← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 177

Sashe 83

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 3 "Hey Fatima ya kike?" Ya fada yana kallonta sai ta amsa cike da far'a da zumudi. "Fine" Aliyu ya kalli Emily. "Ni fa ba ke na zo dauka ba, Fatima kawai nace zan dauka" "Ni ma ka ji nace ka tafi da ni ne?" "Ina karantar abun da yake cikin zuciyarki a fuskarki da idonki shiyasa kika yi anko da ni, ni bakin voile ke bakin abaya" "Saboda an rubuta a fuskata ina son ka tafi da ni?" "Bana bukatar a rubuta, saboda ina iya karanta rubutun da alkalin zuciyarki ya ayyana ko babu tawada" Ta bude baki zata yi magana ya tare numfashinta. "Ki cigaba da musawa daman ai kin saba" Sai ta yi murmushi ta sauke kanta kasa, shi ma murmushin yayi ya mika hannu ya bude gaban motar, Fatima bata jira yace ta shiga ba ta shige front seat. Emily ta duba wayarta ganin kiran Vito na shigowa wayarta ya daga mata hankali sai ta yi hanzarin kallon Aliyu. "Ku yi hanzari ku tafi" "Ke fa?" Ta girgiza kai ta rufe motar. "Ba zan je ba" Aliyu ya kalli wayar dake hannunta da yadda hankalinta ya tashi a take sai ya kashe motar. "Dan Allah ka tafi kuma karka dawo da ita sai idan na kiraka" "Idan baki ra'ayin tafiya yawon da ni ba zan cilasta miki ba, amman ke ki fara tafiya gidan tukuna" "Aa sai ka wuce hankali zai fi kwanciya idan ka tafi" "I'm your boss ni zan baki umarni ba ke zaki ba ni ba" Ta kalli titin ta sake kallonsa cikin tashin hankalin da take boyewa. "Amman kace baka son bacin raina, dan Allah ka tafi" Tana fadar hakan ya murzawa motar key cikin wani yanayi na am masa dole ya hau titi, bata bar gurin ba sai da ta daina hango su, sannan ta koma cikin gidan da sauri, ta shiga falon cikin tsoro sannan ta haura sama zuwa dakinta wayarta ta fara kashewa ta boyewa tana dagowa sai ga Vito ya shigo fuska kamar bakin maciji, wani irin cin burki yayi ya tsaya kallonta daga sama zuwa kasa, ganinta da Abaya ya ninka masa bacin rai. "Miye wannan a jikinki?" Ta yi shiru bata amsa masa ba. Sai yayi cikinta mayafin abayar ya fara fisgewa ya jefar ya rike wuyanta da karfi. "Ina Fatima take? Ina kika je? Meyasa kika saka wannan kayan?" Ta ture shi da karfi ta fara magana cikin tsawa. "Saboda ina ra'ayin sakawa, na gaji da abun da kake min Vito komai na rayuwar duniya sai ka zaba min zan yi? Tufafi sai wanda kake so? Bana mu'alama da kowa sai wanda ka yarda da shi? Yar aiki mai gadi duk sai wanda ka zaba?" "No ba zaba miki tufafi ba, ki saka duk wanda kika so, amman ban da wannan! Ke yanzu ba abun kunya ba ne a gurinki ki yi koyi da musulmai? Ina hankalinki ya tafi? Me kike son zama Emily? Zan amince miki ki yi komai zan baki gata amman ban da canja addini Emily ba zan taba yarda da wannan ba" "Bana son zama da kai, ina son na bar gidan nan na yi rayuwata ni kadai" "Baki da wannan ikon, wane yake hure miki kunne ko? Ina kika tafi? Ina Fatima?" "Ba ruwanka da wannan" Ta sake riko wuyanta. "Miye bana miki Emily? Wane irin gata ne ban baki ba? Wane irin jira ne ban yi ba akanki? A duk lokacin da na miki maganar aure hankalinki wani gurin yake tafiya, gaba daya ba nine a gabanki, na gaji yanzu, waya zo gurinki ko kuma gurin wa kika tafi?" Ta ki ta yi magana, a take ya wulgar da ita kasa da dukannin karfinsa, sai kuma ya bita ta kama abayar jikinta daga saman gurin v shafe dake gaban rigar ya yaga daga sama har kasa. "Ba zaki sake saka wannan tufafin ba, ba zaki sake kula kowa ba, you already know yadda raina yake baci idan kika kula wani miyasa kika yi? Me yasa kika kasa karbata har yanzu?" Ta dauke ta da mari, ya kai mata duka a fuska kamin ya mike tsaye ya cire belt din jikinsa ya fara dukanta tana ihu, and he keep questioning her. Sai da yayi mata duka sosai irin dukan da be taba yi mata ba sannan ya jefar da belt din ya zauna kan kujera tana kallon yadda take murza jikinta tana kuka, a yanzu kuma sai ya ji ransa ya fi baci akan duka da yayi mata fiye da laifin da ta aikata. Bedsheet din kan gadon ya yaye ya lulluba mata a jikinta da babu komai sai underwears, ya zauna a gurin ya rike kansa. "I'm sorry" "Ka kashe ni kawai, na gaji" "Ba zan kashe ki ba, amman zan kashe mutumen da yake ziga ki, na san ba zai wuce wannan dan iskan yaron na gurin aikinku, ba mamaki shi ya turo NDELA har gida na" Emily na jin