← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 177

Sashe 115

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

mana ba? Kuma na san Emily ai tana nan ko?" "Eh haka ne, Emily tana nan tare da mu, Aliyu kuma be fada min ya aikata muku wani abu ba" Ammy ta sauke ajiyar zuciya. "Na san kin san yadda muke ta faman neman Emily, shi kansa Aliyun ya fi kowa sani domin Turhan be boye masa komai ba, amman ace Aliyu ya san inda Emily take wai har da ya a tsakaninsu amman ko da wasa be kyankyawasa Turhan ba?" Ummi ta hade yawu. "Ammy a yanzu ba zan iya bawa Aliyu kariya ko wanka ko dora masa laifi ba, Aliyu dai danki ne kamata yayi ace ki same shi ku tattauna" Ammy ta yi murmushi mai sauti. "Emily tana gurinki ne duk tsawon lokaci nan ko kuma dai a yanzu ne ta zo nan" "Aa ni ma a yanzu na san da ita, shi ma saboda abubuwan da suka faru ne na daukar yarta da Kameela ta yi ta kai muku ba tare da izininta ba" "Ai Kameela ta kyauta mana Wallahi, ba dan ita ba wata kila da har yanzu ba mu san komai ba, kuma Aliyu ya san yadda Turhan yake ta neman yaya" "Ta kyauta tun da ta raba uwa da a, kuma ta raba igiyar aurenta kin ga ai ta ci riba, ni kuma sai na yi mamakin da aka ce Fatima tana hannunku kun riketa uwarta tana nan tana fama da kewar da damuwa, kun san yarinyar bata da gata sai Allah, gashi yanzu har ta bar musulunci" "Ummi ya kike magana kamar kina goyon bayan Aliyu? Kina ganin hakan daidai ne kenan?" "Bana goyon bayan Aliyu, amman ni dai na san ban manta lokacin da kike zuwa kamun kafa a gurin Daddyn Aliyu ba saboda kina neman a baki dama ki samu ganin Turhan, daga baya kuma kika koma rokon a bar shi ya rika zuwa inda kike, ke dai uwa ce na san kin san zafin rabuwar da da uwa, ya kike tunanin Emily tana ji a yanzu? Yarinya ta raini yarta shekara da shakaru rana tsaka ku dira a rayuwarta ku karbe mata ya? Anya kun yi adalci kuwa? Abun ma ai da kunya" "Ba karbe muka yi ba, mun rike ta ne ta yadda zata saba da mu, ke kin sani Turhan kadaina haifa, ko kare aka ce nasa ne ya kike tunanin zan so shi balle jika? Ni dai ban aurawa Emily Turhan da nufin cutar da ita ba, idan ma ba su fahimci juna ita da Turhan ba, ni be kamata ta saka ni ciki ba, kuma ko yaya dai za a juya a juyo Emily tana da igiyar auren Turhan a kanta karki manta da wannan" "Ammy idan kin zo saboda Emily ne, tana sama daki na farko hannun hagu, ni dai ba zan fada miki fari da baki akan jikarki da yarki ba, kabli da ba'adin rayuwa kin sani, idan kin yi daidai ko akasin haka a bayyane yake, ni zan shiga na karasa girkina" Ummi ta mike tsaye ta nufi kitchen, Ammy ta bita da kallo mai wuyar fassara sannan ta tashi ta haura sama ta shiga dakin da Ummi ta fada mata Emily tana ciki. Emily ta sauko da kafafuwanta kasa ta kalli kofar tana jin tsanar sunan Kameela ma balle kuma abun da ya alakance ta. Mikewa ta yi tsaye ta nufi inda take kyautata zaton bandaki ta tura ta shiga. Kallon ko'ina ta yi komai yana nan na gyara jiki ko gashi na maza kai kace Aliyu yana rayuwa a gidan har lokacin. Shaving cream ta fara dauka ta duba sannan ta duba shower gel, ta nufo shower ta kunna ta daga kai tana kallo ta tara hannunta ruwan ya zuba a hannunta sai kuma ta juyo gurin madubi ta kalli kanta kamin ta kunna tab ta fara wanke fuskarta, bayan ta gama ta dauki karamin tawul data gani aje a gurin ta dauka ta goge fuskarta ta aje sannan ta fito, tana karewa dakin kallo gaban madubin gadon ta fara nufa tana duba turaruka da suke gurin da mayuka na maza na gyara jiki, daya bayan daya ta dauka tana dubawa sannan ta aje ta nufi closet ta bude tana kallon tufafinsa talkaminsa da kuma hulluna. "Assalamu Alaikum" Sallamar Ammy ce ta saka ta juyowa ta kalli kofar sai ta maida kanta gurin kayan da take kallo ba tare da ya amsa ba. "Kina fushi da ni har yanzu, amman baki fahimce ni ba ne Aisha, bana nufin cutar da ke, daga lokacin da kika bar min wasikar nan kika gudu ba sake walwala ba, Turhan be saka samun damata ba, na yi mamakin da na ganki a cikin wannan shiga da kuma canja addinin da kika yi, wannan duk be dace da ke ba" Emily ta juyo ta kalleta. "Toh me ya dace da ni? Cigaba da zama da mutumen da na fi kaunar mutuwata a kansa? Ko kuma yarda da surukar da ta fifita farincikinta akan nawa? Ke kika fada min danki zai ba ni farinciki zai ba ni gata, sai gashi danki ya maida ni baiwa a masarautar da shi ya kamata ya ba ni gata, ya maida ni kurma alhalin ina ji, ya gabatar da ni masarautar a matsayin baiwa da kika ba shi, ko wace safiya sai na wanke bangaren matarsa, bana iya cin abincinsu a haka nake daurewa, ko da yake laifina ne, ai ya gargade ni tun kamin na aure shi, yace kar na amince, amman saboda ina son na faranta miki rai na miki sakamako da abu mai kyau na amince, ban taba son Turhan ba, kuma ba zan taba son shi ba, na aure shi saboda ke, a daren ranar da aka daura auren ya fada min bakar rana ce a gurinsa, a daren da aka samu cikin Fatima ya fada min bakar rana ce a gurinsa, ya fada min ba zai taba so na ko son abun da zai fito daga gareni ba, na azabtu a masarautar nan kyautar da ni aka yi ga wata mata matsayin baiwa da haka na zamu yanci, na raini cikin yata cikin wahala na haife ta ta girma ba tare da kulawa daga ubanta ba... Ko da yake ba zaki fahimta ba danki ne a gabanki..." Ta karasa tana girgiza ka tana share hawaye. Ammy ta kai zaune tana hawaye. "Na aura miki shi ne da tunanin ke da shi kuna son junanku, ni ma na yi makamanciyar rayuwar da kuka yi, amman ni na cutu ne saboda mahaifinsa baya so na, ban yi tunanin Turhan zai kyamace ki ba, shiya sa sai da na zaba na mika masa, ban ba shi gama garin bakar fata kamar sauran ba, ban yi nufin kulla Sheri ba Emily alheri na yi nufi" Emily ta dauke kai. Ammy ta nuna kusa da ita. "Zauna... Zauna ki fada min wane irin zama kuka yi, kuma me kike bukata a yanzu?" Emily ta kalli Ammy da idonta suke cike da hawaye sannan ta zauna tana aje numfashi mai nauyi a muhallinsa. [7/14, 6:25 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA
Chapter 115 · 0% Book details