Sashe 34
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 Ta hado tea ya kawo ma Ummi. Ni ba irinka bace, me zan yi da tea yanzu da yamma" Murmushi yayi ya zauna yana updating status dinsa domin sanar da duniya matarsa ta haihu amman dan be zo da rai ba. Bayan ya gama ya aje wayar ya kai hannu zai dauki tea kiran Kameela ya shigo wayarsa, fasa shan tea yayi ya dauki wayar. Hello... "Kana ina Ina gida Tare da wa?" Ya kalli Ummi sannan ya amsa mata "Tare da Ummi" "Na ji Hajiya tana maganar wai zata tafi da ni gida gobe idan an sallame ni Kamar al'ada ce ko mace ta koma gida idan ta yi haihuwar fari "Bana son na barka, ni bana son tafiya, za a iya min komai a nan mana" "Haka ne amman idan ta nuna tana son tafiya dake ba zamu iya hanawa ba Ina son idan ta maka maganar tafiyata kace mata aa kana son na zauna a nan din" Yayi shiru be ce mata komai ba jin hakan ya saka ta kashe wayarta, domin ita ma ta san mijinta ba kasafai take saka shi abun da be yi niya ba. "Kameela ce? Bata son tafiya gida, ni kuma ba zan iya jayayya da iyayenta ba, bana son abun da zai kawo mana rashin jituwa musamman da Hajiya "Rashin jituwa na nawa kuma? Bayan wanda aka sha kamin auren? wacan ai ya wuce Ummi, kuma tun daga lokacin sun san ni ba kanwar lasa ba ne, Aliyu kike ji fa Ummi Ya fada yana murmushi, Ummi ta tabe baki. Aliyu soyayya? Romeo baban kauna, sharukan din masoya? Mai alkawarin da ba zai iya cikawa ba Ya kalleta da dan mamaki still yana murmushi. Ummi ina kika samo duk wannan kuma? Baka yi alkawarin cewar ba zaka kara ma Kameela abokiyar zama ba? Ya rausayar da kai. Ta fada miki ne?" Aa ai kasan iyayenta ba yan dattako ba ne, sun fada dan na ji kuma na ji" Ya shafa kansa. "Idan baka yi hankali ba, kishin Kameela sai ya halakata ya jefaka a matsala, domin zafin kishin yayi yawa, madadin kai kuma ka nuna mata abun da take yi kuskure ne sai kawai ka shimfida mata tabarma ta hau, akan wane dalili zaka mata alkawarin ka haramtawa kanka abun da Allah da kansa ya hallata maka? Kai da malami ne Aliyu, ban yi tsammanin wannan daga gareka ba Ummi baki fahimta ba ne Ummi ta hade rai. Toh fahimtar da ni Ya gyara zamansa ya aje wayarsa gafe. Ummi ke kika haife ni, kin san halina ciki da waje, tun kamin na yi aure ke kin sani, bana da ra'ayin auren mace sama da daya, Allah ya hallata mana auren mace mace sama da daya ne idan zamu iya adalci, shi kuma adalci wani abu ne mai nauyi sai dai mu kwatanta, ni kuma bana son na aikata wani abun da zan tashi a gaban Allah wani dan'adam ya tuhume ni da shi, kuma Ummi kin san iya gwagwar mayar da muka sha kamin iyayenta su yarda su ba ni aurenta Saboda an yi fadi tashi sai ya saka ka zo ka yi mata alkawarin da ni na san wata rana sai ka karya shi, mata na mahaifinta yake aure bayan Hajiya? Ina ce matansa uku, ai ta tashi ta ga ubanta da mata biyu ko bayan mahaifiyarta, sai kai dan ta raina ka zata saka ka yi mata alkawarin ba zaka kara aure ba, yan'uwanta ma saboda basu da kunya za su nemi fada min magana "Wata kila yanayin abubuwan da suke faruwa gidan su na kishin ne ya saka take tsoron kishiya, amman me Hajiya ta fada miki? Sun miki wata maganar marar dadi ne?" Ya tambaya yana jiran amsarta, karamin aikinsa ne ya daga waya ya kira Anty Shafa da take yayarta ya ci mata mutunci akan Ummi, bayan kuma abun be kai ya kawo ba. Wannan maganar suka fada mana, ni ba zance ka kara aure ba, domin Kameela bata min komai ba ta rike ni kamar uwa, family ta ne dai ba su da mutunci shiyasa ake son idan za'ayi aure a nemo yar gidan mutunci, ka karanta ka gani amman duk ka tsallake wannan ka aurota Kameela tana da tarbiya Ummi, tana da biyayya daliba tace fa, tana da ilmi daidai gwargwado, ita dai bar ta ga rashin sirrin sai kuma zafin kishi, kuma duk mace ba zata rasa wannan ba, kuma ni ba cilasta ni na yi mata alkawari ba, na mata alkawarin ne da yakinin zan cika kuma zan iya, saboda ina son kwanciyar hankalinta da farincikinta, kamar yadda Daddy na yake son matarsa Ummi ta watsa masa harara. Dan iskan yaro, ai ni ban hana Daddynku aure ba, kuma ban ce yayi min alkawarin ba zai kara aure ba, kawai be yi niya ba ne, waya isa ya hana Daddynku abun da yayi niya? Tohm Daddyna zan gado gamu gani ai, farin tuwon nan dai cikin bakar tukuyar can ya