Sashe 171
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amman abubuwa sun yi sauki da na hadu da Vito, ya taimaki rayuwarmu kamin na rasa shi, ya rasu cikin ruwa ya fada ba tare da mun sani ba, da taimakon mijina an yi masa sutura an masa sallah an kai shi makabartar musulmi. Zancen yafiya kuma ba zan yafe ba, wannan shari'ar sai an yi ta" Hankalin Khaleefa ya tashi jin cewar an da aka haifa ya mutu, sai dai tashin hankalin be kai na jin furucin ba zata yafe masa ba. Shi da mahaifiyarsa da kawunsa da suka zo suka shiga bada hakuri. Aliyu ya mike tsaye "Khaleefa, ina tunanin zai fi kyau ku kuma inda aka ba ku masauki a yanzu, gobe da safe idan kun karya sai ku koma garinku, Ummi na da numberka zan karba, duk lokacin da hankalin Matata ya kwanta ta ji zata iya yafe maka zan kiraka" Khaleefa ya kalli Aliyu... "Ranka ya dade ka fahimce ni, idan na koma ba tare da yafiyar Aisha ba, ban san iya abun da zai faru a gaba ba, wata kila rayuwar ba zata kai lokacin da kake zato ba" "Amman tana cikin damuwa yanzu ba lallai ta yafe maka ba" Mama Baraka ta fada. "Bana cikin damuwa, na samu iyali yan'uwa da uwaye, ma samu miji ina da ya, rayuwa ta sauya na gamsu da abun da aka ba ni a yanzu, na gamsu da wannan sakamakon, kawai dai ba zan iya yafewa ba ne" Aliyu ya nunawa Khaleefa hanya yana jin kamar ya kai masa duka. "Please..." Khaleefa ya kalli Emily yana mamakin yau shi ke zaune a kasa tana kan kujera, yau shi yaje neman yafiyarta tana kin yafe masa, yau ita take da mijin da yake kira da maigidansa, ga duniya ta samu tana gida mai kyau gaba daya ma ta sauya kamar ba ita ba, babu wanda zai fadawa cewar ya taba aureta ya yarda. Baya son jayayya da Aliyu saboda ta bangarensa albashi ke shigo masa duk da baya tuka musu mota a yanzu. "Tohm na barki lafiya Aisha, ina jiran ranar da zaki yafe min, mun gode Hajiya" Ya nufi hanyar fita yana hawaye mahaifiyarsa kuma na kuka wiwiwi kawunsa kam tun da aka shigo ya ma kasa cewa komai. Bayan sun fita Mama Baraka ta kai hannu ta shafa fuskar Emily. "Dan Allah ina sake rokin yafiyarki, ki yafe min, duk ni ce silar shigarki wannan halin" Emily ta kwanta jikinta tana kuka, Mama Baraka ma kuka take tana kara jin tausayin Emily sosai. Aliyu ya sauke kansa kasa. Fatima ta nufi inda Aliyu yake tsaye "Wanene wannan? Ni ban gane abun da ake ba" "Mahaifin London ne" "Amman fuskarsa ta kone fatar wuyansa ta hade, gobara aka yi a fuskarsa?" Aliyu yayi murmushi ya duka ya dauki Fatima ya fice da ita yana mata hira. "Na Wahala, a baya rayuwa bata ana min dadi ba, na shiga tasko kala kala, an nuna min yama, babu wanda yake damuwa da matsalata, na zauna a gidan Khaleefa abun da zan ci ma sai ya gagare ni, sai na yi wankakau, ina jin ciwo ya hana ni zuwa asibiti sai a biyo kamar zan haifi shege, amman da amaryarsa ta samu cika suka rika murna, ni gaba daya ban haifi yarana da farinciki ba, mazan nan biyu ba su dandana min komai ba sai azaba da rashin imani, bana kaunar ko ayansu har abada... " Emily tana fada tana kuka. Mama Baraka ta kasa cewa komai saboda ta san ita ce silar komai da ace bata jefar da yarta ba da duk ba wannan labarin ake ba. Suna haka yar da Ammy ke riko ta shigo da sallama Mama Baraka ta amsa Emily na share hawaye, har ta gaisa da Mama Baraka ta tambayi Fatima idonta na kan Emily. "Fatima kamar tana waje ko? Tare da Aliyu" "Okay, bari na tafi daman na zo daukar ta ne, babanta yana can yana jira" "Okay tana nan waje" Ta mike tsaye sai Emily ta nuna mata ledodin dake aje gefen kujera. "Ki tafi mata da wannan kayan nata ne" "Tohm" Ta dauka ta fice. Aliyu be dawo falon ba sai da ya tabbatar hankalin matarsa ya an kwanta da ya shigo sai yake ta kallon fuskarta, baya son yayi zancen ta sake tuna damuwar kuma he need to hug her ko zata ji sanyi dan haka ya ce. "Bari mu tafi gida dare yana yi, direban ya dauki Fatima sun yafi" "Eh ta shigo nan ai, yarinyar da ta kawo ta, ban san ko za su sake kawota ko kuma aa" "Yace zai barta a gurin Ammy ai, idan tana nan da sannu zata dawo hannunmu, ita da kanta zata yi hankalin yin haka ai" "Haka ne, haka yayi miki Aisha? Idan ba miki ba ke ma kina da hakki sai a masa magana" Mama Baraka ta tambaya. "Yayi ko ba komai ya kula da yarsa ba kamar Khaleefa ba" Sai da suka kara bata minti talatin sannan suka yi ma Mama Baraka sallama daf da za su fita take tambayar