← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 177

Sashe 81

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi ma kuma sai da na yi fadi tashi shiga nan fita nan, daker na samu haduwa da nada na samu ana barinsa ya zo gurin ko kuma ni na tafi, bayan Turhan ban sake haihuwa ba saboda maganin da aka bani a gidan mahaifinsa, shi ma haihuwarsa ta zo ne kawai saboda Allah ya kaddara akwai da a tsakani, shiyasa a yanzu na maida shi abokin ban kalle ta sigar dan fari ba, komai a gidansu ake masa abinci da nake ci ma daker ya iya koyar cinsa, idan ya zo nan tufafi kalar da nake so yake sakawa, zamu yi wasa da dariya mu yi hira mu yu yawo kamar ni da kane na ba dana ba, matar da ya aura ma daga masarauta aka zaba masa, kuma har yau be taba kawo min ita na ganta ba, sai a waya, shiyasa ni ma na yi masa nawa tanadin na musamman kuma na san zai so ki zaki dace sosai" Na kalleta da kamar mamaki jin ta ambace zan dace, sai na nuna kaina. "Ni" "Eh, ana nake yi ma tanadinki, na miki alkawari zai soki zai rike ki amana kuma zai so danki, a yanzu ne zaki san miye aure zaki dace, kuma na san zaki so shi domin shi ma kyakkyawa ne, kusan duk yan mata da nake hada shi da su cemin yake baya sonsu amman ke kam ba zai iya juya miki baya ba, domin kina da kyau kina da haske da gashi kamar matan garinsu, shiyasa nake ta boyonki ina fargabar kar wani yace yana sonki ki karba, kin ga idan ya aure shi zai aje ki a nan dole zai rika zuwa akai akai, kuma ni na zan samu nawa jikokin ta bangarena, idan ba haka ba ina tunani gaban kadan dauke shi zasu yi ba za su bari na zauna da shi ba" Na sauke ajiyar zuciya ina tambayar kaina to idan kuma ya zo ya ga ban masa ba fa. Kamar tasan abun da nake sakawa sai tace. "Karki damu da wai ba zai so ki ba, sai so ki ina mai tabbatar miki zai kaunace ki Aisha kamar zai yi hauka, ke kanki zaki yi mamaki yadda zai kula da ke, saboda ni na zaba masa ke da kaina kuma kin sha wahalar rayuwa Allah zai saka miki ta hanyarsa In Shaa Allahu, abun da na cutar da ni a zaman da muka yi da mahaifinsa shi ne shi baya so na, da ace yana so na da ba zan wahala a yadda na wahala ba, amman ke na san Turhan ba zai bari ko yatsa a nuna miki ba, dana yana da kirki sosai yana da tarbiyar kuma yana da addini daidai gwargwado na miki alkawarin Turhan ba zai taba cutar dake ba ba zai taba cin amanarki ba" Ta yi min campaign ta gyara danta sosai da halin da ta san ba nasa ba ne, ta fada min abun da ba haka yake ba, ta lullube danta da kyawawan halayya alhalin akasin hakan ne a tare da shi. Ni dai ban iya cewa mata komai ba, domin kyautatawa tana biyo kyautatawa ne, ta ina zan iya cewa danta bana kaunarsa macen da bata san ni ba ta rike ni ta kyautata min ni da ana, gashi ta yi kuskure bata tambayi ra'ayi akan kudirinta ba, idonta ya rufe akan muradinta da kuma burin da take da shi. Dafa ni ta yi "Aisha karki damu, na lura da kyakyawan halayen dana, kuma ba zan ce ni din mace ce mai nagarta 100 bisa dari ba amman dai na san na kam kamanta na kan kyautata iya yadda zan iya, ba zan yarda a cutar da wani ina gani ba sai inda karfina ya kare, Wallahi ba zan bari Turhan ya cutar da ke ba na miki alkawari, ke din abar tausayi ce Aisha baki da kowa kuma gani ba ki jidadin aure ba, duk wanda ya ji labarin ki dole ya tausaya miki, wata kila ta dalilinki zan samu aljannata gashi ina jinki kamar yata, ba zan taba bari Turhan ya cutar da ke ba" Ba zan iya amsa mata da aa ba amman a lokacin na ji a jikina ban shirya sake wani auren ba, idan kuma nace ba zan auri danta ba a ina zan zauna? Zai kula da ni wa zai rike ni ni da ana? Ina cikin wannan tunanin muka ji kyallowar Ibraheem ni da ita muka tashi da sauri muka shiga cikin falon na haura sama na dauko shi ihu kawai yake na yi rarrashi na na ba shi madara be saurara, sai ya yanke shawarar na tafi da shi asibiti haka na saka hijab cikin tashin hankali muka tafi asibitin, su yi iya bincikensu sun ba mu test da hotuna kala kala amman ba a gano asalin damuwarsa ba sai da ya shekara biyu cif, suka ce min ana Autism ne, ga shi yana fama da sickle, daga lokacin hallayarsa ta sake yau ciwo gobe lafiya baya yarda da kowa sai ni sai kuma Ammy mai aikin Ammy ma daker yake yarda da ita, ko sallama aka yi da karfi sai ya fasa ihu jiki yayi ta rawa ya cige, tun