Sashe 161
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 7 KAMEELA POV. Sosai ta natsu tana sauraren labarin da Hajiya take bata kamar yadda Alhajin ya fada mata yadda abubuwan suka faru. "Wai kawai sai ta bude baki tace Aliyu... Na ce daman dai hadin baki aka yi da uwarko?" Kameela ta kai tsaye. "Hajiya dan Allah karku bari a yi auren nan, Wallahi ina son mijina, kuma na san yana so na, kawai makircin yarinyar nan da uwarta" "Zancen banza, aure ai tuni aka daura, babanku yace mai gidansa da dansa ba su bar garin nan ba sai da aka daura auren, wai da la'asar sai kace auren kauye" Anty Shafa ta karba mata. "Auren kauye ai yafi na wannan arniyar daraja, kuma shegiya ce shiyasa suka daura auren kar ya subuce, dadin dadawa kuma Mama Baraka ai zata iya yin komai saboda ace yarta ta auri Aliyu kin ga ai ta yi gasa da ke" Kameela ta dora hannu a kai. "Na shiga uku, Innalillahi... Hajiya ina son mijina ina son Aliyu" Hajiya ta daka mata tsawa. "Ke dalla gafara can mahaukaciya, Aliyu autan maza ne halam? Tun da kika aure shi wani farinciki kika samu? Kuma ke da kike ikirarin ba zaki zauna da mai mata ba? To yanzu ai yayi aure, kuma shi be damu dake ba sai ke? Ko kuma mu mahaukata ne da za mu bar ki yi kishi da marar uba? Yarinyar da bata kai rabin matsayinki ba? Daman can ba son auren nan muke ba, shi kuma be shirya rike amana ba, aure be jimawa daga dawowa haihuwa an fara samun matsala" Ta fashe da kuka tana jin duniyar ta juye mata mijin da take so ya juya mata baya, dakunsa da take kuma ya kare a yau saboda yayi auri abun da bata taba zato ba, gashi iyayenta sun kasa fahimtarta. "Ki duba ba fa Hajiya, ko irin ya dawo yana bada hakuri din nan be yi ba, gaba daya ya nuna shi daman ba sonta yake ba, kawai iyayensa da shi sun shirya wulakanta zuri'armu ne, idan har yana sonki kuma yayi nadama ai kamata yayi ya kawo kansa yana kuka yana faduwa kasa yana tuba, amman ba ko da ya, sai ma tafiya ya auri marar asali ko dai ya manta waye shi ne? Kuma iyayenwai suka bar shi? Tab" Anty Shafa ta fada tana tabe baki da jinjina lamarin. Kameela ta tashi ta bar su a falon, dakinta ta shige ta kwanta kasa tana kuka kamar an yi mata mutuwa, bata taba jin zafin azabar kishi da bakincikinsa ba irin yau. Aliyunta ne dai yayi aure? Ta rarraba ta isa bakin gadonta ta kai hannu zata dauki wayarta kuka ya ci karfinta. " Aliyu ka yi aure? Ina alkawarin da ka yi min Aliyu? Ina soyayyar da na nuna maka?" Ta kai hannu daker ta dauki wayar ta da sabon layin da take aika masa sako ta gwada kiransa tana kuka, ringing daya ya daga, ba dan be san mai kiran ba sai dan ya shiryawa kiran. "Sallamu Alaikum" "Aliyu ina alkawarin da ka yi min? Cewar ba zaka min kishiya ba?" "Na cika miki, tun da ban miki kishiya da igiyar aurena ba" "Ina ladar soyayyar da na nuna maka?" "Na miki sakamako iya yadda zan iya, fadi tashi a tare muka yi har iyaye suka amince muka yi aure, yanayin rayuwar aurenki da zafin kishinki, rashin nazari kamin yanke hukunci sune abubuwan da suka hana zaman aurenmu, kuma ba zan miki Karya ba, kowane namiji yana son kwanciyar hankali da farinciki a gidansa, iyakar hakkinki na baki, har wanda ba naki ba na baki, kin wuce gona da iri Kameela, idan ma na ce zan cigaba da zama dake ba ni da kwanciyar hankali, kuma mahaifiyarta ba zata yarda ba, gashi kuma iyayenki ba so na suke ba" "Munafiki azzalumi maci amana, can da baka ganin komai sai a yanzu da ka auri karuwa? Yar titi marar uba? Yar zina? Matar da aka haifa na da aure ba? Ai baka yi aure ba Aliyu tun da baka auro yar gidan mutumcin ba" "Zaki iya zagina ki ci mutumci, amman ban da matata, dan an haife ta ba da aure ba, miye laifinta? Ko kina tunanin dan'adam yana iya tsallake kaddara ce ne? Ko daga sama ta fado ina sonta a haka, dan haka karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, kamar yadda ban yarda a taba mutumci lokacin da nake aurenki ba, ba zan yarda a taba mutumcinta ba" Ya yanke wayar, Kameela ta ji kamar ta haukace tsabar bakinciki na jin kalaman Aliyu. A daren da bakinciki ta kwana tunani be barta ta runtse ido da sunan bachi ba, ganin abun take kamar mafarki, wai Aliyu yayi aure, a tunanin zai gama kewaye kewayensa ne ya dawo mata. Idan ta tuna yadda take rayuwa da mu'alama da mijinta, ta hango yanzu Emily ce a makwafinta, sai ta ji kamar zata haukace, wani karin bakin cikin ma Emily daga tsatson Mama Baraka take ba, da ace daga wani gurin ne dabam