Sashe 117
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ya mu'amalance ni kamar yadda ka yi ma Aisha" A take murmushin dake fuskar Turhan ya gushe. "Ta inda ya dara ka, shi be gabatar da ni a matsayin baiwa ba a gidansa, na shiga a matsayin mata, amman boye ni yake bana fita idan yayi baki saboda kar a gan ni, matansa duka biyu basa bukatar ganina dan haka ban isa na chudanya da su ba, shi kansa auren ya zamo masa dole ne kawai a haka yake zaune da ni, da aka samu cikinka sai ya ji tsoro kar na fara yin zuri'a da shi alhalin baya bukatar wani jinsa a cikin familynsa sai nasa, be yarda na shayar da kaiwa, ina haihuwarka aka karbe aka bawa wata balaraba ita take shayar da kai take maka hidima, da ya ga baka yi kama da ni ba har dadi ya ji, shiyasa bayan na haife ka sai aka hada kai da hadimata aka ba ni maganin hana haihuwa na sha ba tare da na sani ba, da maganin ya zauna a cikina sai ya haifar min da rashin lafiya, a dole yake bani kulawa saboda kar na fadawa mahaifin ya wufintar da kyautar da yayi masa, sai da ya ji ya gani da wahala da ni sai wata rana ya saka na shirya masa abinci, ban san ya aka yi ba amman dai bayan ya ci abinci ya kamu da ciwon ciki aka je asibiti suka tabbatar guba ce, abun da har na kasa ganewa shi ne shi ya saka gubar da kansa ko kuma hada baki yayi da likitan saboda ya fadi hakan? Daga gidan sarauta aka wuce da ni gidan yari wai ina son kashe sarki, mahaifina ya shiga ya fita ya samu daker aka fitar da ni, a wacan lokacin sun yi nufin kashe ni saboda su share labarina. Da aka dawo da ni kasar nan sai ya aiko da min da takardar da saki, wannan maganin da aka ba ni ya zama sanadin da ban samu lafiya ba sai da aka yi min aiki aka cire min mahaifa gaba daya" Ammy tana labarin tana zubar da hawaye, ta kalli Turhan. "Kasan me yasa na fada maka duk wannan?" Ya girgiza kai alamar a a jiki a mace ido na zubda hawaye. "Saboda na fahimci na yi kuskure na hada aurenka da Aisha, balaraben asali be son bakar fata, balaraben mutum yana da dagawa, ina tuna yadda na yi ta yaki na yi ta fadi ta shi na ganin hankalin mahaifinka ya dawo gareni amman hakan be samu ba, indai akan auratayya ne balarabe be taba karbar bakar fata. Gaba daya sun ture karantarwa da koyarwa Ma'aiki da yace wani be fi wani ba sai wanda ya fi jin tsoron Allah" Ya share hawayensa. "Ammy me ya kawo wannan maganar?" "A yanzu da na fada maka ka ji dadin abun da mahaifinka yayi min?" Ya girgiza kai. "Taya kake tunanin Fatima zata ji? Ya zaka ji idan wani yayi ma yarka haka? Da ace ba mahaifinka ne ya aikata min haka ba me zaka yi?" "Ba zan bar shi da rai ba?" Ammy ta daka masa tsawa hawaye na sauko mata. "To kai ba zuciya ce a kirjinka ba? Me yasa baka ji haka lokacin da kake cutatawa amanar da na baka ba? Aisha nan uwar wasu ce ai gashi nan ta haifa maka a, yar wasu ce ita ma yar adam ce idan aka munana mata tana jin zafi kamar yadda zaka ji" "Ban san... San... Iya abun da ta fada miki ba, amman Wallahi ban taba dukanta ba, kuma ba a taba dukanta na kyale ba, ban tana hana mata abinci ba, a lokacin da kika aura min ita na yi kuskuren na kin karbarta ne saboda ina tsoron yadda zan gabatar da ita a matsayin mata a masarautar Mahaifina ba lallai ya karbeta ba, matata ma haka kuma wacan lokacin ina jin kamar darajarta bata kai ba, amman yanzu duk na gane kuskuren hakan" "Ta fada min irin zaman da kuka yi, kuma ta fada min a yanzu saki take so" Turhan ya ji zuciyarsa ta buga da karfi ransa ya bace sosai. "Idan tana son saki zata iya fadar tana son saki ba sai ta saka kin tuna da abun da be kamata ki tuna da shi ba" "Ni na hada auren yanzu kuma