Sashe 158
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
A-B ya ciro daurin dollars a aljihunsa ya aje kasa. "Zan fi kowa farinciki idan ta amince, kuma ace ni na biya sadakin kanwar nan tawa" Emily ta sake daga kai cikin tsananin damuwa. "Dan Allah ku gafarce ni, kuma ku fahimce ni, bana nufin bata ran kowa, bana nufin zubar da kimar kowa, na yafewa Turhan amman hakan baya nufin na yarda na aure shi, Wallahi ba zan iya zaman aure da shi ba, akwai wanda na so" "Wake kike so?" Alhaji Bulama ya tambaya, sai ta yi shiru. "Ki bude baki ki amsa mana, ko a addinin musulunci bazawara amsawarta ake amfani ba shirunta ba, shiru na budurwa ne, haka Annabi S. A. W ya fada" Daddy ya ji kamar yace kar ta fada. "Aliyu..." Ta furta a hankali, falon yayi tsit na tsawon lokaci, kamar babu wani abu mai rai a ciki, tsabar jin nauyi Daddy ya ji kamar kasa ta tsage ya shige ciki. Turhan ya mike tsaye ya fice falon ba tare da ya kalli inda Emily take ba zaune ba. Sarkin Sudan ya tsare ta da ido. "Kin san mutanen da suke zaune a gabanki kuwa yarinya?" Emily ta fashe da kuka ita kanta bata nufin watsa musu kasa a ido. "Ku gafarce ni dan Allah? Ku fahimce ni ku taimaki rayuwata, ku bar ni ni ma na yaki iskar yanci" Sarkin ya mike tsaye bayan an fassara masa abun da ta fada ya fice tare masu rakiyarsa. "Amman baki yi kyauta ba, kuma ba mu tsammaci haka ba" Cewar Alhaji Bulama sannan ya mike tsaye ya fice, tare da rakiyar Mahaifin Kameela. Dr A-B ya kalli Emily dake ta kuka ya sakar mata murmushi. "Aliyu kike so?" Ta daga mishi kai. "Share hawayenki na miki alkawari ba zan bar garin nan ba sai an daura aurenku, ni ma kamar uba ne a gurinki ai zan iya bada aurenki, na nufin biyan sadaki ba zan fasa ba" Ya juya ya kalli Daddy ya tura masa kudin. "A rike wannan a matsayin sadakin Emily, a sanarwa duk wanda ya kamata a sanarwa, zan tafi na dawo daga can zan sanar da Madam Baraka, anjima kadan zan dawo za a daura aurenta da wanda take so, ni dai burina ta kasance cikin farin ciki, amman a tabbatar da shi ma yana sonta gudun abun da zai je ya dawo kar ya cutar mana da ita" Ya tashi shi ma ya fice, Daddy ma mikewa yayi tsaye ba farinciki ba bakinciki domin shi ma be ga dalilin da zai saka ayi ma Emily dole ga abun da bata so ba. Emily kadai aka bari a falon tana rusar kuka, bata sani ba ko shi ma Aliyun ya juya mata bayan ta watsa ma manyan mutane kasa a ido. Ummi ce ta shigo da kanta ta kama Emily ta fita da ita bayan Daddy ya fada mata abun da ya faru. Daddy ya sanar duk wanda ya kamata ya sani cikin kankanen lokaci, Dr A-B ya tafi kai tsaye yayi magana da Madam Baraka ya fada mata abun da ya faru, sai ta daga waya ta kira Emily ta sake tambayarta da gaske Aliyu take so Emily ta amsa mata da eh. Kamin a daura auren sai da Daddy ya jira Aliyu ya tambaye shi ko yana son Emily. "Eh ina sonta Daddy?" Ya amsa kai tsaye babu boye boye babu kwankwanto, gabansa sai faduwa yake ba kamar ya san wainar da ake toyawa. "Tohm za a a daura aurenku, daga baya abubuwa za su biyo baya" "Na gode Daddy Allah ya ba ni ikon sauke nauyin da za a dora min" Daddy ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba. Sannan ya sanar da Ummi yadda suka yi, Ummi ta shigo ta ta sanar da Emily halin da ake ciki yan'uwan Daddy da nata duk sun hallara gidan. "Anjima idan an fito sallah La'asar za a daura aurenku da wanda kike so Aisha" Emily ta kalli Ummi tana kuka. "Allah kasa ya rike ni amana..." Ummi ta kama hannayen Emily tana hawaye. "Wallahi ko ba ni da rai Aliyu ya ci amanarki, ban yafe masa ba..." Emily ta kwantar da kanta jikin Ummi, Ummi ta rungumeta tana amsa sallamar Mama Baraka. [8/21, 10:14 PM] ABOKIN RAYUWA