Sashe 152
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abun ne?" "Hawayen ba na tsakanin mutum da mutum ba ne, tsakanin Rai da Mahaliccinta ne, Wallahi na dade da gamsuwa Allah aya ne, wannan dalilin ne ya saka karbar musulunci ya zama abu mai sauki a gurina, ban sani ba ashe ma a musulma aka haife ni. A yau na ji karatun nan dabam, ban taba jin karatun da yayi min dadi ya tsuma jikina irin naka ba" Aliyu ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yi murmushi ya zauna a gurin. "Shi Alkur'ane abinci ne ga ruhi, waraka ce ga ko wace cuta, kuma tsira ce ga kowane rai, ga dadin karantawa, ga dadin sauraro ke ma wata rana zan so na ji yadda ta ki kira'ar take" "Anya zan iya?" "Idan kina tare da ni akwai abun da ba zaki iya ba?" "Ta ko'ina Aliyu kai ZaKi ne, ka tare duk wata kofa da zata nuna gazawata" "Saboda babu gazawa a tare da ke, na yarda da ke fiye da yadda na yarda da kaina, miyasa kike kwankwanto akan abun da ni na hango shi tun kamin ki fada" Ta share hawayenta tana murmushi. "Ta ko'ina fari kake Aliyu, har yanzu na kasa ganin dogon bakin a tare da kai, na kasa ganin abun da ake ta nuna min akanka" "Ke ce mace ta biyu bayan mahaifiyata wanda ta yarda ba ni da aibu kuma bana yin mata laifi, hakika Emily ke ta musammance" "Kai din gwanin magana ne, ka iya kalami, kowane harafi yana ratsa cikin jikina ya fahimtar da ni abun da da ban fahimta ba" "Saboda kin iya saurare ne, kusan ni bawa ne duk wani abun da sarauniya take son ta ji, halshe ne yake sarrafawa ya fada ba tare da neman izinina ba, jindadin yadda kike ba ni lokacinki, alfarma kike min na san ai ban cancanta ba, na gode da karramawa" "Sai ka rika yin abu kamar ni din wata ce Aliyu" Ta fada a shagwabe kamar mai shirin yin kuka. Ya duba ko'ina ya ga babu mai ganinsu. "Ni na taba fada? Sam sam sam ke din ai ba wata ce ba, ke Emily ce mace mai kyakkyawar zuciya, ga hakuri da juriya, macen da data sha wahalar rayuwa kuma ta cancanci girmamawa d soyayya daga gurin kowa, ba zaki taba zama wata ba, wata yana nufin wata wanda ba kowa ba, ke kuwa mutum ce har da rabinsa" Ta yi murmushi ta sauke kanta kasa. "Idan an min izini, ina son zan shiga ciki kin san ke ba muharramata ba ce, kuma a musulunci babu kyau mace da namiji su kebe su kadai" "A har a nan da yake fili kuma da rana?" "Ai bana iya banbance dare ko rana idan kika tsare ni da idonki, kwarjini kike min komai girman guri sai inji kamar muna a cikin karamin daki ne, shiyasa nake ta taka tsantsan kar na bata miki rai, Emily, au Aisha yau kin yi shiga ta mutumci na jidadin laifinsu ne basa fada miki yadda kike musu kyau shiyasa baki damuwa ki rufe kanki da jiki" "Su wa?" "Tufafin mana? Ita mace ai tsada ne da ita, shiyasa idan suka killace a jikinta suke yin kyau, basa son rabo da ita" "Haka suke fada maka?" "Haka na gani rubuce a fuskarki, ki daina musu da abun da baki iya canjawa Aisha kina yi ma tufafi kyau" Ya mike tsaye ya fice gurin ya barta a nan zaune a gurin fuska da murmushi, zuciya da annuri. Tunanin Aliyu ne raya daren Emily, tana ta tunanin da be ma kamata ta fara shi yanzu ba, ba zata iya cewa son Aliyu take ba bata shiryawa ma wannan ba, amman tabbas shi din na musamman ne a gurinta yana da wani mukami mai girma a zuciyarta a idonta kuma yana da nauyin kimar da ba zata iya aunawa ba. Sautin karatun Kur'ane ya tashe ta daga bacci ta bude ido ta juya ta kalli Blue-Tooth din dake aje kusa da kunnenta na dama, sannan ta juyo ta kalli Fatima dake zaune tana kallonta. "Momy kowa ya tashi tun dazun ke ce kawai baki tashi ba, har Uncle Aliyu ya zo ma, shi ne yace na kawo wannan redio mai magana amman kar na tashe ki" Emily ta yi murmushi ta janyo yarta jikinta. "Hmmm ban kwanta da wuri ba shiyasa na ke bachin safe" "Uncle Aliyu yace na rika kunna miki karatun kina sauraro idan an je na saka carji yace zai rika biyana kudi idan ina haka" Ya shafa fuskar Fatima. "Fatima kina son Aliyu ko?" Ta daga kai. "Yes" "Sosai?" Ta daga kai. "Shi da Dady wa kika fi so?" Sai ta rake murya kamar mai rada tana zare ido. "Dady, amman karki fada masa" Emily ta yi murmushi. "Momy ke har yanzu baki yin sallah? Kowa yayi sallah da safe, ke har yanzu ba zaki yi sallah ba? Gidan Ammy ana sallah nan ana sallah miyasa baki yi? VITO baya nan babu wanda zai dake ki" Tana maganar tana yatsina fuska. Emily ta tashi zaune. "Kin fara dawowa da halinki ne Fatima? Fada min magana any how?" Fatima ta