ina jin tsoro har na saba, ana ya sha wahala gashi kuma yanzu be rayu ba, kuma be ji sauki ba har ya bar duniya, kuma be ga ubansa ba" Ya rufe baki tana kuka. Aliyu ya mike tsaye ya nufi windows office din ya tsaya tana kallon harabar ma'aikatar, sai a yanzu na fahimci dalilin Ammy na juyawa Turhan baya, ta ki ta fahimce shi ta saurare shi. Ya sake juyowa ya kalli Emily dake ta kuka, dawowa yayi gurin teburin ya zari tissue ya mika mata ta karba tana shaye hawayenta. "Ba zan ce na fi sauran ba, amman dai na miki alkawari daga yanzu wani ba zai sake cutar da ke ba, sannan ina son na ja kunnenki akan Tasmia karki sake yarda da ita, abu na karshe da zan fada miki shi na har yanzu Ammy tana sonki, mace ce mai kirki kawai danta ne ya tsaba alkawari, saboda wannan ta juyawa Turhan baya, wannan dalilin ya saka yake nemanki, yanzu haka ya fada min bata da lafiya kuma yana tunanin kamar har da tunaninki ya saka ta ciwo" Ta kalle shi tana hawaye. "Asha ma ba nadama yayi ba, ashe ma..." Ta kasa karasa. "Dan Allah Aliyu ka yi min alkawari ba zaka taba fada masa inda nake ba" Ya kalleta sai yayi shiru na dakiku kamin ya amsa mata. "Na yi, ba zan taba bari Turhan ya san inda kike ba ta dalilina sai idan ke kika yi ra'ayi, you have my words" Ta daga masa kai alamar gamsuwa. "Mu je na kai ki gida" "Zan iya tuki na zo da mota" "No i want to take you home safely" "Amman za a iya cewa ranar mun shiga mota daya, kuma yanzu a sake ganin mun shiga" Ya rumgume hannayensa. "A duk lokacin da zan aikata wani abu uku nake dubawa kuma nake jin nauyi, Ubangijina, mahaifaina, matata, Ubangijina ya san ba ni da wata mummunar manufa akanki, sai kyakkyawa, Matata ta san da ke, iyayena ne suka rage su kuma na san ba su da matsala, the rest can go to hell, let's go" Ya fara takawa ya isa kofar ya bude ya juyo ya kalleta sai ya samu shi take kallo. "Aliyu yana da banbanci da sauran ki saka wannan a zuciyarki, you can trust me" Ta mike tsaye ta isa kofar ta fito sai ya janyo kofar a daidai lokacin da Amal ta fito office dinta, dan tsaye ta yi da farko irin na mutum da mamakin ganin sabon abu ya rufe shi, Aliyu yayi kamar be ganta ya jera da Emily suka wuce, a tare suka sauka kasa suka isa har gurin motarsa ta bude ta shiga, shi ma ya shiga. "Amman lokacin tashi aikin be yi ba" Yana yi ma motar key ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. "You need to rest, labarin zaki karasa min wani lokacin, don't stress yourself" Ya tashi motar suka kama hanya, sai ta maida dubanta gurin agogon da ya bata tana ta murza agogo a hankali. Kallo mace ya wuce sau biyu zuwa uku haramun ne a gurinsa amman Emily ya kasa dauke idonsa a kanta, musamman a yau da tausayinta ya zame masa nauyi, tukin kawai yake amman idonsa da hankali yana gurinta har ya isa gidanta, ya faka a wajen gate din gidan yana kallonta. "Aliyu..." Ta kirashi da muryarta kasa kasa. Ya amsa mata yana kallonta zuciyarsa cike da tausayinta. "Ka taba marmarin abun da baka taba samu ba?" Ta tambaya har lokacin bata kalleshi ba. "A'a" Ya amsa mata bayan few seconds. "Me kike marmari?" Ta kalleshi tana kuka. "Iyayena, ni uwa amman ni ma ina neman tawa uwar ina jin kewarta duk da ban taba kasancewa da ita ba, me yasa suka jefar da ni, me na yi musu? Miyasa gashin kaina yake yake da idanuwa na, ni yar asalin wace kabila ce, wa na biyo mahaifina na ko mahaifiya? Minene asalin sunana? Su waye yan'uwana? Duk ba ni da amsar ko daya" Ya busar da iskar bakinsa. "Emily kuka kike son na miki ne?" Ta girgiza kai. "Toh dan Allah ki yi daina kukan nan haka, kin cika zuciyata fal da tausayinki, a yanzu kuma bana son ganin damuwarki, ban wanzu a wacan duniyar da kika sha wahalar rayuwa ba, amman ina ta dorawa kaina laifi miyasa ban san ki tun a farko ba? Wata kila duk wannan wahalar da baki shata ba, iyayenki kuma wata kila ma sace ki aka yi aka kai a gurin ba tare da sanin iyayenki ba, domin alama suna nuna ke ruwa biyu ce, amman ki daina kukan kin ji?" Yana mata maganar cikin sanyin murya da rarrashi. Ta share hawaye. "Good Girl" Ya bude motar ya fita ya zagaya bangarenta ya bude mata ta fito. "Na san Fatima bata nan yanzu, amman anjima idan ta dawo school ta huta ni ma na tashi aiki zan zo na dauke ta mu je yawo" Ta bata fuska kamar zata fashe
Chapter 81 · 0% Book details