← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 177

Sashe 26

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 Assalamu Alaikum. Barka mu da Sallah. Allah ya karbi ibada ya maimaita mana. *** ***. ***. Ta tura kofar dakin ta shiga fuskarta dauke da murmushi. "Hello my beautiful boy" Ya kalleta kawai ya dauke kai ba murmushi babu far'a kuma babu fushi, ta karasa kusa da shi cike da karfin guiwa ta zauna a kan gadon, hannu ta kai zata shafa shi a take ya saka mata ihu. Da sauri ta janye hannun, ta mike tsaye ta matsa gefe. Ka yi hakuri London I'm sorry Ta hade yawu tana kallonsa rashin jindadin dake zuciyarta ya bayyana a fuskarta. Hannu ta saka a aljihu jean din dake jikinta ta ciro wayarsta ta yi dialing din number Vito. Ta juyawa London baya hannunta daya a kan lebenta tana cizon akaifarta idonta tab da hawaye. Na dauka ka yi magana da London kace min ya hakura fa Yeah na masa magana kuma ya hakura Amman na zo yanzu yana min ihu, baya son na taba shi Vito yayi shiru for few seconds yana karantar yanayinta "Kuka kike yi?" "To me zan yi" Ta fada a tsawa tana shessheka kuka kai kace shi yayi mata laifin. Daker ta iya hade yawu sannan ta kashe wayar ta juyo tana fuskantar London, rasa makamar yadda zata ba shi hakuri ya sakata ta zauna a gurin tana cigaba da kallonsa har lokacin hawaye sauko mata suke, tunanin rayuwar da ta yi kamin ta haifi London da kuma wanda ta yi bayan haihuwarsa, da yadda rayuwarsa ta zo mata, halin da ta shiga fargabar matsalar saninta da Aliyu yayi a yanzu duk suka taru suka mata tsaye a cikin kai. Sai da ta yi da gaske sannan ta iya runtse ido tana maida numfashi a hankali, sai kuma ta kai hannu ta shafa sarkar cross din dake wuyanta. Wayarta ta fara ringing alamar kira, tana kallon kiran har sai da ya kusa yankewa sannan ta amsa ta kara a kunne ba tare da ta yi magana ba. "I have to take care of something, ba zan iya zuwa ba, amman na yi magana da wani abokina yace akwai wani abokinsa kwararen likitan kwakwalwa, kuma ya shigo garin nan yin wani abu, zai shigo ya duba London kamin ya wuce" Dana ba mahaukaci ba ne Vito, ciwo ne kawai yake damunsa Ta rufe da fada zuciyarta na bugawa da karfi tsabar bacin rai, ya san yadda zai tafi da ita dan haka yayi shiru be ce komai ba sai na tsawon lokaci. "Zan aje wayar" Ta fada jin be ce komai ba har na tsawon minti biyar. "Na sani, kawai zai duba shi ne ya bashi ya bamu shawarwari wata kila za su taimaka mana" Tare da ta sake cewa komai ba ta kashe wayar, daga inda take zaune take kallon danta har bachi ya fara daukarta tana angaje har ta kai ta kwanta a gurin, bachi mai nauyi yayi gaba da ita, bata farka ba sai kusan asuba, ta bude idon tana hamma ba tare da ta rufe baki ba, dagowa ta yi kadan ta leki London, ganin yana bachi ya bata karfin guiwar mikewa tsaye ta karasa kusa da gadon da yake kwance ta zauna, ta mika hannunta a hankali ta shafa fuskarsa zuwa kansa, tausayi yake bata sosai saboda lalurar da yake dauke da ita, ba zabin mutun bane ya kasance a yadda yake so, ko kuma waninsa ya kasance a wani hali na dabam marar dadi, abu ne sa yake tsare tun gabanin halittar rayuwa, an rubuta yadda dan'adam da rayuwarsa zata kasance. Knocking aka yi sau biyu da two fingers, da sauri ta dago ta kalli kofar dakin hakan yayi daidai ta turo kofar dakin da aka yi aka shigo. Cak ta tsaya tana kallon mutumen da ya kasance bakuwar fuska a gurinta, kamar yadda shi ma yake tsaye yana kallonta. Lafiya? Ta tambaya ganin ya gagara karaso, haka kuma ya gagara cewa komai. Takawa yayi baya ya ja mata kofar ya rufe, bata gama mamakin waye shi da kuma dalilinsa na aikata hakan ba, ya sake turo kofar dakin ya shigo with full confidence... Kallonsa take har ya karaso kusa da ita idonsa cikin na ta. "Sunana Doctor Adam Bello amman an fi sanina da Dr A-B kwararen likitan kwakwalwa, ina aiki a asibitin Special Care Hospital dake Abuja, abokina ya fada min akwai wani yaro da zan duba a dakin nan, wanda nake kyautata zaton kanenki ne..." Ya karasa yana kallon London dake bachi, zuciyarsa na raya masa kanenta, a yanayin halittar jikinta da kuma kurciyar dake fuskarta ba su bar masa alamar da zai aje London a matsayin danta ba. "London ba mahaukaci ba ne" Ya daga girarsa biyu kadan ba tare da ya kalleta ba. Ni ma ban ce ni likitan mahaukata ba ne, mutane ne suke kuskuren fahimtar ciwon sai suke ganin kamar hauka ce Ya kai hannu ya kama hannun London yana taba tsatsunsa a hankali. Fada min idan kanenki ya farka yana farkawa a firgice? Idan babu kowa a kusa