haka ta yi karfin halin tashi zaune. "ba shi ba ne, karka dauki alhakinsa, mutumen da nake aiki a tare da shi shi ne mutumen da ya taimaki ni lokacin da na kusa rasa rayuwata da cikin Fatima, shi ne mutumen da nake ta ajiyar agogonsa, he has nothing to do with this, karka cutar da shi Vito, idan wani abu ya same shi ba zan taba yafe maka ba, kuma ba zan taba yafewa kaina ba" Ta karasa daker tana kuka, ya kalleta ya sake kallonta ya sake kallonta a karo na uku, ya rasa me yasa ta kasa kaunarsa ta kasa bashi hadin kan da yake bukata, bayan duk abun da yayi mata, bayan duk tsawon shekarun nan da suka dauka tare bayan dubun kyautatawa. Mikewa yayi tsaye ya fice daga dakin ya dawo falo ya zauna ya saka hannunsa aljihu ya ciro wani karamin kwalba mai kamar akwati ta zuba wata farar hoda a hannunsa ta shaka da karfi ya rufe ido yana juya kai na dan lokaci, sannan ya tashi ya fice daga gidan gaba daya. ALIYU POV. Da farko yawo ya so yayi da Fatima sosai kuma yayi mata siyayya amman halin da ya bar Emily ya tsaya masa a zuciya, hakan ya saka shi canja kudirinsa na kai Fatima park da guraren shakatawa ya tafi da ita super market kawai ya siya mata kayan wasa da na ciye ciye, tana zabar abun da take so yana tambayarta sallah nawa ake a wuni, me ake karantawa da wane lokaci ake yi, kuma ita tana yi ta bashi amsa daidai ban da yin sallah, tana yi sallah ne a duk lokacin da take sha'awar yin sallah, sai da suka shiga mota ya kama hannunta yana murmushi yace. "Yanzu ki min alkawari kullum zaki yi kowace sallah babu fashi, kuma komai kike zaki aje ki yi sallah" "Wata rana ina gajiya fa" "Eh ko kin gaji ki yi a haka, ai ba zaki so idan kin mutu a kona ki ba ko?" "Eh" "Good kina son idan kin mutum na musance a aljanna ko? Guri mai kyau da ni'ima kuma komai ake so za a samu a ciki" "Har da kayan wasa" "Sosai da kayan dadi kala kala, amman sai idan mutum yana yin sallah, kin ga ina son ki ba zan so ki shiga wuta ba" "Eh ba zan shiga ba wuta ba, Momy ce zata shiga wuta ita ce bata sallah, kuma ita ce kafira" Aliyu yayi murmushi mai sauti. "Toh a duk lokacin da kika yi sallah ki rika rokon Allah yasa Momy ta dawo hanyar musulunci, ai ba zaki so a kone ta ba ko?" "Eh amman wata rana ina son a kone ta sai a cireta" "Aa babu kyau Momyki tana sonki ita ma ba zata so ki kone a wuta ba, duk wanda kake so ba zaka so ya shiga wuta ba" "Sai wanda baka so? Toh Vito ina son ya kone a wuta yayi baki ya soyu" Nan ma Aliyu dariya yayi "Aa shi ma ki masa addu'a Allah ya shirya shi ya dawo musulunci" Ta lake kafada ta turo baki gaba. "No bana son shi ba zan yi ba" "Zan rika biyanki idan kina musu addu'a" "Noooooo bana son shi i hate him ni bana son shi" "Da alama kina da kafiya Fatima ki daina ba shi da kyau kinji don't be a stubborn girl" Ta makale kafada ta juya masa, murmushi kawai yayi ya daga wayarsa ya kira number Emily sai ya ji ta a rufe hakan ya dan kara masa damuwa. "Fatima da kuka fito Vito na cikin gidan?" "Aa Chidimma ce kawai" Ya sake gwada kiran still switch off. A take hankalinsa ya tashi, gashi tace kar ya zo har sai ta kira be san me zai yi ba a yanzu kuma be san a wane hali take ciki ba. Sai da ya fara tuka motar yayi nisa yana ta sake sake kamin ya kama hanyar gidan Tasmia ya faka harabar sannan ya fita ya taka zuwa kofar shiga gurinta ya kwankwasa, shiru ya sake knocking nan ma shiru, wayarsa ya ciro ya shiga WhatsApp ya lalubo chat dinsa da Tasmia ya duba number ta yayi coping ya saka a dial ya kirata, ringing uku ta yi kamin ta yi na hudu ta yi picking. "Hello" Sai yayi mata sallama kamar yadda ya saba yi na kowa, ta amsa masa ta gaishe shi, bayan ya amsa ya dora mata da dalilin kiransa. "Am... Alfarma nake nema" Ta yi jimmmmm kamin ta amsa. "Fadi komai kake so Aliyu, ai ban kai matsayin da zaka nemi alfarma ba, sai dai ka yi min umarni, kuma dole na na bi ko da kuwa wuta ka ce na fada" Ta fada with excitement. "Interesting... Okay.. Anyway na zo gidanki ban same ki ba" "Allah yasa ba laifi aka ce na yi ba ba" "No ina son kije gidan Emily ne ki duba min ita, ina tare da Fatima a yanzu, bana son na je gidan har sai na yi magana da ita, kuma jikina yana ba ni ba lafiya ba" A take yanayin muryarta ya sauya saukin kiran da take ya ragu. "Ni fa bana son jefa kai a matsala,
Chapter 83 · 0% Book details