Sashe 11
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Barka da warhaka mutanen arziki Shim kun san cewa Khadeeja Candy komai da komai? Amman banda an mutum da mutum Ina masu neman kayan Kitchen masu kyau masu inganci, Luxury Warmers manya da kanana, ina masu neman Bedsheet kings and Queens manya da kanana, ina masu neman Akwaitunan lefe da na tafiya. Khadeeja Candy na da Boxes kala kala, ina masu neman tufafi, kama daga Atamfa, Laces, Shadda Lace, Veils, shoes and Bags, Materials. Akwai freezer, Gas cooker and water dispenser. Duka zaku samu a gurin Khadeeja Candy Store, Khadeeja Candy dai taku ta makaranta, da fatan za ku yi patronizing ina. Za ku iya join group dina domin bawa idanuwanku abinci https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Kuma zaku iya saka order ta wannan number 08036126660 WhatsApp. KHADEEJA CANDY STORE expect more, and pay less... Page 5 Bata sauko ba sai da ta tabbatar ya fice daga gidan, sannan ta sauko ta sakawa Fatima lunch dinta a lunch box ta shirya mata komai kamar yadda ta saba, Londom kuma da ake masa darasi a gida sai ta zuba masa a nasa na nasa kayan cin abincin, sannan ta haura saman ta shiryawa cikin shiga ta riga da wando ta saka turare ta maida sarkar Cross dinta a gaban rigarta yadda zata fito da kyau. Red hair dinta ma ya faku da kyau ta yi kyau ta fito tsab, kana ganinta ka ga kyakkyawar mace mai aji, da matukar daukar hankali. Id card dinta na aikin ta fara dauka ta saka sannan ta dauki jacket ta saka saboda yanayin garin akwai sanyin sai dai ba sosai ba. File din jiya ta dauka tare da jakarta ta wayarta ta fice daga dakin, sai da ta shiga dakin Londom ta duba shi ta sunbance shi sannan ta fito ta leka dakin Fatima, sai ta same ta zaune da alama farkawarta daga bachi kenan. Da murmushi Emily ta karasa kusa da ita ta aje kayan dake hannunta ta shafa kanta. Good Morning Princess Fatima ta kalleta ba tare da tace komai ba. Okay jiya na san mun yi fada kamin ki kwanta kin kwanta da fushina I'm sorry Ta bata fuska. I just hate Vito Mom, ke kuma kullum kina shigar masa baki ganin laifinsa Princess V be mana komai na ganin laifi ba, yana kula da ku yana kula da ni, gidan nan da duk abun da yake ciki nasa ne, be taba mana komai ba I just hate him, bana son ki aure shi Momy Ta fada cikin kuka, Emily ta juyo ta fuskance da kyau damuwar ganin hawayen yarta na bayyana a fuskarta. Ba aurensa zan yi ba, ni na gama aure a rayuwata, amman baki da dalilin tsanarsa, shi yake kula da mu, shi kadai ne mutumen da ya rike ni ba tare da kyama ba, shi kadai ne ya kaunace ni a yadda nake yake kokarin kyautata min, shi ya maida ni yadda nake a yanzu Ya fada min aurenki zai yi ko da bana so, yace min na fara kaunarsa tun a yanzu saboda shi zai zama step father dina No no... Princess ba zan auri kowa ba, ba zan aure shi ba, ba zai zama stepfather dinki ba, but ya kamata ki girmamashi No... To mu bar masa gidansa Momy Emily ta shafa fuskarta. Shi ne kudirina, amman ba zan iya haka ba sai na tsaya da kafafuwana, shiyasa na dage nake son fara aikin nan, zan rika saving kudi idan na tara zan koma wani gurin za mu bar masa gidansa da komai nasa, na miki wannan alkawari Fatima Fatima na jin haka sai ta rumgume ta da sauri tana murna. Promise Mom I promise Ta fada yana shafa bayan yarta, Fatima ta dago daga jikinta ta rike fuskarta. Momy a ina kika samu aiki Wani babban kamfani ne dake hakar ma'adanai da bincike akan albarkatun kasa, babba guri mai girma kuma mai hawa har biyar Ke a hawa na nawa kike? Na hudu, ina aikin da wata mace mai mumman hali, sunanta Amal kin san musulmai ba su da kirki ko? Ita ma bata da kirki ko kadan Fatima ta wara ido kamar ba ita ce ta gama fushi dazun ba. But I'm Muslim Mom you know Emily ta ja kumatunta. "You're different because you were raised by a Christian mother" Ta yi dariya ta sauka daga kan gadon, Emily ta bita da kallo tana jin kaunarta sosai, haka take son yaranta fiye da kanta, tana son farincikinki yaranta fiye da nata, bana son su rasa komai domin ta san yadda ake ji idan ka rasa wani abu, domin ta tashi ita kadai ba tare da yan'uwa ko iyaye ba. Ta sani ta rasa farinciki, sai dai ta daukarwa kanta alkawarin ba zata yarda yaranta su rasa farinciki ko su shiga makamanciyar kazantacciyar rayuwar da ta shiga ba. Tana zaune gurin har Fatima ta fito daga bandaki ta shimfida karamin sallayarta ta dauki hijab, kallonta kawai take cike da burgewa