Sashe 17
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da na shiga masarautar ban saka mijina a idona ba sai da aka yi sati biyu, idan na fito cikin masarautar sai na fuskanci wulakanci, ba irin wulakanci na bawa da sarki ne, wulakanci irin na banbancin launin fata, wulakanci irin na wanda aka kyauta a gurin da ba a da bukatarsa, na fuskanci tsangwaba domin yarenmu da na su ba daya ba, kusan babu wanda ya san an auro a wajen masarautar domin ba a fita da ni, ba a nuna ni a matsayin surukar gidan, sai matar da na tarar wato uwargidana Maimunatu, surukarna suna wulakanta ni mijina da abokiyar zamana ma haka, ko da rana daya ban taba fadawa mahaifinta halin da nake ciki ba saboda bana son ya ji cewar ya zaba min abun da be dace ba Ta rufe ido hawaye na sauko mata. Shiyasa nake matukar tausayin Aysha, ni kadai na san irin tsangwamar da ta fuskanta a masarautar, domin na san yadda abun yake, gashi kuma Turhan ya watsa min kasa a ido ya tsaba alkawarin da ya daukar min Ta bude ido har lokacin hawaye ke saukowa daga idonta, ta mike tsaye ta nufi kofar falon ta bude ta shiga, kai tsaye ta nufi stairs ta shiga dakinta. EMILY POV. Ta kara minti talatin akan lokacin da Amal ta fada mata na shigowa office, domin ta shigo kamfanin karfe bakwai saura mintuna na safe, a tare suka nufi elevator ita da mutumen da suka shiga wacan karon, wannan karon ma a tare suka shiga, ta rasa dalilin kaddara na hadata da wannan mutumen, ko da yake a kamfanin yake aiki kamar ita, dole za su rika haduwa ko da bata so, kamar yadda za ta yi ta haduwa da mabanbanta mutane a gurin. A yau din bata cikin walwala da zumudi kamar jiya, saboda danta dake can kwance a asibiti, gashi kuma yarta Fatima na fushi da ita, thirdly kuma bata samu wadataccen bachi ba, ga gajiyar aikin jiya tattara a jikinkinta, sai ya zama mood dinta ya canja gaba daya, ta sama silent ba kuzari. Good Morning Ta gaishe shi saboda tana son ta yi masa tambayar da ba lallai ne idan ta yi ma Boss dinta Amal ta amsa mata ba. Aliyu ya kalleta kawai ya dauke ido ba tare da ya amsa mata ba, hakan kuma ya harzukata. Daman fa tambaya ce kawai zan yi, karka yi zaton ko ina son kullum alaka da kai ne ko wani abu makamanci haka, haduwar da mu ke kaddara ce ke hada mu, ba wai dan ina son haka ba, ni maza ba burge ni suke ba, so ka sauke girman kan please Ya juyo ya kalleta a nan din ma ba zai iya karyata kyaunta ba, amman ba zallar kyaun yake kallo ba yadda take bulbule shi da masifa a duk lokacin da kaddara ta hada su ne yake mamaki. Daman zan tambaye ka ne, ko bakon zuwa ma'ana new comer zai iya daukar hutu saboda wani uzuri na rashin lafiya Nan din ma be jin zai iya amsa mata, sai kallonta da yake kamin ya dauke kansa. Da yaren turanci take masa magana, sai dai ganin be amsa ta ba ya saka ta wani furuncin da Hausa. Wato dai ma'aikatar nan kowa dan iskan kansa ne, kowa jin kansa yake, na tambaya wata kila shi ma sabon dauka ne kamar ni, sai kallona yake babu amsa kamar kurma, idan na sake magana kace min aku Wannan karon be kalleta ba, be kuma bar murmushin zuciyarsa ya fito a fuskarsa ba har suka tsaya a 4 -floor. Ta saka kafa zata fice Tambaya kawai mutum yayi maka shiru kamar kurma Ta fada da Hausa. Ya furta a daidai lokacin da Elevator ya zo rufewa, ya furta mata hakan ne saboda ta san yana jin