Sashe 53
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Wai ke me kika dauke ni ne? A harabar gida gidan dai ba aljannu ne za su tsallako su shigo nan ba ina zan ga mata?" "Baka kallon mata amman ai akwai social media kuma wasu ma za su iya samun numberka su kiraka" "Saboda ni kadai ne namiji a duniyar nan? Kameela wai wane irin kishi ne yake damunki? Ke har alkawarin da na yi miki ba ki yarda da ni ba" Ta yi shiru. "Na san kowa da yadda Allah ya halicce shi, amman ya kamata ace muna damuwa da wasu abubuwan ba wai kishi ba a koda yaushe, already kin aure ni, ina sonki kina sona kina da kishi wannan abu ne da na sani tun kamin na aure ki kuma na aureki na miki alkawari ba zan miki kishiya ba, toh miye kuma abun daga hankali da bin diddigina?" " Mata shedanu ne wata zata iya sakawa ka karya alkawarin da ka yi min" "Akwai abubuwan da ya kamata ace mun damu da su, wata ma kokarin ganin ta samu kwanciyar hankali take, wata bata da iyaye bata da yan'uwa bata da kowa, damuwarta na samun canjin rayuwa ne, bata ta kishi take ba, be kamata muna damuwa da wasu abubuwan Kameela" "Damuwar wasu ba tamu bace, kowa ai da kalar kaddararsa, ni tawa kaddarar kishi ne da kaunarka yaushe zaka zo?" "Sai idan zaki koma zan zo na tafi da ke" "Saboda me? Yanzu baka yi marmari na ba?" "na yi idan na zo mi zan yi? Aiki nake a nan fa Kin sani, zan zo amman dole sai na dauki hutu" "Toh ka dauki hutu mana" "Okay, zan dauka shikenan" "Eh i love you" "I love you more, ki kula min da kanki" "I will sai da safe" "Okay" Ya aje wayar yana daga kansa ya kalli sama, labarin Emily halin da ta shiga kawai yake hangowa, ya kan ji labari kala kala na ban tausayi amman be taba jin kalar nata ba, be taba arba ido da ido da wata mata da ta sha wahalar rayuwa kamar ita ba. Duk kuma labarin da ta bashi na rabin wahalar da ta sha ne na rayuwar da Khaleepa, be san wane irin zama suka yi da abokinsa ba, be san ya ya riketa ba, da alama shi ma bata sha da dadi ba shiyasa har take guje masa kuma ta biyowa yarsa cewar tana da uba a raye. Ya sauka daga bayan boot din motar da yake zaune yana mamakin yadda zuciyar wasu mazan take bushewa su saka rashin tausayi a ciki har su cutar da abokiyar zamansu, ba su yarda ana hisabi ba ne ko kuma dai gani suke kamar matan ba su da hakki su kadai ne suke da hakki akan matansu? Abun takaici ne kuma abun haushi ace Khaleefa ya juya mata baya ya san wacece ita kuma ya amince ya aureta. A yadda taba shi labarinsa mutum mai addini amman ya take saninsa ya rufe ido ya zalinci wanda bata da kowa sai shi. Bata da uwa ba uba sai shi ko da yake har a yanzu a cikin wahala take a ganinsa saboda Vito ya mata duka a gabansa ranar da yaje gidan, shi ma yayi mata hakan ne saboda ya san bata da kowa. Ya tabbatar da ace tana da iyaye a raye wannan kangi da wahalar rayuwar da cin zafin ba za a yi mata shi ba. "Rashin iyaye masifa ne" Yana maganar yana danna kiran mahaifinsa bayan sun gaisa ya nemi ya ba shi Ummi ita ma suka gaisa sannan yayi musu sallama ya kashe wayar. Ya gwada kiran number Emily har sau biyu ya ji ta a kashe sai ya ji duk ya damu ya san halin da take ciki domin ya aje ta gidanta a dazu a wani yanayi marar dadi, yanzu kuma ya ji wayarta a kashe, waya sani ko mutumen dake nuna mata fin karfi ya ga lokacin da aja aje ta a dazun ko kuma wani ya fada masa, waya sani ko ma ya mata duka akan haka saboda kowa ya maida ita baiwa saboda bata da gata. Gashi ya tuna mata da baya ya san yanzu damuwar zata mata yawa, a yanzu ya gamsu da hujjarta na son gina rayuwarta ita kadai da take ba tare da neman taimakon kowa ba. "Idan kin ga wannan sakon ki kira ni, ina son na san halin da kike ciki" Ya aika mata sakon yana jin zafin yadda suka cutar da ita har cutarwa ta yi nasarar sauya tunaninta akan musulunci da musulmai. Ya dan jima a tsaye a waje, labarin da ta ba shi kawai yake ta hararowa yadda ta yi zaman. Sai kuma ya ji ya kagu ya ji irin zaman da ta yi da Turhan yadda ta hadu da Vito kuma taya halittar jikinta ta canja zuwa siririya bayan Turhan ya fada masa tana da jiki sosai a labarin da ta bashi a yanzu kuma ta fada masa ta yi rama sosai a gidan Khaleefa saboda wahalar data sha. Ya bude motarsa ya zauna a ciki yana kai dubansa gurin agogon da ta aje masa dazun a office. Ya kai hannu ya dauko agogon yana ta juya shi a hannunsa. "Kai wasu mazan akwai bakar zuciya" Ya fada yana mamakin yadda wani zai aikata abun da shi ba zai iya kusantar makamancinsa ba me balle ya aikata. "Waya sani shi ma ko yana can yana nemanta" Ya ayyana da nufin Khaleefa a ransa kuma yana jin haushin Turhan tun gabanin ya san wane irin zama suka yi. EMILY POV. Ya aje wayar a hankali kusa da ita bayan ya kashe wayar gaba daya. Ya zauna kusa da Emily da bata iya daga ido saboda kukan da ta sha idon ya rufe mata sai ciwo yake. "Za a maida shi mutuware su aje shi a can kamin ki samu salama a shirya bikin mutuwarsa" "London Musulmi ne, musulmi na haife shi please ka bari a birne shi a makamartar Musulmi, ina jin kamar ban masa adalci ba idan na masa haka, ban bashi kulawa data dace ba, da ace na san zai mutu da na zauna da shi a kowane second da minute" Vito ya rumgume ta. "Ai kin bashi kulawa, shi ne yake kyamarki ba laifinki ba ne" "Amman ai shi ba shi da lafiya ya kamata na masa uzuri" "Baki da laifi a gurin kowa Emily, lokaci yayi da ya kamata ke ma ki so kanki ki dagawa kanki kafa ki yi ma kanki uzuri, kin bashi rayuwa mai kyau ki tuna shi ya rayu da uwa da yar'uwa hakan ma abun farinciki ne a gareki" Ta daga kanta daga jikinsa ta kalleshi duk da kasancewar bata iya bude kwayar idon. "Na gode Vito na gode daka taimaka min gurin bashi gata da rayuwa mai kyau, na gode da baka taba gajiyawa da shi ko maganinsa ba, baka taba kyamarsa ba" Ya maida ita kirjinsa. "Ba zan taba kyamar abun da ya fito daga jikinki ba" Ya shafa bayanta a hankali alamar rarrashi. _______________________ Slowly slowly VITO is my favorite Team VITO iya wuya [5/10, 7:12 PM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL ABOKIN RAYUWA