← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 177

Sashe 92

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daga baki baki na zube kasa, sai ta yi tafiyarta. Na kusan awa daya a gurin sannan Turhan ya fito cikin shigarsa ta jallabiya da alkibba mai kyau hannayensa a baya ya karasa kusa da ni cikin wata irin tafiya ta kasaita ta ban taba ganin yayi irinta a gidan Ammy ba, fuskarsa babu annuri. "An fada min kin yi magana? Saboda me?" Maganar ma a rarrabe yayi min ita saboda kasaita ta. "Dukan ne yayi min yawa ban san lokacin da na yi ihu ba, ka yi hakuri" Sai a lokacin ya kalleni yana jin kansa. "Wa yasa aka doke ki? Me kika yi?" A tunani da sanin matarsa aka min dukan dan haka da ya tambaye ni sai na ce. "Matarka" Na kama hafafuwansa na rike ina kuka. "Turhan dan Allah ka maida ni gida" Ya ja baya. "Karki sake taba kafata, tashi ki fice, kuma na fada miki ke kurma ce karki sake ki sake yin magana" Na tashi daker na koma bangarenmu, na samu tufafin wata na dora kaina akai domin ni Turhan be bani nawa tufafin da Ammy ta hado ni da su ba, kuma bata kira ta ce a bani ba, kowa yana ta tufafi daga kala biyar zuwa sama ni kuwa kala biyu ne daga tufafin da yake a matsayin uniform dinmu sai tufafin da na cire. Ina dakin aka sake zuwa aka dauke ni hadimar Gimbiyar tana ta masifa sai dai ban san me take fada ba. Wacan dakin aka sake maida ni aka sake zaneni sai dai wannan karon ban yarda na yi uhu ba saboda Turhan ya gargade ni. Dukan ne ya zama silar rashin lafiyata a masarautar har na tsawon sati gashi babu kyakkyawar kulawa babu maganin kirki, rayuwar bauta rayuwa ce ta kaskanci da wulakanci Aliyu, wanda ba zan yi ma kowa fatanta. Da na fara jin sauki sai na koma kan aikina tun daga lokacin bana bari ma asuba ta yi ina bachi, da zarar karfe uku ta yi na dare na farka ba zan sake komawa bachi ba. Zamani ya waye duniya ta canja ban taba tunanin har a lokacin akwai sarakunan da suke mulkin bayin ba sai da na ga masarautarsu Turhan. Gashi basa ganin kimar bakar fata, domin a duka bayin babu larabawa sai yan wasu yarukan ko kabila, ni kaina sai su yi ta kallona wasu har taba gashin kaina suke suna yaren da bana ji, wani lokacin kuma a daga fatar idona a kalli idon. A ranar da Allah ya kaddara za a samu cikin Fatima, da safe ne sosai ina goge fadar Hadimar Gimbiyar ta zo ta kama hannuna ta shiga da ni can ciki sannan ta saki hannuna ta fice, ina tsaye a gurin Turhan ya fito sai na yi hanzarin zubewa kasa na maida idanuwa kasa. "Biyo ni" Ya fada sai na mike tsaye na bi bayansa, da halshen larabci ya sallami masu saka turaren dakin sai daya daya umarci ta ba ni turaren na karba na bi bayansa har muka shiga bangarensa. Muna shiga ya nuna min inda zan aje turaren ya ce. "Shiga wacan dakin akwai bandaki a ciki ki yi wanka, ki cire tufafin ki daura tawul" Yana min maganar yana kallo da kyama da kuma dan bacin rai kamar wanda baya cikin yanayi mai dadi. Na aje turaren na nufi dakin da ya nuna min na shiga, na cire tufafin jikina kenan ban kai ga shiga bandakin na ji shigowarsa. "Dole ce kawai saboda kin min karya kince matata ce ta saka aka duke ki alhalin ba ita ta saka ba, kin saka ta kaurace min na tsawon lokacin nan" Wata kila yana cikin uzurin da ba zai iya jira na yi wankan ba, ko kuma yana tsoron ta shigo ta tarar da mu ne sai ya yi abun da zai yi cikin gaggawa, bayan ya gama yana ta tsaki da tofar da yawu. "Wannan ce bakar rana ta biyu a gurina bayan ranar da na aureki, kuma karki sake na ji maganar nan kin shigo dakina a gurin kowa ko kuma wata alama" "Dan Allah Turhan ka maida ni gida" Na roka ina jin kaina a cikin wani irin kaskanci da ban taba samun kaina a ciki ba. "Idan kika sake fadin sunana ko daga ido ki kalleni sai na saka an miki illar da zai lalata miki idon, ko baki in yaso sai ki zama kurma da gaske, tashi ki bace min da gani" Ya daka min tsawa rai a bace, a cikin rakunan bakincikina, ranar da Khaleefa ya sake ni ba zan manta da ita ba, ba zan manta da furucin da Turhan yayi a gareni ba na kiran ranar aure da kuma ranar da ya tara da ni a matsayin bakar rana ba, haka ba zan manta da ranar da na rasa ana ba. Na kimtsa kaina na fito ina jin jikina yana min wani iri domin na dade irin wannan alakar bata hada ni da kowa ba bayan na fito daga gidan Khaleepa. Na cigaba da aikina