fito, muna nan da kai wata rana sai ka zo min jikinka na rawa kace zaka kara aure, saboda iyayenta ba yan mutunci ba ne, kuma ba su so aurenka da ita tun farko ba, na lura matukar ba kashe auren nan suka yi ba hankalinsu ba zai kwanta ba Haba Ummi ke ma kin san idan na auri mace ta auru Wallahi, aje dai sama a dawo a shiga wuta da ruwa a mutu ayi rai amman ba zan sake mace ba, noooo saki be ma cikin abun da nake magana, ni dai ina son matata, matata kuma tana so na to duk abin da zai biyo baya daman dole mu yi hakuri da shi Ummi ta tabe baki. "Allah ya baku zaman lafiya" "Ameen, Ummi ke ma yanzu dai kamar Kameela ta fita ranki" "Aa ina sonta, ai tana mutunta yan'uwanka kuma tana sonka tana girmamani, ni kawai familynta ne bana so, abubuwan da suka yi ta yi kamin aurenku har yanzu ban manta ba Yayi murmushi kawai be sake cewa komai ba, Ummi ta dauki wayarta tana amsa kira, shi kuma ya shiga amsa sakwannin dake shigo masa. Sai dare Ummi ta koma asibitin tare da Aliyu, Kameela ta tarbe ta da hannu biyu Ummi ta zauna kusa da ita tana mata sannu. Sai kusan goma Ummi ta yi mata sallama ta fita Aliyu ya mike tsaye. "Zan je na kaita gida na dawo, gobe zata wuce jirgin Safe zata bi" "Okay sai ka dawo" Ya matsa kusa da ita ya sumbance. "Sai wani shinning kike kamar ba haihuwa kika yi ba, kumburin nan ma ya miki kyau" Ta yi murmushi. "Ba zaka yi ma Hajiya magana ba? Ina jin tana maganar tafiyar fa, gashi sunce gobe za su sallame ni "Idan an tafi dake zan zo na same ki" Murda kofar dakin da aka yi ne ya saka shi aurin janye hannunsa a jikinta ya matsa baya. Anty Shafa ce ta shigo tana hamma. Yauwa Aliyu Hajiya tace ka hadowa Kameela kayanta a zo da su nan gobe za su wuce idan Allah ya kaimu" Ya kalli Anty Shafa fuska ba yabo ba fallasa, kamin ya juya ya kalli matarsa. "Me da me zan dauko miki my love" Ta dan bata fuska kamar zata yi kuka, ita ganin take idan bata kusa da shi zai kalli wasu matan ne, kuma kamar ta bashi damar magana da Emily ne. "Ba sai ka dauko komai ba, zan siya a can Yayi murmushi kawai ya fice. Sai da ya fita sannan Anty Shafa ta zauna tana fadin. Abun dai be yi ba, kin haihu ace uwarsa wai zata koma gobe gobe kuma jirgin safe zata bi, kamar dai bata sonki, shi kansa ban ga yana wani daukinki ba Kameela ta hade rai tana magana a shagwabe. Kin ga Anty Shafa ki daina zarga min uwar miji, kuma ni mijina yana so na na sani Gaki ga shi ai indai namiji ne, har zai miki alkawari ki yarda, ba gashi kin janyowa kanki ba har kin rasa danki? Farawa da iyawa kenan daga chat da mata sai zancen kara aure, muna nan dake sai Aliyu ya saka ki kuka da bakinciki, ba namiji ba, can talkaminmu suka tsinke" Kameela dai ta yi shiru bata ce komai ba, sai dai ranta babu dadin tafiyar da zata yi da kuma kalaman da Anty Shafa take fada akan mijinta. Aliyu be dawo dakin hannu sake ba sai da kayan kwalama da kuma akwati daya babba ya saka mata abubuwan da ya san za su mata amfani, ko ba su fada masa ba ya fahimci ba su son tafiya gidansa ne shiyasa suka ce ya hado mata kayan, madadin ita yayarta ta tafi ta hado mata kayan, shiyasa Hajiya take son da am sallameta ta wuce da ita daga nan ba tare da sun tafi gidan ba. Shi kuma be shirya wulakanta kansa ba, ko neman rigima da su ba shiyasa, be musa musu ba ko ya nuna musu damuwarsa akan yunkurinsu. Da kansa ya hada nata wani tea mai kauri ya bude naman da ya zo mata da shi har tiriri yake yana saka mata a baki. Yanzu ya aka yi da Emily din? Kuma taya aka yi ma ka gane ta? Anya zai iya fada mata a gurin da yake aiki take aiki? No.. Ya tambayi kansa sai kuma ya bawa kansa amsa. Hotonta ai ya bada yanayi da kamaninta, kuma kana ganin yarta zaka san yar Turhan ce domin fuskarsa ce Meyasa ba zaka fada masa ba, bayan kasan yadda yake ta nemanta Ya kai mata tea a baki. "Ita ta bukaci kar na yi haka Saboda me? Wata kila tana da dalinlinta Dan Allah ka fita sabgarta ka cire kanka a tsakaninsu, ba a shiga tsakanin mata da miji ni dama ace be saketa ba abun zai fi min sauki" "Saboda ke zaki hada aurensu? Dan Allah masoyiyata ki bari mu rabu tafiya, karki saka kanki a wata damuwa dan Allah, ke kin san wanene, kuma yaushe na ce miki ya sake ta." "Au be sake ta ba? Au to da sauki ai" Yayi murmushi yana kara jinjina lamarin Kameela, shi dai