← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 177

Sashe 156

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 6 A lokacin da ta shigo falon bata samu kowa. a cikin ba, hakan ya bata damar nufar dakinta kai tsaye ta shige ta cire hijab ta kwanta kan gado ta aje wayar Mama Baraka ta bata a gafe ta kai flower Aliyu a hanci tana shakar kashin dake jiki sai lumshe ido take fuska dauke da murmushi. A rayuwarta bata taba haduwa da wanda ya iya sarrafa halshe ya karantar da ita sabon karatu ba kamar Aliyu, idan ta ce be tafi da zuciyarta ba ta yi karya. "Ashe kin dawo" Ta bude idon da sauri ta tashi zaune ta boye fulawa a bayanta, tsabar shauki ya mantar da ita yadda ake rufe kofar daki, bata san a sake kofar take na sai da Ummi ta shigo. "Eh na shigo baki falo" "Ina daki ne, toh ya kuka yi?" "Bata amince ba, tace ta fi son na zauna a tare da ita" Ummi ta sauke ajiyar zuciya. "Daman na yi wannan tunanin, ita ma ya kamata ta samu lokaci da ke ai, kuma Abuja babu wani nisa idan kika so ganinmu za ki iya zuwa" Ta yi shiru sai kuma ta mika hannu ta dauko wayar da Mama Baraka ta bata. "Ta ba ni waya" Ummi ta shigo ta zauna ta karba tana murna. "Maa Shaa Allahu" A nan suka bude ashe har da sim ciki ba su sani ba sai lokacin, Emily ta yi kamar ta fadawa Ummi ta ga Vito a yau sai kuma ta yi gudun kar hankalinsu ya tashi musamman idan Aliyu ya sani. "Allah yasa alheri ya tsare, sai kin gama gani sai a saka miki numbobinmu" "Tohm Ummi" "Kin ga Tasmia?" "Eh ta ba ni katin aurenta, a can ma na bar shi waje ina jin" Ta fara duddubawa bata ga Iv ba. "Ai kara da kika jefar babu amfanin tafiya bikin ai, kawai dai saboda ta matsa ne yasa na ce Aliyu ya hakura ya barta ta zo, ai neman yafiya ne ba wani abu ba, amman kin san yaron nan ba shi da ta ido fa ta zo sai da ya saka Nafeesa ya bincike ta? Baiwar Allah har tausayi ta ba ni" Emily ta yi dariya kamar yadda Ummi ma take dariya. "Haka ta fada min" "Kin san Aliyu be son abun da zai same ki, be yarda da ita ba ne gaba daya" Ummi ta sauka kan gadon ta mike tsaye. "Bari na barki ki huta sai kin fito" "Tohm Ummi" Emily ta bita da kallo har ta fice tare da ja mata kofar dakin. Downstairs Ummi ta sauko. "Ta fada maka Hajiya Baraka bata barta tafi tare da mu ba?" Aliyu ya aje red apple din hannunsa. "Ban tambaye ta ba" "Daman na yi wannan tunanin shiyasa ban kwallafa rai akan tafiya da ita ba, idan ma Hajiya Baraka ta yarda ba lallai ne Ammy ta yarda a tafi da Fatima ba? Ka duba ka ga gaba daya ta dauke hankalin yarinyar nan daga gidan nan, ba dan ma Aisha tana da hakuri da kai zuciya nesa ba da Allah kadai ya san damuwar da zata shiga ko matsala" "Ummi ni bana ganin laifin Ammy fa, tsakani da Allah ke kanki kina son jikoki balle ita da Turhan kadai ta haifa, kuma an dade babu abun nan, sannan a inda take ma ita kadai take zaune, taya son abokin hira ai" "Haka ne kuma, Allah ya kyauta" "Ameen, yanzu tafiyar ke kadai zaki yi ta kenan?" Ummi har ta wuce ta juyo. "Ban gane ni kadai zan tafi ba? Ga Nafisa ga ka" "Aa ni ba zan tafi ba, ni da ke koyawa Ayusher karatu? Bata gane karatun kowa sai nawa, idan na tafi wa zai koya mata?" Ummi ta tabe baki tana murmushi. 'Yanzu na yi magana yace ba sonta yake ba, kake koya mata karatu ko dai kake koya mata soyayya' Ta fada a ranta a fili kuma sai ta ce. "Kadai tsoron kake ka tafi wani ya rutsa dan ginin da ka fara ko?" Yayi murmushi "Ai ni idan na yi gini a filin da yake nawa babu mai iya rusa shi Wallahi, bana bada kofa balle ma kuma wannan yarinyar Ummi?" Ummi ta kara tabe baki. "Uhm uhm an duniya haya in taba, Allah ya baka ikon cigaba da tausayinta kamar yadda ka fada" Ta mike tsaye yana dariya ya fice falon. Ummi ta girgiza kai ta nufi Kitchen. "Daman ai na fada idan ta yi tsami ma ji, kullum idan aka yi magana sai kace tausayinta kake, kai ba zaka iya aurenta ba ko Turhan ya mutum yanzu me aka yi? Hmmm yaran zamani ana hango musu abu suna kaucewa, su karyataka" TURHAN POV. Duk wata hanya da zai bi ya fahimtar da mahaifinsa yadda yake son Emily da kuma yadda kasancewa da ita zai kwantar masa da hankali ya hada kan iyalinsa guri daya, ta hanyar auren Emily a karo na biyu ne kawai yake jin zai mallaka masa Fatima a kusa da shi, abu ne mai wahala Ammy ta yarda ya zauna da Fatima a Sudan, amman idan da Emily ba ba shi da haufi, baya ga haka kuma baya ra'ayin wani ya kasance da matarsa