ina hawaye har na gama, sai rayuwa ta ci gaba tun ina saka ran Ammy zata zo ko kuma ta kira amman babu ko daya, gashi ni kuma ban taba rike waya ba tun bayan dana zauna a gidanta ban san ma ta ina zan same ta ba. A haka na sake shafe wata biyu a gidan, kuncin da na shiga sai yafi na baya saboda matarsa da hadimarsa sun tsane ni a yanzu ba tare da na san laifin da na yi aikata a agaresu ba. Ga kuma lailayin da nake ta yi a boye. Muna cikin wannan halin wata rana sai fadar sarkin ta yi babban bako. Wani babban mai kudi kuma dan kasuwa ya sauka masarautar tare da rakiyar manyan mutane daga Nigeria. Aka saka mu yi wanka muka fito tsaba saboda zamu tarbi bakon tare da tawagarsa. Sai kuma aka yi dace Turhan da matarsa sun tsallaka sun bar kasar zuwa gurin da be fada min ba, na fahimcin hakan ne ta hanyar rufe wani bangare da aka yi a part dinsu aka hanani shiga na gyara kamar yadda nake, kuma aikin da ake yawan sakani ya ragu ba ma ni kadai ba har da sauran bayin. Wasu kuma na daina ganinsu wata kila har da su aka yi tafiyar. Matar Sarkin wanda take zaman step mother din Turhan ta tarbi matar dan kasuwar da ba zan iya fadar dalilinsa na zuwa garin a lokacin ba. Ni da mutum uku aka zaba mu yi Serving din matar dake wanye da abaya kanta da wings ta nada gyalen abayar a wuyanta ga bakin gilashi, da alama dai ba musulma bace shiyasa ta kasa rufe kanta. Kusan shi ne karo na farko da na bar garen Turhan zuwa wani bangare na gidan, wata kila babu wata adatattun bayi ne a lokacin wata kila kuma Allah yayi nufin kubutar da ni ne, shiyasa abun da duk ya faru ya faru. Muna jera abincin a madaidaicin falon da aka ware mata ina satar kallonta zuciya nata yi min sake sake, yadda zan samawa kaina mafita, domin tun da muka shigo naji tana waya da yaren igbo. Sai da muka gama jera abincin tsab sannan na kalli matar cikin karfin hali da nemawa kai masifa na soma mata magana da yaren na Igbo. "Dan Allah ina neman taimakonki, na ga ke ma igbo ce yar'uwata dan Allah ki taimaka min" Sauran bayin da muke tare da su suka kalleni kamar a firgice sai dayar ta fice da sauri. Matar ta kalleni tana mamaki ta ba ni amsa da yaren na Igbo. "Kina jin igbo ne? Daga ina kike?" "Daga Nigeria, ki taimaka ki maida ni gida dan Allah, ni yar kabilar igbo ce, daga Lagos na zo aiki gurin wata mata a kaduna sai ta hada baki da wani suka siyar da ni a matsayin baiwa a gurin dan sarkin garin nan, ina zaune a nan ne a matsayin kurma wahala nake sha sosai a nan, gashi na baro ana kuma ba shi da lafiya, yanzu kuma idan baki taimaka min ba kashe ni za su yi saboda sun ji na yi magana ba su taba jin na yi magana ba" Ina maganar da yaren na Igbo ina kuka. "Amman baki yi kama da mutanen Nigeria ba" "Wallahi daga Nijeriya nake, a gidan marayu na tashi ban san kowa na wa ba, idan mum tafi zan kai ki har gurin domin ki tabbatar dan Allah ki ceto rayuwata" Na yi mata karyar an siyar da ni ne domin ba lallai ta yarda ba idan na fada mata dan sarkin garin ne ya auro ni ya mayar da ni haka. Daya daga cikin manyan hidiman bang aren Turhan ne ta shigo ta kama hannuna zata fice sai na cigaba da rokon matar. "Na yi kasada na jefa kaina a matsala na yi magana idan baki taimake ni ba, shi kenan na rasa rayuwata kuma ana ya rasa ni, ke fa uwa ce ki taimake ni dan Allah" Bata ce min komai ba, a lokacin ne na gane na yi kuskure na jefa kaina a babbar matsala domin ban samu biyan bukata ba. Waje aka fitar da ni can bangaren Turhan aka bar ni tsaye a rana a lokacin har na sadakar na san hadimar zata min hukuncinta ne kuma idan Turhan ya dawo shi ma yayi min na shi. Tsawon awa uku na yi tsaye a ranar kamin hadimar da kanta ta sake zuwa ta kama hannuna muka koma bangaren na Sarkin da sai a lokacin na taba ganinsa ido da ido a cikin fadarsa. Matar ta nuna ni tana murmushi tana fadar nice da yaren turanci, mai fassarawa sarkin yayi Larabci sai sarki ya daga kai da hannunsa kadan wani na kusa da shi yayi magana sai aka fassara ma matar a nan ni ma na ji yana fadar. "Sarki yace ya baki ita kyauta" Matar ta yi godiya sosai sai aka fitar da ni waje, a nan sai da suka dade cikin sannan suka fito fadawan sarkin suka yi ma mutumen rakiya tare da matarsa ni kuma na shiga a tawagar masu rakiyar dan kasuwar a wata mota ta dabam. Hankali be kwanta
Chapter 92 · 0% Book details