wata kila zata fin saukin kishi. Yanzu kenan Emily ta yi nasa? Bayan ta shiga tsakaninta da mijinta tun a PH gashi kuma ta aureshi, babbar matsalar ta ma babu mai rataya kishin ita kadai take yakin, tun da yan'uwanta sun gagara fahimtarta. Haushinta da Hajiya ta ji ya saka bata damu ta cilasta mata fitowa ta ci abincin ba, a ganinta akwai mazan da suka fi Aliyu komai nesa ba kusa ba, amman tana wahalar da kanta ta wanda tun tashin farko ba su so auren da shi ba, a yanzu ma taki ta bawa wasu kofa ne amman ana nuna mata kauna, gata kyakkyawar bazawara sakin Wawa, babu a balle abu ya dame ta. Sai da ta bari kowa ya gama karyawa sannan ta sauko ta nufi dinning kanta na tsarawa kamar zai fashe, ta zuba madara da suga a cup ta zuba ruwan zafi sai kuma ta ji ba zata iya sha ba. Ta zauna a kujerar tana kallon Anty Shafa dake kwashe kayan wasan yaranta. EMILY POV. Kusan wannan ne karon farko da aka daura aurenta ta kwana da cikakke farinciki. Wacan auren nata na farko anyi shi ne a lokacin da iyayen mijinta basa so, kuma bata da wanda ya tsaya mata, tsabanin yanzu da komai kishiyarsa ne, na biyun kuma an daura da wanda bata so be san darajarta ba... But Aliyu ya zama wani na dabam a gareta, ya nuna mata farinciki da jindadin data kasance matarsa, gashi mahaifiyarsa tana sonta, ga shi yan'uwanta sun shaida. A yau ta kara sanin darajar yan'uwa da dadinsu. Ta farka cike da farinciki, da kuzari tana gama Sallah asuba sakon Aliyu ya shigo wayarta. "Barka da safiya matata mine and mine only, farar mace mai farar zuciya" "Barka da safiya Aliyu?" "Wato Aliyu ko? Idan na zo sai na horar da bakin nan sai na masa hukunci" Ta yi dariya. "I'm sorry" Ta rubuta masa. "I love you" Ta maida masa amsa da heart Emoji guda biyu. Sannan ta dauko karatun da suke fara karantawa, sai ga kiransa ya shigo ta amsa tare da amsa sallamarsa. "Amince ya tabbata ga kyakkyawar yan mata ne mai zazzakar murya, da tattausar zuciya" Ta yi murmushi mai sauki. "Tare da jarumin da ya tare komai ya wanzar da farinciki a zuciyata" "Zai wanzar dai, yanzu ne zai fara aikin, ina nan kwance ina ta tunaninki, kuma na san idan na dako sammako Ummi zata gan ni, dan haka na jira na ji muryarki" "Na gode da ka kira ni" "Aa ranki ya dade na gode da kika amsa, za mu iya karatu ta waya? Ko sai na zo?" "Zaka iya?" "Ta ina zuciyarki ta samu kwarin guiwar tambayar abun da ba zan iya ba saboda ke?" "Ina sonka Aliyu" Ta fada da kwalla a idonta. "Ni kam kaunarki nake Amaryata wacce ta fi ta kowa, bude littafinki ki fada min abun da kika iya" "Ni ba na gane komai idan baka kusa da ni" "Ki sassauta kalamanki, inda ba son kike zuciyata ta fashe da kaunarki ba, da kuma kewarki da na yi a yau fiye da kullum" Ta yi dariya. Sannan ta fara karatun bakin inda ta iya ya dora matada wani. Bayan sun yi sallama ya aiko mata da sakon. "I love you" Ta aika masa da sakon heart. "No ki ko yi fada min I love you, yana kara damkon kauna kuma ni mijinki ne" "Okay" as reply "Okay??" I love you ta tura amsa. "I love you more" Ya maido mata da amsa. Ta kwanta a gurin tana ta kalmomin cike da kaunarsa. Misalin karfe takwas na safe ta fito dakinta ta sauko kasa cike da kunya ta shiga Kitchen domin ta ya Ummi aiki kamar yadda ta saba. "Yanzu nake kokarin cewa a kiraki, ki shigo ko kara koyar abubuwan da mijinki yake so" "Ummi ina kwana" "Lafiya alau, an tashi lafiya?" "Alhamdulillah" Ta amsa tana jin tsananin kunya abun da bata saba ba. Suna tsaka da girkin ne, daya daga cikin ma'aikatan gidan ya kwankwaso kofar ya sanar da Kulu dake mopping din falon cewar ana sallama da Emily. Kulu ta shiga kitchen ta sanar da Ummi. "Wake sallama da ita?" "Ban tambaya ba Hajiya" "To ki tambaya mu ji, yana ina?" Kulu ta juya, bata jima ba ta dawo. "Wai Hajiya Baraka ce" "Ah ah tana ina?" "Can wajen gate" Daga Ummi har Emily fuskar mamaki suka yi. "Bata shigo ba?" Emily ta tambaya. "Eh haka yace tana can waje" Ummi ta dan yi shiru sannan ta amsa. "Toh gata nan zuwa" Sai da Kulu ta fice sannan Ummi ta kalli Emily ta ce. "Wata kila tana son ta yi wata magana da ke bata son mu ji ko mu gani, ki tafi ki same ta" "Okay" Ta amsa sannan ta bude kofar baya ta kitchen din ta fice daman jikinta a lullube yake da Hijab. Ta nufi gate din ta bude a hankali ta fita, ta yi zaton ganin Mama Baraka ne, sai ta yi arba da Turhan tsaye kusa da motarsa. Da ta duba ko'ina bata ga alamar Mama Baraka ba sai ta juya zata koma. "Ba zan samu