yatsina fuska ta sauka kan gadon ta fice. Emily ta juya rai a ba ce tana sake arba da Blue-Tooth din da Aliyu ya aiko mata sai bacin ran ya gushe murmushi ya cika fuskarka, ya matsa ta kai hannu tana shafa Blue-Tooth din. Sai kuma ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki ta wanke bakinta da fuskarta ta fito, sleeping dress din da suke jikinta masu kama jiki ne, saboda ta girmama Aliyu ta dauko daya daga cikin hijab din da Ummi ta aje mata green ta saka sannan ta fita. Aliyu na tsaye yana magana da Nafisa Fatima na rike da kafarsa tana lilo, Emily ta fara saukowa sai duk suka kalleta. "Wow kin ga yadda kika yi kyau?" Cewar Nafisa, Aliyu ya kalleta daga sama har kasa ya sauke kansa kasa be sake kallonta ba har ta sauko, be kuma fasa murmushin da yake ba annuri ya cika fuskarsa. "Ina kwana Emily" "Lafiya kalau" Ta amsawa Nafisa sannan ta kalli Aliyu da already ya juya. "Ina kwana" "Lafiya alau, kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah" Ya juyo da sauri ya kalleta murmushin dake fuskarsa ya fadada, sai dai be ce mata komai ba sai da Nafisa ta shiga dakin kasa. "Alhamdulillah.... Baki taba fadin wani abu mai dadi irin wannan ba, musulunci zai miki kyau Emily sosai" Yaja mata kujera. "Bismillah zo ki karya" Ta nufi dinning din ta zauna tana tambayar ina Ummi. "Ta tafi dubiya, tace ba zata dade ba, bari na duba waje" Fatima ta amsa sannan ta fita da gudun wajen. Aliyu ya zuba duk wani abu da yake son karyawa da shi ya dauki plate din. "Zan shiga ciki na karya, ni ma yanzu na shigo" "Har a cin abinci nan din ya mana kadan ne?" Ya kalli gurin kamar wani bakonsa. "Kin manta karatun jiya ne?" "Aa da dare ma da shi na kwanta ina ta bita" "Allah yasa dai kin haddace" "Ido ma suka haddace abun da suka gani, balle abun da kunnen ya ji, ya ratsa kwakwalwa ya zauna a zuciya?" Aliyu ya sake dubanta da kyau ita da shi suka sakarwa juna murmushi. "Da alama dai ba zan sha wahala ba gurin taya hajarna" "Ai tuni aka siyar maka farashi daidai da aljihunka" Ya sauke yin murmushi amman wannan karon mai sauti, ya juya rike da plate dinsa ya haura sama. Sai da ya shiga dakinsa ya zauna sai wani tunanin ya fado masa, a take murmushin dake fuskarsa ya gushe yanayinsa ya sauya, abincin ma kasa ci yayi sai ruwan Tea kawai ya sha. Emily na fara cin abinci sai ga Fatima ta turo kofar falon ta shigo da gudu. "Momy Dady ya zo tun dazun yace na kira ki" Emily ta aje spoon din hannunta, har ta yi kamar ba zata fita ba, sai kuma ta mike tsaye ganin yadda Fatima take ta rawar jiki. Ta nufi kofar da Fatima ta bude ta fita. Turhan na zaune cikin motarsa dake bude kafarsa daya tana waje, fitowa, tun da ta fito ya daga kai yana kallon be sauke ba be kuma kyabta ba har ta iso inda yake, idan yace a cikin hayyacinsa ya fito cikin motar ya tsaya a gabanta yayi karya, domin giyar kaunarta ce ta rinjaye ta hankalinsa. "Abun bakinciki ace idan kika tashi da safe, wani ne zai yi arba da kyakkyawar fuskarki ba ni ba" Fuska babu yabo ba fallasa ta ce. "Na yi tunanin wani abu mai muhimmanci ne ya kawo ka" "Duk wani abu da ya shafe ki mai muhimmanci ne a gurina Aisha" "A yanzu ko?" Ya sauke kansa kasa yana jin nauyinta. "Har yanzu kina kallon abun da ya faru baya, kin kasa fahimtata Aisha, wasu na shirya min gadar zare wasu kuma sun gagara gane lissafina da abun da nake ji a zuciyata, ki yi hakuri dan Allah ki yafe min" "Ina tunanin mun kai karshen wannan tuntuni, na yafe maka Turhan" Ya kalleta. "Zaki yarda ki sake zama da ni?" "Aa" Ya dauke wuta na dakiku. "Na zo ne na jaddada miki cewar ina kaunarki Aisha, kuma zan tafi Sudan na san ba za ki so na tafi da Fatima, zan barta a nan saboda jindadinki, amman na zan dade ba zan dawo, kuma ina son na tafi da Fatima a yau ta ga mahaifina" "Yayi kyau, idan ka dawo idan ba wani abu ne da ya shafi Fatima ba toh ba dole sai ka zo ka gan ni ba" Yayi murmushi yana jin zafi a zuciyarsa ko kadan be yi zaton duniya zata juyo masa dayan shafinta ba, be yi tunanin zai zo yana rokon mace watan ma Aisha, sai kuma rayuwa ta kawo shi nan. A ka'ida be kamata ace yana zuwa gidan makiyinsa ba, mutumen da ya shirya masa zagon kasa kuma yayi masa gadar zare, amman yana zuwa saboda Emily. Ya bita da kallo har ta koma ciki sannan ya kurdusa ya rumgume yarsa, sannan ya kama hannunta ya saka ta mota shi ma ya shiga suka bar gidan. Ta dawo ta zauna tana cin abincin zuciyarta nata tunanin kalaman Aliyu,