yaren da ta yi magana da shi. Sai ta juyo da sauri ta kalli elevator da already ya rufe, zuciyarta na bugawa da karfi, sai a lokacin tunani ya zo mata, what if shi babban ta ne a gurin aikin? Wata kila yana a hawa na 5 ne ma ko kuma sako yake kaina, amman be yi kama da karamin mutum ba. Bata dauka yana jin hausa ba, a tunaninta Igbo ne ko yorba, shiyasa bata yi magana da duka yarukan ba sai hausa, bata yi tsammanin a kusa zata samu mai jin hausa ba kamar ita ba, ko da yake ita ma zama a arewa ne ya saka ta kware a hausar ba mamaki shi ma ya zauna a can din ne. Idan ba haka ba Parthcourt da Zamfara ai akwai nisa sosai, a take ta tunatarta kanta abun da ta manta, kamfani ya kan hada mutane kala kala wasu ma daga wata kasar wasu kuma daga wasu yarukan. Fargabar rasa aikinta ko janyowa kanta wata sabuwar matsalar ya hanata ta sukuni har ta gyara office din Boss dinta ta gama, duk kuwa da wani bangare na zuciyarta yana raya ba wani babba ne a kamfanin ba, domin bata taba ganin wani ya rako shi ba, haka kuma zuwan da yayi da safen nan ya fahimtar da ita haka, domin da babba ne a kamfanin ba zai shigo a irin wannan lokacin ba sai 10 ko 9am kamar yadda Amal take shigowa, wannan tunanin ya yaudari zuciyarta har ta samu sukuni. ALIYU POV. Kusan duk wanda ya san shi fari sani a kamfani ya ga shigowarsa a irin wannan lokacin zai yi mamakin haka domin be saba shigowa a irin wannan lokacin ba. Ya wuni da tunanin matar nan da sake gani a yau, yadda halshenta yake iya furta hausa da kyau haka ya nuna alamar ta taba zama arewa ko kuma daga arewar take ma, sai dai abun da ya daure masa kai siffarta gashin kanta ba sun sanar da duk wani mai kallonta cewar ita din baturiyace, haskenta yayi yawa blue eyes dinta da jan gashinta ya fahimtar da shi haka. Sai dai ya kasa tantancewa shin ita din ce matar da abokinsa yake nema ko mai kama da ita? Idan har kama ce ta ina taya sunan zai zama daya Aisha? Ta ya idon da gashin zai zama hali da jikin ne kawai zai banbanta? Sau hudu yana daga waya zai kira Turhan sai kuma ya fasa domin ba shi da wata kwakkwaran hujjar da zai rike cewar matar da yake gani a kamfaninsu ita din ce matar da Turhan yake nema, idan tsabanin haka ne zai wahalar da abokinsa ne, saboda haka yana bukatar hujja, domin Turhan ya fada masa cewar ita wacan tana da jiki kuma bata da masifa gashi bata yi boko ba, ba kamar wannan ba. Ko dai yan biyu ne, ya tambayi kansa sai kuma ya rasa wa zai bashi amsar. Misalin karfe daya ya shiga bandakin office din yayi alwala ya fito ya kashe Bluetooth din dake kunne yana fitar da kirar'ar Qu'ane ya shimfida carpet yayi Sallah, sannan ya mike tsaye ya fito daga office dinsa. Nick, if there are any newly recruited employees named Aysha, please bring their files to my office Okay Sir Ya bada umarnin sannan ya fice ya sauka kasa gaba daya, Elevator na budewa yayi arba da mutane biyar masu jiran budewarta ciki har da kyakkyawar karamar yarinya mai goye da jakar makaranta, tana sanye da uniform pink short skirt and White shirt, an yi mata parking din bakin gashinta a baya, tana ta kallonsa da blue eyes dinta kamar yadda yake kallonta babu kyabta ido. Zanen halittar fuskar yarinyar ya saka shi manta mutanen dake mika masa gaisuwa kuma suke jiran fitowarsa domin su shiga Elevator. [4/20, 9:58 AM] ABOKIN RAYUWA