tana jin dadi tana jin farinciki a duk lokacin da ta ga yarta tana ibadar da ta zabarwa kanta, bata son tauye mata hakki ko kadan hakan ya saka ta barinta ta aiwatar da addinin da ta dorata akanshi da farko kamin ta yi kokarin canja mata ra'ayi hakan kuma ya gagara saboda abun da shiga zuciyar Fatima sosai. Even though ba ko da yaushe take sallah ba, amman duk inda zata shiga ko a tambaye zata fadi cewar ita musulma ce, hakan kuma ya kan bawa duk wanda ya san mahaifiyarta mamaki, domin mutanen da suka san Emily a yanzu sun santa a Christian, kamar yadda sarkar Cross din dake wuyanta take nunawa a kullum. Okay Princess zan tafi aiki, na san yanzu Chidimma zata shigo ta shirya miki zaki tafi makaranta, i love you Ta fada sannan ta mike tsaye ta dauki kayanta ta fice daga dakin. Ta yi tafiya sosai kamin ta samu abun hawa kasancewar safiya ce ba kasafai ake samun ababen hawa a unguwar da safe irin lokacin da ta fita ba, gashi bana da ra'ayin amfani da motar da V ya siya mata tana son nesanta kanta da wasu abubuwan ne tun a yanzu. Karfe bakwai daidai mai texi din ya shiga da ita cikin kamfanin, sai da ta sallame shi sannan ta fita tana kallon yadda a yanzu ake bude wasu bangaren ma, masu shara da mopping na yi. Tsirararun mutane ne kawai suke shigowa a kamfanin. Kai tsaye ta shiga ciki ta hau Elevator zuwa 4 floor din da take, a nan din ma ta samu masu mopping suna gyara floor din. Da Keys din hannuna ta yi amfani ta bude kofar Office dinta ta shiga sai ta shiga ga mamakinta sai ta samu an goge ko'ina. Da mamaki ta aje file da jakar hannunta ta fito ta tambaye wani namijin dake mopping a gurin. Dan Allah ka ga wanda ya shiga office din nan? Gaskiya bayan ni babu wanda ya shiga Kai ka gyara office din? Eh ni na gyara ni nake gyara ko'ina ai Kana da key din dakunan kenan? Eh ni nake kula da ni ni aka hannatawa komai Okay sannu da kokari Ta koma ciki, har ta zauna sai ta tuna da Office din Amal a take ta yi hanzarin tashi ta fito ta nufi office din ta bude sai ta juyo ta kalleshi. Me yasa baka gyara nan ba? Tace ke zaki rika gyara mata Okay... Ta furta with little bit of confused, why her? Bayan ya fada mata shi yake gyara ko'ina, ko da yake Amal din ta fada mata da kanta tun a ranar farko. Idan ka gama ka ara min mopper zan gyara gurin A madadin ya bata sai yayi mata jagoranci zuwa gurin da ake aje moppers din ta dauko daya da tsintsiya ta gyara office din tsab sannan ta mayar ta aje. Komawa ta yi office dinta ta zauna bata san me zata yi ba dan haka ta bude data ta ta shiga social media sai misalin tara ma'aikatan kamfanin suka fara shigowa. Misalin 9:15am telephone dinta ta yi ringing, a gurinta abu ne sabo a kirata da telephone in her own office, sai da ta yi murmushi sannan ta amsa kiran Hello Ki same ni a office Oka... Kamin ta karasa wayarta furta okay din Amal ta aje telphone din. Emily ta mike tsaye ta fice daga office din zuwa office din Boss dinta. Tsayawa ta yi tana knocking domin bata manta gargadin da tayi mata ba a jiya. Ta mata izinin shiga bayan ta bata lokaci tsaye a gurin. Good Morning Maa Na fada miki sunana Amal ki daina kirana Maa kamar wata tsohuwar I'm sorry Waya gyara dakin nan yau? Ni na gyara Good, sauraka kasa ki samo min snacks zan yi breakfast da ki siyo min bubble tea Ta jafa mata Atm dinta, tana duba wasu takardu. Ina file din da na baki jiya Emily ta kalli Atm din dake kasa, me yasa ba zata iya bata da hannunta ba ko ta dora a tebur ta dauka? Me yasa take son wulakantata? Ko da yake ba abun mamaki ba ne ita din ai musulmace, ta duka ta dauki Atm din tana amsa mata. Yana office dina Idan kin ga dama ki kawo nan Kallonta kawai Emily ta yi ta juya ta fice daga office din, nata office ta koma ta dauko file din ta sake knock ta tsaya har sai da ta yi mata izinin shiga sannan ta shiga ta aje mata ta fito. A nan kuma ta fara tunanin ina zata samo mata snacks da bubble tea a yanzu, ita ba sanin kamfanin ko unguwar ta yi sosai ba. Haka dai ta nufi elevator ta danna botton din dake jiki ta bude mata, ta shiga sannan ta taba number 1, a take ta fara yin kasa har ta isa first floor ta fita, wata zuciyar na fada mata ta tambaye mutane wata zuciyar kuma na hana ta, ita wa ta sani ma balle ta tambaya. Haka ta mike ta fita daga roof din kamfanin ta mike doguwar hanyar har ta isa gate. Ta kalli dama ta kalli hagu kaminnta yanke shawarar nufar left side tana tafiya tana dubawa ko zata samu mai siyar da