sai shi kadai. Da mahaifinsa ya fahimci abun da zuciyarsa take muradi sai ya karbawa bukatarsa. Ya fahimcin hankalin dansa baya a tare da su a yanzu, domin an maido masa matarsa an shirya tsakaninsu ya fahimtar da ita kuma ta yi masa uzuri, amman tunaninsa fa hashensa kullum yana gurin wacan matar ne da be da tabbacin zata dawo gareshi. Ya saka mahaifinsa a gaba ne, da neman yayi masa ruwa da tsaki saboda yana ganin idan mahaifinsa ya wuce masa gaba Emily zata samu, yadda yake gani za a bullo ma lamarin abu ne mai wahala Emily ta tsallake tarkonsa. Kamin su bar kasar Sudan sai da mahaifinsa ya kira Alhaji Bello ya fada masa bukatarsa da kuma rakiyar da yake son yayi masa, Turhan ma da kansa ya sanar da Dr Adam yadda suka shirya komai, ya fada masa yayi hakan ne saboda neman yafiyar Emily wata kila idan yayi wannan zata yafe masa. Dr A-B ya ba shi goyon baya dari bisa dari kuma ya tabbatar masa da cewar tare da shi za'ayi tafiyar. Sosai kaunar Emily ta kama Turhan kusan da ya ji labarin musuluntarta ta gurin Fatima yayi murna yayi farinciki sosai. Sati daya da yayi a garin sai yake jinsa kamar shekara, tunaninsa yana kan Emily ne, har ta kai idan ya kalli matarsa sai ayyana da ma ace Emily ce, ko kuma idan Emily ce ga yarsu ga ta farincikinsa ya cika. Idan kuwa zuciyar ta tuna masa Aliyu yana can yana kalla masa mata sai ya ji kamar ya hade zuciyar ya mutu saboda kishi da bakinciki. Babu daren da baya mafarkin kasancewa da Emily, idan ya zauna shi kadai shiru baya tunanin komai sai nata, idan ya fita aiki tana nan a ransa, wasan dokin da yake idan yana yi sai yayi ta ayyana yadda zai koya mata wasan idan ta kasance matarsa. Be fadawa Mahaifinsa cewar ba da aure aka haifi Emily ba saboda baya son mahaifinsa ya yanke kudurinsa ko ya ki goya masa baya, ya fada masa mahaifinta Bature ne kuma ba a kasar yake ba, mahaifiyarta kuma tana auren wani yaron abokinsa wato Bulama Bello step father din Dr A-B, ya fada masa uba daya suke da Dr A-B, ya kuma fada masa a yanzu tana zaune idansu Aliyu ne, sun yi makirci sun zaunar da ita gidan saboda ya kar ta koma gurinsa. "Za mu nema maka yafiyarta da kuma aurenta gurin Ahji Mudallab, ba zan yi zuwa biyu ba" Da mahaifinsa ya fada masa haka ba karamin dadi ya ji ba, domin hakarsa ta cin ma ruwa daman abun da yake nema kenan Shi ma mahaifinsa ya gama sallamawa da fahimtar irin son da dansa yake yi ma wata mace da ba jintsi da jinin larabawa ba. Turhan kam yana ganin ta ko'ina an daure Aliyu da iyayensa kuma an saka Emily a tsakiya ba zata iya cewa a a ba. Ta waya yake labartawa Ammy komai idan kuma yana video call da yarsa sai ya fada mata yana dawowa zai je ya dauko Emily za su dawo su zauna guri daya. Sarkin Sudan da kansa ya daga waya ya kira Mahaifin Aliyu ya sanar masa za su neman yafiyar Emily a gidansa, a ciki satin nan da zai shigo. Saboda ya kyautata musu ya aje uzurinsa ya sanar da Ummi cewar ta daga zancen komawarta Abuja a satin zuwa Next week saboda zai dawo Kaduna a satin, sai dai be yarda ya fada mata ko Aliyu cewar iyayen Turhan ne za su zo ba, yayi hakan ne saboda gujewa Ummi ko Aliyu su fadawa Emily ko su shirya wani abun da zai zama laifi a gurin Turhan. Dan haka ya zabi shiru da bakinsa ba tare da ya fada musu dalilin dawowarsa ba. Mahaifin Aliyu ya sauka Kaduna on Saturday, Sarkin Sudan ya sauka Abuja on Saturday tare da Turhan da yan rakiyarsa masu fassara masa daga hausa ko turanci zuwa larabci, a gidan abokinsa Bulama, sun samu kyakkyawar tarba a daya daga cikin manyan masaukan baki da Bulama yake da su, abinci aka kawo musu kala kala tun daga kan na Nigeria har zuwa na kasar Sudan. The following day suka suka shiga private jet na Alhaji Bulama zuwa garin kaduna, Dr A-B be fadawa Emily za su zo ba, duk kuwa da kasancewar tana kiransa akai kai da sabon layinta da Mama Baraka ta bata. Sai yayi tunanin ko Mahaifin Aliyu ya sanar musu da zuwan, sai dai duk da haka be yi mata maganar ba saboda yana son ta ganshi as surprise kamar wacan karon. Even Mama Baraka bata san wainar da ake toyawa ba. Domin mijinta baya magana da ita, balle ya labarta mata cewar mai gidansa Alhaji Bulama zai sauka garin a ranar ta Lahadi ba, shi ne mutum na farko da ya fara isa filin jirgin ya tarbe bakin da aka sanar masa da zuwansu amman ba a fada masa dalili ba. Alhaji Bulama ya sanar masa ne saboda
Chapter 156 · 0% Book details