Sashe 42
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 1 Tun daga wacan ranar ban saka ganinsa ba, amman ban manta sunanansa ba, ban manta kyaun fuskarta domin Khaleefa yana da kyau sosai kwatankwacin yadda mutane suke baya kyauna. Kusan zan iya cewa kyaun ne abun da ya ja hankalina izuwa gareshi. Na cigaba da rayuwata ta yau da kullum kamar yadda na saba a gidanmu na marayu, da safe zan tafi makaranta da yamma kuma na leka gurin aikina na gyaran mota wato garejen oga Shakur, idan aka samu aiki yayi kyau ko kuma muka samu customers da yawa a ranar yana min alheri kamar yadda ya saba. Kasancewar yau assabar na tafi aikin tun safe ban tashi ba sai yamma, da zai sallame ni yayi min sallama mai kyau, ba karamin faranta min rai yayi ba hakan ya kara min karfin guiwar tafiya gida, na yi wanka na shirya na fito domin kashe kudin da aka bani, domin abu ne da kowa ya shaideni da shi alheri hali na, idan na samu kudin na kan sawo abubuwan dadi na kawo, kowa ya saka hannu ya ci, ban san na ci ni kadai ba. Na isa gurin na gaisa da shi da yaren igbo na ba shi kudi nace ya hada min kayan marmari, a nan yake fadan min domin da na taimakawa yayi siyayya ranar nan kullum sai ya zo nemana. Da mamaki na tambaye shi. "Nema na? Me zan masa?" Yayi murmushi ya koma cikin karamin shagonsa ya dauko farar takardar ya miko min. "Number ce ya rubuta yace idan kika zo a baki, duk da haka kuma yana zuwa kullum da zaki iya jiran shi anjima kadan zaki ga ya zo" "Amman yace na yi masa laifi?" "Alamu be nuna hakan ba" Ya miko min ladar na karba, har zan tafi sai kuma wata zuciyar ta ba ni shawarar na tsaya na jira shi mana idan ma wani abun ne ai zan ji. Haka kuwa na aikata na zauna a gurin muna ta hira da Mutumen sai ga shi ya iso da babur dinsa kamar wacan karon. Tun kan ya sauko daga kan babur din fuskarsa ta washe da murmushi, ya karaso kusa da inda muke zaune yayi min sallama, na amsa masa kamar musulmai, sai ya washe hakora. "Garkiwata kamar dai kin fini iya hausa" Na yi murmushi zuciyata na bugawa da wani irin karfi, irin bugun da bata saba yi ba. "Kana ta nemana aka ce, amman dai ba laifi na yi ba ko?" "Laifi kika yi babba kuwa" Ya fada yana dagawa igbon hannu tare da mika masa 2k. "Laifin me" "Kin san kin taimake ni a nan haduwar farko, haduwa ta biyu kuma kin ceto rayuwata kin ceto abun hawana kuma abun sanata, tun daga lokacin zuciyata bata barni na zauna laifi ba, na yi bata hakuri har na gaji amman bata bar ni ba, wata kila saboda ba ni da kowa a garin lagos ne, wata kila kuma saboda taimakon da kika yi min ne, ko kuma dai saboda kina marainiya ne amman dai kin tsaya min a rai kuma kin ba ni tausayi sosai" "Baka da kowa a nan" Na tambaya da mamaki fuskarsa na cika ni da kwarjini, ba dai kyaun ba kam Khaleepa akwai kyau kamar dan indiawa. "Ba ni da kowa, kawai na biyo abokina ne da yake achaba a Lagos saboda ance yafi arewa samun kudi, sai na zo ni ma nake yin achaba, ban san kowa ba sai ke sai abokin nan nawa, sai kuma mutumen igbo" "Interesting" Na furta not knowing what to say next, yayi tagumi yana kallona. "Ashe dai zan sake ganinki, na ji kamar na yi hauka, kullum sai na zo nan neman kyakkyawar fuskar nan" "Amman ya kan yi ka iya magana da igbo nan bayan baka jin yarensa" "Wani na samu yake rubuta min duk abun da nake so na tambaye shi idan na zo, sai shi ma ya rubuta min idan na tafi gurin wacan sai a fassara min" Na yi murmushi ina yaba karfin halinsa, amman fa ya burge ni, neman ganina kawai zai saka shi wannan hidimar. "Ni zan tafi" "Haba ban gama kallonki ba fa, kuma kin san yaushe nake bata lokaci ina zuwa nan nemanki" "Idan na dade ban dawo ba kawaye za su neme ni, kuma ba a son muna fita muna dadewa a waje ba tare da wani dalili ba" "Shikenan muje na rakanki, akwai abubuwa da yawa da nake son sani akanki, kamar yadda aka yi kike jin hausa, kuma kike da kirki da kulawa, kuma gashi kina da kamun kai, dan na yi mamakin yadda na baki kudi baki karba ba, kuma gaki kyakkyawa" Duk yadda na so na tafi ni kadai be yarda ba sai da ya goyani da babur dinsa ya kai ni kusa da gidanmu na marayu, a boye na sauka domin bana son kowa ya gan ni, idan aka gani ma za'ayi min fada. Ya sake rubuta number shi ya ba ni ya bani kudi a nan din