yan'uwanta, Mama Baraka tace mata suna daki ita ta hana su fitowa saboda abubuwan da ta san za su faru. Emily ta shiga ta gaisa da su suna ta murnar ganinta har da rumgume ta sannan suka fito gaba dayansu suka rakota har gurin mota ta shiga. Da suka isa Aliyu ya bude mata mota ta fita ya saka hannayensa ya share mata hawayen dake mata zuba. "Kukan nan ya isa haka Qalbina" "Na tuna ana, da Vito ne taimake shi ba da Allah kadai ya san kalar wahalar da zai sake sha" Ta fada jikin mijinta tana kuka, sai ya rumgumeta yana shafa bayanta. "Indai zaki tuna rayuwar baya ne, zaki yi ta kuka da bakinciki ne, ki manta da komai dan Allah, bana son kukanki balle na ganki a damuwa" Ya duka ya saka hannunsa biyu ya dauke taya nufi kofar falon, da zai saka key ya bude kofar falon sai ta raba kafafuwanta biyu ta makale masa yayi sama da ita ya saka key din ya bude sannan ya tura ya shiga da ita, a hankali ya zauna kan kujera tana lake a jikinsa kamar yadda yara suke yana shafa bayanta, hausawa suka ce macen da ake so yar gata ce a gurin mijinta. Haka Aliyu yayi ta rarrashin matarsa kayan dadin daya siya mata ma daya dauko daker ya samu ta sha ice-cream din da ya fara narkewa ya bude biscuit ya bata piece daya ta ci ta kawar da kai. Ta kwana da tunanin abun da Khaleefa yayi mata da kuma London, hakan ya saka ta mafarkin anta, Aliyu na zaune kusa da ita yana lasa waya ya ga hawaye na sauko mata, sai ya kai hannunsa ya share, a firgice ta farka sai da ya rike ta. "Lafiya? I'm here no one can hurt you" Ya dawo da ita jikinsa ya yi mata addu'a ya tofa mata ya shafe mata jikinta, sannan ya bude kur'ane wayarsa ya soma karantawa sautinsa na fita, har sai da bachi ya sake dauketa sannan ya aje ya lullube matarsa ta kashe wutar dakin ya rumgume sosai yadda ba zata ji tsoro ba. Ya san ta kwana da zazzabi saboda a kirjinsa ta kwana jiya, dan haka be bari ta shiga kitchen ba shi ya shirya musu komai na karya, da ya kawo kuma ta gagara cin komai. Ya taba jikinta "Ki daure ki ci wani abu, sai mu tafi asibiti daman ina son muje tun last week, kawai ban miki maganar ba ne" Ya kai kunnensa bakinta. "Daure fada min, me kike so?" Ta kwanto jikinsa. "Kai nake so, Abokin Rayuwata my Soul mate" "Abu mai sauki, a soye kike so na ko gashe?" Dariya ta subuce mata ta daga kanta sama tana jin kaunar Aliyu, sai ya dawo da ita jikinsa yana murmushi. "Fada min mana" "A saka mai da yaji a bani na cinye kayana" "Na nawa kuma? Ai tuni kika cinye kurwar gangan jikince kawai ta rage, na miki na mayu" Ta saka dariya tana shafa fuskarsa, da dabara da waya da hira da janta da nishadi ya samu ta yi breakfast din da bata yi niya ba saboda ta farka jikin nata ma babu dadi bata ra'ayin cin komai. Kamin ya dauke ta zuwa asibiti sai da ya saka ka mata booking komai ta yadda da sun tafi ba sai sun wahala ba, haka kuwa aka yi suna zuwa ta hau layi gaba ta wuce ciki likita ta dubata ta yi mata tambayoyi sannan ta rubuta mata maganin da zata fara sha ta bata test din jini ta bata PT tace taje ta gwada idan sun koma gida, saboda Aliyu ya ki yarda ta yi fitsari a asibitin wai it's public place. Jinin kawai ya yarda aka bada sannan ya sauke ta gida ya tafi gurin aikinsa. The following day shi ya tashe ta bachi kamar yadda ya saba, ya saka ta yi fitsarin ya saka abun awon domin shi ya san yadda ake amfani da shi, ita kam bata sani ba saboda bata taba gwajin ciki ba sai dai kawai ta ganta da shi. A bathroom ya bar abun be sake shiga ba sai da suka gama sallah yayi mata karatu ta koma ta kwanta sannan ya shiga bandakin ya dauki abun gabansa na faduwa ya duba. Ya dube kansa a mirror yayi murmushi mai kyau ya jinjina kai sannan ya fice rike da abun ya isa inda take kwance yayi bedsheet din da aka siya gurin Khadeeja Candy ya kalli fuskar matarsa yana ayyana yadda yaransa za su yi kyau idan suka biyota. "Alhamdulillah... Alhamdulillah..." Ya furta sannan ya sumbance ta, ya shafa fuskarta yana hura mata iska a fuska. "Qalbina... Yi hakuri ki tashi... Ba zan iya barin ki ki yi wannan bachin ba" Ta bude ido daker ta kalleshi sai ya tada ita zaune ya rumgume ta, da ya ji hakan be masa ba ya mike tsaye da ita ya kwantar da kanta a wuyansa kafafuwanta makale a jikinsa. Ita dai ta yi lamo domin bata san wainar da ake soyawa ba. Daga dakin ya fito falo da ita ya zaunar da ita kan kujera ta ya zube gaban guiyoyinsa