Sashe 164
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 7 TALIYAR HAUSA YAR MURJI Abinci na gargajiya, ano na musamman, jin da in iyali! Idan kina/kanason abinci mai ano na musamman wanda zai tunatar da kai da in gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al ada ce mai ha a iyali, auna da jin da i a teburin gida. Me yasa za ka za i Taliyar Hausa Yar Murji? An yi ta da tsafta da inganci Ta dace da kowanne irin miya: miya mai wai, miya taushe, ko miya mai Sau in dafawa cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa Lafiyayye, mai sau in narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman Muna a Kaduna amma anonmu ya zarce iyaka! Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). Idan kana son jin da in abinci na gida wanda ke ha a zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa Yar Murji yau! wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. Ka more anon gargajiya mai tsafta, mai da i, mai orewa! TWO MONTHS LATER... "Ah gaskiya an gyara gidan sosai, Aliyu yayi kokari, iyayenta ma sun yi, ko ku kuka mata kayan da Ummi ta yi dariya tana kallon kanwarta Hajiya Larai. "Hajiya Larai, ba mu muka mata ba, mahaifiyarta ta karbe ragamar komai daga hannunmu, ita ta yi mata komai, da kam har na yi magana da Khadeeja Candy za mu siya kayan Kitchen ta mana breaking down na komai sai gashi ita mahaifiyar tace dan Allah kar mu yi komai mu bar ta ta yi, sai muka cire hannunmu, lefe kawai ta hada mana, sai na yi ma Hajiya Baraka Recommending dinta, indai ba ta canja ba ina tunanin gurin Khadeeja Candy aka siya komai na kayan Kitchen da bedsheet da curtain har frames ma domin komai saidawa take" "Mhn idan ba ke ba Ummi yaushe za ayi ma yarinya miji kuma ayi mata kayan dakin? Wannan ai shi ke nuna kin an bata sadakar Aliyu kenan, wannan uban lefe da aka zuba ai kam dole uwarta ta dafe ka cire ta a kunya" "Daman shi lefe idan namiji yayi ai kansa yayi ma, tun da shi za'ayi ma kwalliya, ba faduwa ba ce" "Haka ne, ta yi kokari gaskiya, dan kan an zuba kaya komai yayi gwanin sha'awa kam, kai kace ma dauko komai aka yi aka zuba kawai a ciki" "Ai Khadeeja Candy ce ba daga baya ba indai kaya ne, gurinta nake siyan tufafi Laces shadda, Atamfa abaya shoes kai komai fa, har adashe ma na ga tana yi, kuma a kawo maka komai cikin aminci da salama, facebook na fara haduwa da kayanta na gwada saya yanzu kam har mun zama regular customer" "Ikon Allah wasu fa suna da zafin nema, toh ita kuma a facebook take siyar da kayanta ne? Zan so na gwada dan gaskiya kayan nan sun burge ni" "Aa fa kin ji Hajiya Larai da wani zance, a ko'ina kika searching dinta za ki same ta, a TikTok ne, ko Instagram har Snapchat, ko a WhatsApp, amman fa ki tabbatar kin shirya siya" "Hajiya Larai ta yi murmushi, ta dauko wayarta Ummi na karanta mata number Khadeeja Candy wanda take whatsapp chat da ita. "0 8 0 3 6 1 2 6 6 6 0" "Zan dubata ta WhatsApp In Shaa Allahu, auren Maimuna da za'ayi sai mu siya mata komai a can ma, tana dai siyar da manyan kaya ko?" "Sosai, cooler daga 12k har ta dubu tari taskwas za ki samu a gurinta, ya danganta da abun da kike so" "Aiko zan gwada da yardar Allah" "Tohm Allah ya amice, ba da ke za a tafi karbar garar ba ne? Ko da yake kin ga dakin amarya har kin gaji" "Da ni mana, ina za a barku a baya, mun bada sadakar ango kuma ace ba za mu karbo gara ba?" "Wane irin sadaka Hajiya Larai?" "Ah yo sadaka mana mai sunan Mama, ke kin san idan ba Aliyu ba babu wanda zai kwashi wannan yarinyar nan haka, a aje zancen kyau a gafe a kalli asalinta" "Kin gani Hajiya Larai karki bar Aliyu ya ji zancen nan na ki, domin yana son matarsa idan kika fadi wani abu marar dadi akanta karamin abu ne ki ga ya sauya miki fuska, su shegu ba sa da zafi ko gata ne? Miye na su a ciki? Wannan zancen na cikin gidana ne, ni ban san miya ja ni na fada miki ba" "Aiko dai kin san ni bana barin ta kwana, amman ai ba nuna mata zan yi ba, ko shi ta kasa dai tana saka, tun da ke ma kin bi ina ni ina juya baya?" "Kawai ki musu f atan alheri, domin babu abun da zai raba su sai mutuwa da yardar Allah" "Tohm Allah ya sanya alheri, mu din ai sai da hakuri, ko'ina akwai mu, dangin miji ba, mu ga fari mu ga baki, mu koma gefe mu yi magana" Ummi ta tabe baki tana dariya. "Wanda