ma ban karba ba, be tafi ba sai da na masa alkawarin zan kira shi mu gaisa da wata wayar. A ranar kasa cin abincin dare na yi, na gagara cin kayan marmarin da na siyo sai tunaninsa nake, a wacan lokacin akwai kurciya sosai a tare da ni, domin ina da shekara goma sha biyar ne, a lokacin ina sss1, gashi kuma wani be taba nuna min kulawa kamar yadda shi ya nuna min ba, ina da kyau wannan abu ne da ni kaina na sani, amman kyaun nawa be taba sakawa wani be taba nuna min kulawa mai kama da soyayya kamar shi ba, sai dai mutane su na haba haba da ni, wata kila suna gani ko tunanin ni na yi karama ne. Abu kamar wasa muka fara shakuwa da juna, da wayar mai dafa mana abinci a gidan nake amfani ina kiransa mu gaisa, wani lokacin har cin hanci nake bata, shi kuma da zarar ya ga flashing dina zai kira mu dade muna yawa, idan yana son ganina kuma zan boya na tafi nesa da gidanmu na hadu da shi mu ga juna, a gaskiya na so Khaleepa a wacan lokacin irin son da idan ina tunaninsa bana iya bacci, idan ban yi waya da shi sai na wuni cikin wani yanayi na rashin dadi, a makaranta gurin aiki bana da komai sai tunaninsa. Wani lokacin zai yi min siyayya sai na boya na shigo da ita ba zan fadawa kowa ba, ranar da Marry wacce take kasan gadona ta gane ina soyayya ta tsare ni da tambaya har sai da na fada mata shi ne mutumen da muka hadu kuma na fada mata shi musulmi ni, sai ta fusata kuma ta tsorata ni cewar ai su musulmai basa auren kafirai, kuma a arewa ba a son wanda ba bahaushe ba, arna suke kiranmu, a madadin na yi nazarin kalamanta sai soyayya ta rufe min ido na fara gaba da ita. Na same shi da maganar tabbas a lokacin, sai ya karyata abun da ta fada, a nan yake fada min asalinsa da gidansu da garinsu da yake kauyen Kaduna. Ya nuna min fargabarsa ta daga gurin inda nake zaune ne, yana ganin kamar ba za a yarda a aura masada ni ba, a lokacin ni ma hankalina ya tashi domin na san ba za su yarda ba. Haka dai muka cigaba da soyayya, yana fada min idan ya aure ni, zamu yi rayuwar aure mai kyau, zai nuna min soyayya zamu rika cin abinci a tare wanka kwana komai kamar na masoya, ashe karya yake amman ni ban gane ba, kawai abun da ke daukar hankali kyaunsa da kuma yadda be taba yarda ko da wasa ya taba nuna son taba jikina ba, har ta kai yana kiran mahaifiyarsa ya ba ni mu gaisa, be min karya ba ya fada min sana'arsa kuma ya fada min shi dan kaduna ne, amman a kauye suke zaune tare da iyayensa. Soyayya da muka fara da Khaleepa kusan kamar ta budewa maza kofa ne, domin babu ranar da zan fita wani be nuna yana so na ba, amman bana sauraren kowa sai shi, idan naje church kullum addu'ata na yadda kowa zai amince na aureshi ne. Ana haka wata rana aka shigo kirana tare da sauran yan mata sa'anin na, muka tafi sai muka samu wasu manyan mutane ne suka zo neman ya da zasu rike kamar su suka haifeta. Daman akan yi hakan wasu jarirai suke so, wasu kuma wadanda suka dan tasa, amman ita tace tana son matashiyar buduwarwa, domin ta taba daukar jaririya kuma ta reneta tana can hannunta a gurinta ta girma. Matar tana yin arba da ni, sai ta zabe ni, suka ba ni damar tafiya na shirya domin a ranar zan tafi bayan ta yi duk abun da ya kamata, a ranar na sha kuka sosai a gurin abokan zamana na gidan, domin tun muna yara muka taso tare, har na ji kamar kar na bita, sai dai kuma ina son tafiya ni na shiga family na samu wanda zata rike ni a matsayin ina son na rumgumeta na ji yadda ake ji. Gidanta babba gida ne a lagos tana da masu kyau, ga manyan motoci da ac abinci sai wanda na zaba nake ci, tun a ranar da aka kawo ni ta fada min ita bata taba haihuwa ba, tana da jiki sosai likitoci sun ce kitse yayi mata yawa ba zai barta ta haihu ba, hakan ya saka take son rike yara kamar yaranta. Ta nuna min kauna tace zata rike ni kamar yarta, ban maida sati a gidan ba aka canja min makarantar da nake zuwa makarantar masu kudi makaranta mai kyau. Mukan zauna musha hira da ita idan na dora kaina a jikinta sai na yi ta kuka, ashe dai ni ma wata rana zan samu masu sona. Ta tambaye ni a ina na iya duka yaruka hudu da nake ji, na fada mata yaren Igbo da yarbanci daman kowa ya iya a Lagos domin mun tashi mun ga su ake amfani da su, turanci kuma ba iya a makaranta, hausa kuma na koya a gurin