zan raba, ka rubuta takardarta ka ba ni zan kai mata" "Zan sake ta, amman ba zan bata Fatima ba" "Tsakanin kai da yarka babu ruwana a ciki, amman tsakanin kai da ita ni na hada yanzu kuma zan raba" Ya hade rai sosai ya tashi ya haura sama gurin da yarsa take. Ammy ta dade zaune a gurin zuciyarta na mata turkuki sannan ta tashi ta shiga dakin, a daren kwana ta yi da bakinciki tuna baya da kuma bakinciki abubuwan da suke faruwa a yanzu. Turhan kuma ya kwana tare da yarsa da tunanin abubuwan da yayi Emily, motsi kadan idan Fatima ta yi sai ya farka domin a kirjinsa ta kwana har safe. Washe gari suka hadu gurin karyawa, Ammy ta juye halshe ta gudun kar Fatima ta fahimci me suke magana akai, da yaren Larabcin Sudan ta ce. "Idan ka rubuta takadar ka ba ni da kaina zan tafi na kai mata" Ya tsayar da cin abinci da yake ya kalli Ammy da babu fuskar wasa a maganarta ya ce. "Da gaske kike yi Ammy? Wai da gaske kike na saki AISHA?" "Na taba maka wasa a irin wannan gabar? Alkawari ma daukar mata kuma zan cika" Ya kasa hade abincin dake bakinsa sai dawowa yayi da shi ya zuba a plate din. "So nasty" Fatima ta fada tana daukar plate dinta ta bar dinning din sai yamutsa fuska take saboda ta yi arba da kazanta. Be kula ta ba sai kallon Ammy yake. "Idan har zan sake ta to miye amfanin nemanta da aka yi ta yi? Kin ce na gyara abun da na bata idan na rabu da ita ta ina zan gyara abun da na bata? And Fatima za a raba mata hankali, bana son ta yi irin rayuwar da na yi" "Daman ai ba sonta kake ba ka fada min, nemanta kuma ya maka rana tun da ka samu Fatima, daman ni burina a nemi yafiyarta kuma asan halin da take ciki, ita ma kuma ba sonka take ba" "Na ji ita tana da hujjar da zata ki ni, ban damu ba idan tana sona ko akasin haka, amman ni nace bana sonta wannan a baya ne, kuma na fada ne kawai saboda ta ji haushi ke ma kuma ki kyale ni, amman yanzu ne lokacin da zan gyara komai, taya kuma zaki ce na sake ta? A yanzu babu wanda nake son farantawa rai kamar ita, Fatima da ke" "Idan kana son faranta mata to ka sake ta mana, bata bukatarka a rayuwarta" "Ni ina bukatarta, idan na sake ta ai ban gyara lafina ba, na kara batawa kenan, kawai ranki ne a bace Ammy amman ni ba zan saki Aisha ba noooooo" "Ka sake ta idan kana sonta kuma ka yi nufin gyara laifinka zaka gyara ko baka tare da ita, ka sake ta sai ka sake bibiyarta idan zuciyarta ta natsu ta yafe maka zata iya amincewa ta sake aurenka" "La la la lala lalala idan na saki Aisha ba zata zabe ni, ta sake aurena ba ko da kuwa maza sun kare a duniyar nan, a yanzu ni nake bukatarka ba ita take bukatata ba, la la la Ammy laa ba zan saki Emily ba, ki can ba ni umarni na bi amman ban da wannan la Ammy laaa" Ya mike tsaye. "Kina cikin fushi zan tafi sai kin huce" Ya nufi yarsa dake zaune kasa tana cin abinci tana game sumbance ta ya hada goshinsa da nata ya lumshe ido yana jin wani irin sanyi da be tana ji ba a duniyar, sanyi rahama na arzikin samun haihuwar da yake nema ido rufe. Sai da ya sake sunbantarta sannan ya mike tsaye ya juya ya kalli Ammy. "Zan yi magana da Aisha, zan dawo da ita kusa da ni, a masarautarmu za mu yi rayuwa mai kyau, idan na sake ai wani banza ne zai aureta, idan mahaifina ya jure ni ba zan jure kallonta a gidan wani ba, zamanta da Aliyu ne su suka kitsa mata komai ni kuwa sai na nuna masa ni namiji ne" "Babu wani hucewa da zan yi, wajibi ne ka sake ta wannan dole ne" Ammy ta fada tana dukan dinning din da karfi. Turhan be sake cewa komai ba ya haura sama ya dauki keys dinsa ya sauko ya fice daga gidan gaba daya. [7/16, 10:07 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA