← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 177

Sashe 68

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

da hawaye. Ya dauki takardar a gabanta ta ciro pen a aljihunsa ya dora a kai. "Idan ina son na canjawa Fatima suna daga Fatima Aisha Emily zuwa Fatima Aliyu Mudallab ya kike ganin zai kasance rubuta min" "Canja sunan Fatima yana nufin daukar ragamarta ne, tsaya mata a matsayin uba ne a kowa guri a kuma ko wane irin hali" "Abu ne kamar ruwan Sha a gurina ko ban yi dan tana yar abokina ba da zan yi dan ke Emily, ki barta ta dandani dadin da yake karkashin inuwar uba" "Na gode da kokarin da kake ta yi Aliyu, amman wannan karon ya zama dole na yi rejecting wannan offer din" "Idan baki ra'ayin sunana ai zaki iya so na Vito ko? Shi zaki iya rubuta min yadda sunan zai kasance saboda gudun kuskure" "Fatima bata karbi Vito a matsayin Uba ba, ba zata yi farin ciki da hakan ba" "Ban taba tambayarta da kaina ba, ban ji amsar daga bakinta ba, dan haka karki yanke hukunci, idan tana ra'ayi ba sai na saka kin rubuta ba, idan kuma bata ra'ayi kin ga shikenan mun huta" Ta rubuta masa full name din Vito da na mahaifinsa ajikin takardar, sunan da babu wanda ya sani sai ita sai mahaifiyarsa sai kuma amininsa na kud da kud sai kuma daidaikun mutanen da aka haifeshi a gaban idonsu Aliyu ya karbi takardar ya karanta. "Toh ina Vito ya samo asali?" After Aliyu yayi mata tambayar ne ta fahimci babu amfanin using wacan sunan a yanzu tun da ya zabi canjawa. "Shi ya canjawa kansa suna saboda sana'ar da yake a yanzu kowa Vito yake kiransa amman ya fada min ba asali sunansa ba ne" Aliyu ya dan yi murmushi kadan yana kara karanta sunan. "Za a iya kiranta Fatima Vito" "Mun gama da yau zaki iya tafiyarki a yanzu, gobe zaki zo aiki karfe 9am haka zaki rika zuwa kullum, Good Luck" Yana fadar hakan ya fice ba tare da ya tsaya jin ra'ayinta ba, is like kamar ya mata umarni ne, yana son ta bishi ta fada masa ba zata iya aikin ba amman ta kasa, lokuta da dama kimarsa bata bari ta musa masa wani abu. ALIYU POV. Office dinsa ya dawo the first time da ya fara yi after zamansa shi ne ya dauki wayarsa dake kan teburin ya duba miss calls din Kameela da kuma sakonta wai ya dauki wayarta ta ji sanyi. Yayi murmushi ya girgiza kai bayan ya gama karanta sakon, sannan ya kirata. Tana daga wayar ya ce. "Idan kin san zaki min maganar Emily ne ko wasu mata ko maganar kishi to ki bari na aje wayata ba sai mun sake kai ruwa rana ba" Sai kawai ta fashe masa da kuka. "Yanzu kuma mi na yi? Waya taba min mata yar jaririya ta yar amanata rabin rayuwata?" "Amman idan ni ce wani yayi min magana ai zaka ji haushi ko?" "Ke ai mace ce a karkashina kike kin san hukuncinki, ni kuma namiji ne, kuma ba lallai sai aure ko soyayya zata hada ni da mata ba, kuma karamar magana sai ki dauketa ki kai a gaban iyaye, na ja miki kunnen Kameela akan kame baki da rike sirri amman babu abun da ya canja" "Ka yi hakuri" Ta fada cikin kuka. Sai ya fadada murmushinsa. "Komai ya wuce yanzu ai, sai ki kiyaye domin ba zan daukar miki wannan ba, yanzu yaushe zaki dawo?" "Ka wuce ko?" "Eh mana, naje gurin Ummi har na dawo gida...." Daga haka ya dauko mata hirar yadda ya so su tafi gurin Ummi su kwana biyu amman ta ruguza komai, sun dade suna magana a waya har ya katse kiran ya kirata Video Call suka ga juna sannan ya fada mata Ummi zata aiko ayi bikonta. Yana gama wayar da ita ya taba chat kadan ya kira mahaifinsa shi kam sun dauki kusan awa daya suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Sai da ya tashi daga aikin gaba daya ya dawo gida sannan ya kira Ummi suna gaisawa ta yi masa maganar Kameela daman ya san zata masa shiyasa ya kira kawai ya gaisheta, daga karshe ta hanye shawarar aikawa ayi masa bikonta daga Kaduna kai tsaye a kawo masa ita har PH. KAMEELA POV. Bayan ta gama wayar da Aliyu a falon Mama Barakat ta mike tsaye zata fice ranta fess kamar ba ita ba, daman a duk lokacin da zata kira shi bangaren step Mom din tasu take zuwa saboda gudun kar ya amsa su samu matsala ko kuma yayi mata wata maganar marar dadi yan'uwanta su ji, gashi kuma Mama Barakat tana yabon Aliyu yana dan mata nasiha yadda zata bullowa lamarin ko ta zauna da shi, ba kamar uwarta da yan'uwanta da suke zugata ba suna zagin Aliyu, shiyasa ko kadan bata son su san tana kiransa ma, haka idan ya tura masa sako sai ta goge saboda kar a dauki wayarta a duba ace naci take masa da magiya. "Haka ya fi, ki daina bari shedan da zuciya na shiga tsakaninki da mijinki" Cewar Mama Barakat tana kokarin zama, ba dan ta ji tattaunawarsu ba sai dan ta ga alamar komai ya wuce a fuskar Kameela da Kuma muryarta. "Ke yanzu ko kishiya za a miki ai be kamata ki tada hankalinki ba Kameela kina da kyaunki daidai gwargado, mace bata gwada miki komai" Ta tabe baki. "Mama Barakat baki ganta bane, kyakkyawa ce kuma yarinya, ina tunanin ma duk yadda aka yi baturiya ce tun a gidan marayu ta tashi wata kila jefar da ita aka yi ko tsintarka, domin gashin kanta ja ne irin na turawa idanuwanta blue ga farinta ma ba fari ne irin na mu ba fari ne irin na turawa" Mama Barakat ta natsu sai kuma ta yi jimmm kamin ta ce. "A a ina take?" "Lagos wai" "Miye sunanta?" "Aisha amman Emily ake ce mata" "Tana da yara? Kina da hotonta?" "Ni mi zan yi da hotonta? Ko kishiyata ce ai ba zan aje hotonta ba balle wata banzar alaka can gamon tsintsiya da ragga, tana da yara, baban yarinyar ma nemanta yake ruwa a jallo wannan matar criminal ce, kin san daman yan Lagos da wadanda ba hausawa ba ba su da tarbiya ita kanta nemanta yake amman kin ga ta mallakewa mijina, ai Wallahi ina komawa ko dai Aliyu ya zare hannunsa daga gareta ko kuma duk yadda za'ayi ayi, haka kawai wata katuwar banza ta lakewa mijina" Tana sane take fadar yan Lagos ba su da tarbiya da kuma yare saboda Step Mom din ta ji haushi, ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya domin ta ciki na ciki ba son Mama Barakat take ba ko da kuwa zata bata duniyar nan, ta mike tsaye ta fice rike da wayar zuciyata cike fal da kiyayyar Emily. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [5/25, 9:50 PM] ABOKIN RAYUWA
Chapter 68 · 0% Book details