be iya zama da ku ba kuke wahalarwa, wanda kuwa ya san ku ya karanci komai ya huta" "Heeeee Ummi.. Kuma fa haka ne..." Hajiya Larai ta kyalkyale da dariya ta mikawa Ummi hannu suka tabe. Sannan ta sauke kafa daya kan daya ta mike tsaye. "Bari na fita waje mu zauna kamin su iso" "Hajiya Larai jibila da cincin kawai za a kawo mana, kayan masarufi a kai ma angon abun sa" "Toh mu karba ne kawai na mu, ba za a raba ba sai kin ga komai" "Tohm shikenan" Ummi ta amsa tana Hamma, kusan tun da aka daura auren na Aliyu da Aisha Ummi bata huta ba, bata wannan bata wacan har aka yi wunin biki da walimar dare domin ya ki yarda ayi kida, haka yayi ko a aurensa na farko, Ummi ta yi zaton a wacan saboda fadi babu dadin da aka yi ta yi ne da family Kameela ya saka yace ba zai yi biki ba, domin su suka yi komai da ake na hidamar kida da raye raye kuma be halarta ba. A yanzu kuma ta gane haline na gujewa tsabawa Allah, ya fada mata ya sake jadada mata cewar Manzon Allah S. A. W ya ce Allah ya tsinewa duk wata ni'ima da Allah yayi ma bawa aka taru aka yi raye raye aka chakudu maza da mata, auren Emily na daga cikin ni'imomin da Allah ya yi masa dan haka na zai yarda ya rayu da ita a karkashin tsunuwar Allah ba, sai dai ba zai hana ta yi nata taron da mata yan'uwanta ba domin addnin ba haramta ba, matukar maza ba su gani ba kuma ba su chakudu ba. EMILY POV. Bata san miye auren gata ba sai da ta zama karkashin inuwar kulawar Aliyu. Daga ranar da aka saka musu rana tana karbar kyaututukan kauna da soyayya daga mijinta danginsa da kuma danginta. Sabon gidan da ya siya ma sai da ya dauke ta ya tafi ta ita ta duba komai ta fadi inda be mata ba aka canja, komai zai siya mata sai ya nemi zabinta, abun da take so shi za'ayi, bata taba auren wani ya lalaba kamar yadda Aliyu yake mata ba. Ko a lokacin da zai fada mata ba shi da ra'ayin yin biki ta sigar lalama ya biyo mata yana lallabata yadda zata fahimta kar ranta ya bace. Sai kuma aka yi sa'a ita ma bata da bukatar bikin saboda bata da wasu kawaye da zata gayyata idan ma za'ayi sai dai Mama Baraka ta yi na ta gayyatar. Haka kuma aka yi, Mama Baraka ta aikawa kowa katin gayyata da wuri, domin Emily ta dawo a sabon gidanta ne ana sauran wata daya biki. Danginta har wadanda suke nesa sai da suka halarcin biki. Emily ta ji wannan auren a dabam kuma ta kara fahimtar yadda rayuwa take tafiya, a wannan auren ne aka yi mata wankan lalle wanda ake yi ma ko wace budurwa a aurenta na farko, sai dai ita bata samu wannan damar ba sai a yanzu, ba taba shafa mata lalle ba sai a wannan karon, yan'uwanta mata da kawayensu ka shirya henna day wanda Aliyu ya dauki nauyi, domin bikin na duka mata ne babu maza. Anyi Walimar dare walimar data samu halarta manyan mutane daga bangaren Mahaifiyarta da kuma iyayen Aliyu da abokan arzikin Ummi. Ranar wunin biki Mama Baraka ta dauko masu masu kudin kwarya da kuma yarbawa suka kayatar da wunin. A gurin Khadeeja Candy ta siya duka kayan Kitchen din da aka sakawa Emily bayan, Ummi ta hadasu da ta bincika kuma ta ga akwai abubuwan da take bukata sai kawai ta zaba ta tura kudi aka hada komai ta aika da mota aka dauko mata, wasu kuma daga baya ta kara aka aiko mata ta hannun Driver. Mama Baraka ta shiga ta tsayarwa yarta tun daga gyaran jiki karbar lefe da kayan saka rana har kayan daki da gara bata bar kowa yayi mata ba. Dr A-B ma da so ya dauki wani abu bata ba shiyasa dama ba, sai kudi mai kauri ya turawa Emily ta hanyar Mama Baraka yace a aje mata idan bukatar wani abun ya tashi. A auren Aliyu Emily ta san miye gata a aure, ta san dadin yan'uwa da iyaye, ta san wasu abubuwan da suke na daga al'adar hausawa da kuma yarbawa. A wannan auren an yi mata gara an yi mata kayan daki da komai da mace take bukata daga iyaye, ga yan'uwanta a kusa da ita komai zata yi su suke shigewa gaba, su bata shawara ko ma su aiwatar ba tare da jiranta ba, yan'uwan Mama Baraka na nesa da na kusa duk an sadata da su wasu ta waya wasu kuma sun zo bikin. Bata kara gode Allah ba sai a daren da Aliyu ya aiko da manyan motoci zuwa daukarta tare da abokansa da wasu daga gwaggonninsa da iyaye. Mama Baraka da yan'uwanta suka yi mata nasiha suka mata kuduba da uwa ke yi ma kowace a, aka dauke ta tana lullube da zane bayan ta saka