai aminta ba, ba zan iya tunkararsa da magana irin wannan ba, Ammy ma dai ta kasa ganewa ne shiyasa har take kokarin hada kifi da kaska" Na daga kai na kalleshi. "Dan haka ina son idan ta miki magana karki amince mata, kuma karki ce mata baki so na domin ta san karya ne wata mace ta kalleni tace bata so na, kawai dai ki fada mata na fi karfinki ba zaki iya cusa kanki a rigima ba, kuma kina da a ke kin san ko haihuwa na yi da ke Allah ya kiyayye ba zan taba son abun da na haifa da ke ba balle kuma dan da kika zo da shi, na zo garin nan da niyar na yi wata biyu ko uku gurin Ammy amman saboda ke next week zan koma, i hate your face, idan aka cire Ammy ni bana ganin kimar ko wace mace bakar fata, iyakarmu da su su mana bauta mu ba su kudi" Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya fice daga dakin kofar dakin ma a bude ya bar min ita. Aiko a take hawaye suka ce min Emily yau ma dai zamu ziyarce ki, suka fara sauko min wasu na bin wasu babu tsayawa. Wai fa Turhan yana min haka ne saboda ina zaune a karkashin mahaifiyarsa, kowa yana juya ni ne saboda ina karkashinsa, da ace ina da gurin dazan raba Turhan ko dan Sarkin aljannu ne be isa ya fada min abun da ya fada min a yau ba. A ranar na daukarwa kaina alkawarin ba zan taba yafe musu abun da suka min na wufintar da ni, kuma na dauki alkawarin kasancewa da nawa Yaya a kowane irin hali. Daga ranar sai ya saka min tsoron sa bana ko son fitowa falon saboda kar na ganshi, domin gabana faduwa yake da zarar na ji kamshin turarensa balle kuma ace na yi arba da shi. Da aka kwana biyu Ammy ta ga haka daga gareni sai ta shigo dakina ta same ni tana lallabani wai kar na lalata mata shiri gashi ta fada masa abun da take buri kuma amince sai kuma ni na kirkiro wannan halin a yanzu. "Aisha ko dai baki son shi?" "Sai na kasa amsawa, amsawa bana son sa yana nufin fasa auren da take nufin hadawa amsawar bana son shi yana nufin butulcewa hallacin da ta yi min na tsawon shekaru biyu, yana nufin rusa burinta na son samun danta a kusa da ita, taya ya zan iya mata haka? Wannan dalilin ya saka na boye nawa kunci na so farincikinta fiye da nawa, abun da ban sani ba ashe ina dabawa kaina wuka ne a kahon zuciyata da kaina" "Ki kwantar da hankali, kar wani abu yasa ki fara tunanin Turhan zai zo miki kamar Khaleepa sam ba haka ba ne, yanzu haka na yi magana da shi ya nuna min tausayinki sosai kuma amince zai aureki, kuma zai rike ki amana, amman ya ce na fara tambayarki idan kin amince saboda kar ya zama an cilasta miki, na fada masa tun kamin ya dawo na yi magana da ke amman zan sake samunki da maganar" "Allah ya ba mu zaman lafiya" Shi ne kawai abun da na fada ta amsa da amin ta rumgume tana farinciki da jindadi. "Ya fada min wata biyu yake son yi, amman mahaifinsa ya kira shi akwai wani buki da suke a can duk shekara zai tafi a satin nan albashi idan sun gama sai ya dawo, dan haka nake son a daura aurenku a satin nan, sai ku tafi tare, abar min Ibrahim har sai kun dawo tukuna" "Tohm Ammy" "Allah ya miki albarka" Jindadin da na gani a fuskarta yasa ni jindadi duk da ina fargabar abun da zan tarar. Turhan ya so gyara kansa a gurin mahaifiyarsa ne ta hanyar nuna masa ya amince da kudurinta ni kuma ya buga da kasa ta hanyar amfani da ni na fadawa Ammy ba zan aure shi ba, daga nan zata fahimci na mata butulci wata kila ma ta kore ni ko kuma ya karyata labarina. Washe garin ranar da aka yi haka Ammy ta bukaci dole sai na fito na yi karin kummalo a falon wai saboda ni da Turhan mu kara fahimtar juna. A dole na fito na karya a gurin muna cikin karyawar ne take mana addu'a da fatan alheri tare da nuna jindadinta na yadda muka bata hadin kai. "Allah ya hada kanku ya ba ku zaman lafiya, sa na yi nufin a hade aurenku da na kanwarka (yarinyar da Ammy take riko) amman saboda uzurin da ya same ka yanzu zan tafi family house a yau na yi magana da su na abun da ya kamata, sai a daura auren albashi a bar bikin sai idan kun dawo sai ayi komai cikin natsuwa da kwanciyar hankali" "Eh haka yayi Ammy" Ya amsa mata yana murmushin dole. "Bari na barku ku ci abincinku, zan tafi na shirya na tafi gurinsu Hajiya" Ta mike tsaye ta fice daga dinning din, fitarta ke da wuya Turhan ya kalleni ya ce. "Ba dai kin amince da wannan auren ba? Sai kin ci ubanki" Ya wurgar da spoon dinsa ya fice a fusace, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, domin na shiga tsaka mai wuya idan na fasa auren nan Ammy zata ga laifina, idan kuma na amince ba dadinsa zan ji ba. Ta bangaren iyayen Ammy ma murna suka yi suna nuna farincikinsu, ba a fara shirye shiryen komai ba sai da Turhan ya bukaci ayi min gwaji, aka gwada jinina da na shi dukanmu bama dauke da kowace kalar cuta da zata dakatar da aurenmu. Haka bi dare ina raya shi da kuka da tunani kala kala har zuwa ranar da Ammy ta shigo min da kaya masu dubin yawa akwaiti goma sha biyu a matsayin lefe na, lefen da aka hada gurin Khadeeja Candy Store, sannan ta danka min dubu dari biyar a matsayin sadakina, ko bata fada min ba na san ita ta biya sadakin ko wani nata, domin bani da kima da martabar da Turhan zai siye da ni da sadaki mai tsada haka, a dan kankanen lokacin Ammy ta saka aka fara min gyaran jiki. Ranar Jumma ah aka daura mana aure bayan saukowa daga Sallah Jumma ar mai raka'a biyu, ina zaune garden din gidan tare da mai kunshin da Ammy ta kira ta bukaci ta yi min lalle mai kyau. Mai aikin Ammy ta shigo tana rangwada guda da murna ta sanar min an daura aurena da Turhan, a take na ji gabana ya fadi wani abu mai kauri da zugi ya tunkari zuciyata ya tsaya, tun daga wannan ranar har yau wannan abun be sauka ba. Kusan zan iya cewa auren dole Ammy ta yi min da Turhan domin bana son shi tsarin rayuwarsa gaba daya be yi min ba. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [6/25, 9:02 PM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ABOKIN RAYUWA