da shi? Ta daga masa kai alamar eh. Wane kalar turare ya fi so?" Har lokacin be kalleta ba. "Ban taba lura da wannan ba" "Uhm, da wa yake yarda? Bayan mahaifiyarsa da Babansa da kuma ke? Dana ne ni na haife shi Sai a lokacin ya sake kallonta, ya dauke shi tsawon dakika biyar kamin ya iya dauke idonsa daga kyakyawar fuskarta mai matukar daukar hankali. "Ya kamata ki san kalar turaren da yake so, his favorite color, wane kalar cartoon yake so, wane kalar wasa yake so, wane yanayi yake shiga idan yana kuka, su waye mutanen da yake so, ki fahimci idan yayi bachi wane kalar mafarki yake? Ya yanayin sakewarsa da mutane yake?" "Na san wasu daga ciki, amman dai shi ba mahaukaci ba ne Yayi murmushi ya kalleta. Da alama zaki sha wahalar rayuwa kamin ki fahimci duniya da mutanen cikinta, ni dai ina baki shawara ne kawai na yadda abubuwa za su miki da sauki tsakanin ke da... Danki... Ya fada tare da jan zaren furta kalmar danta kamar mai jin nauyin alakantata da jininta. Sannan ya ciro katinsa a aljihunsa ya mika mata. "Bana kallon marar lafiya a free ma, balle kuma magana da shi, sai an yi min biya mai kyau, amman da yake ke tafe kike da sa'a, sai ga shi an lallaba ni na zo har asibitin da kike na duba danki kuma na baki shawarwari a free, so hare is my card idan kina son wanin hakikanin waye danki, taya zaki zauna da shi, wane mataki zaki bi har ki yi nasarar sauya rayuwarsa, da kuma yadda zai samu lafiya, sai ki bi matakin da yake kan card din Ya aje mata card din ya juya ya fara tafiya. Bama bukata daman ka zo nan ne dan ka ci kudinmu ko? Toh ni na san waye ana kuma shi ba mahaukaci ba ne Juyowa yayi yana murmushi. Halinku daya sak da matar direban direban Babanmu, amman kuma da ta bi shawarwarin da na dora ta a kai da magani, sai ga shi ta dawo tana min godiya A kokarinsa na fahimtar da ita kudi ba matsalarsa ba ce kamar yadda take zato ya ambato mata direban direban babansu. Da farko she was confused kamar ya Direban direban babansu kamin ta sake kallonsa cike da mamaki. Direban Babanku?" "Nope Direban Direban Babanmu" Ya furta yana hade lips dinsa. "Direban Babanku yana da Direba kenan.?" 'Wane irin kudi babanku yake da shi haka ne? Da har direbansa yake da direba?' Kamar ya san tambayar da ta yi ma kanta a zuciyarta sai ya taka ya matsa kusa da ita, yana kallon kwayar idonta. Babanmu na da kudin sosai, kwatankwacin yadda kike da kyau sosai mai jan hankali Ya fada cikin wata murya na irin mutumen da kuzari ya bar jikinsa, gaba daya kyauta ya gama rudashi. Ta hade yawu da karfi tana kallonsa. Akwai wata tambayar ne? Ta kasa cewa komai, ya kalli agogon hannunsa. Lokacin sallah yayi, duk lokacin da kika shirya bata kudinki, zaki iya nema till then good bye Ta matsa baya ya fara tafiya. "To miye amfanin zuwanka? Baka duba yaron ba baka fada min komai ba taya zan tabbatar da kwarewarka ko akasin haka? Tana maganar tana daga kafadunta. Ko ba komai ai na auna nauyin kyaunki na fada miki matakinsa, yanzu kin san darajarsa Ya fada sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ta bi bayansa da kallo har ya fice, sannan ta sauke numfashi ta kalli card din da ya bar mata, ta kalli danta, sai kuma ta dago wayarta ta shiga camera tana kallon fuskarta. Ita kan bata ga wani banbanci a tsakanin kyauta na jiya, shekaran jiya da kuma yau ba. Mai da wayar ta yi ta aje, tana nan tsare da danta har ya farka misalin bakwai da yan mintuna. Good Morning Sunshine" Suna hada ido sai ya koma ya kwanta ta rufe ya bata fuska sosai kamar zai yi kuka. Chichi chichi "Okay zata zo yanzu" Ta fada ba dan ranta ya so ba sai dan Chidinma ta fi soyuwa a zuciyar danta fiye da ita a yanzu. Ta dauki wayarta ta nufi kofar dakinta ta bude fice tana jin kamar ta fasa kuka. Ta fito asibitin sai ta tsaya a harabar tana kallon mutanen dake hada hada kamar wacce ta rasa abun yi, gaba daya ta rasa me ke mata dadi. Daga inda take tsaye ta dagawa wata matar dake tunkaro inda take hannu matar ma ya dago mata tana murmushi. Emily ta fara takawa ta karasa gurin matar dake tahowa. "Sannu kin gane ni? Matar ta dan yi jimmm kamin ta amsa. Eh kamar ke ce na kusan kade yarinyar ki ko? Haka ne, kina aiki a nan ne? No na shigo kawo ma wata abincin ne, ke fa? Yarona ne ba shi da lafiya "Da sauki amman? Allah ya ba shi lafiya Tana fadar hakan ta wuce abun ta ta bar Emily tsaye a gurin da mamaki kuma da takaicin yi mata magana da yi. Okay Ta fada sannan ta juya tana kallonta kamin ta tsuke baki ta cigaba ta tafiyarta, tana fita wajen
Chapter 26 · 0% Book details