Sashe 88
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
na kawo miki Fatima, daga nan ki karasa min labarina" "Zan karasa maka labarinka ta nan, zan bar maka sako a duk lokacin da ka samu dama sai ka saurara" "Idan haka kika zaba ba ni da matsala" ALIYU POV. Ya bata amsa yana mai gamsuwa da cewar data yi Vito yana zama a gidanta, da farko kam yayi tunanin ko Vito ya mata wani abun ne shiyasa take ta boyo bata son ya ganta. Yana dagowa ya kalli Fatima sai ta bata fuska. "Ni ba yanzu zan koma gida ba" Yayi murmushi shi kan shi yana jindadin zama da ita. "Momy tace abarki ki kara kwana biyu" "Yeehhhhhhhh" Ta rumgume shi sai yayi dariya. "Zamu je da ke yau, na siya miki new clothes kina so ko?" "Eh" "Okay, gobe zan yi tafiya zan tafi Kaduna kuma zan tafi da ke, amman ba zamu fadawa Momy ba sai mun dawo, wannan sirrinmu ne kin yarda?" "Yes yes yes yes....." Ta shiga tsalle da murnar zai tafi da ita. Ya yanke shawarar tafiya da ita ne ganin zata yi kwana biyu a gurinsa albashi idan ya dawo sai ya fadawa Emily cewar ya tafi da ita, tafiyar ta kwana biyu ce idan ya isa Assabar da wuri zai tafi gidansu Kameela, idan kuma hakan be samu ba zai bari sai washe gari, on Monday sai ya dawo PH. Yadda ya fada haka ya aiwatar daga Office dinsa ya wuce da Fatima shipping ya siya mata tufafi da wasu abubuwan da ya san zata bukata, kamar Turaren yara shoe's da kuma ribbons. Fatima ta saka jin sha'awar kasancewa uba saboda yadda yake kula da ita a dan zaman da ta yi na kwana biyu shi yake gyara mata gashi da taimaka mata gurin wanke baki. Ta dayan bangaren kuma yana tausayin rayuwarta domin ya fahimci yadda take tsananin bukatar uba a kusa da ita, sannan ya fahimci sakacin mahaifiyarta na bar masa ita a hannunsa ba tare da damuwa da wani abun zai same ta ba, ko da yake Emily ta aminta da shi ne ya saka ta bar masa Fatima hannunsa, sai dai abun da yake ganin ya kamata ta damu da shi, shi ne Fatima mace ce kuma yarinya karama kyakkyawa sosai, zata iya haduwa da wanda zai iya lalata mata rayuwa, shi kanshi Vito ba dan hankalinsa be gurin ba, da tuni yayi mata aika aika sai dai ta koma kuka da bakinciki, ta dayan bangaren kuma yana ganin kamar saboda Fatima bata da uba ne, dawainiyar ta yi ma Emily yawa ita kadai, sai dai duk da haka wannan yana daga cikin abun da yake son tattaunawa da ita akansa idan ya dawo sun hadu. Abu ne da ya sani hatsari ne Sosai tafiya da Fatima ba tare da sanin mahaifiyarta ba, alkawari daya ya daukarwa kansa duk tsanani duk rintsi ba zai taba barin Turhan ya ga Fatima ba, kuma ba zai bari Fatima ta ganshi ba, dan haka zai yi iya kar kokarinsa duk yadda zai iya wajen kare afkuwar hakan. Business class ticket ya siya saboda ya samu yin walwala shi da Fatima, yana gama sallah ya shiga Kitchen ya hada musu light breakfast sannan ya tashi Fatima ta yi sallah ta yi wanka ya ci abinci ya dawo mata rigar da zata saka ya tsaya bayanta ya gyara mata kanta sannan ya fita dakin ya shiga dayan dakin ya shirya ya, ko da ya dawo ya samu ta saka rigar ya saka turare tana gyara masa kayan kwalliyar dake gaban Madubin. "Good Girl" Ya bata hannu suka taba tana dariya sannan ya fito da suitcase karami da babba ya aje direbansa ya dauka ya saka mota. Sai da Aliyu yayi addu'ar fita ya karantawa Fatima ya biya sannan suka fito, a lokacin da suka doshi motar da za su hau yana rike da hannu Fatima sai wata zuciyar ta raya masa ya kira Emily ya fada mata zai yi tafiya na kwana biyu kuma zai tafi da Fatima mana, zai fi zame masa kwanciyar hankali, sai kuma dayar ta hana shi ta hanyar nuna masa Emily ba zata yarda da shi ba, zata yi tunanin ko yana son kai Fatima ne gurin Turhan, shi kuma baya son maida Fatima a yanzu domin yana jindadin zama da ita, ita kanta tana son haka, bayan duk wannan ma ai Emily ce da kanta ta bukaci ya bar Fatima a gurinsa na kwana biyu. Haka dai ya shiga motar yana ta sake sake, can kuma sai ya ji gabansa ya fadi, ba tare da sake wani tunani ba ya ciro wayarsa ya kira Emily 3 missed calls bata daga ba, ya yanke shawarar fada mata idan ma tace bata aminta ba sai ya maida Fatima a gurinta ai ba laifi ba ne. Ta dayan bangaren ma yana jin kamar ba daidai ba ne ace ya tafi da Fatima a garin da Mahaifinta da kakarta suke ba tare da ya barta ta gansu ba. Da be samu magana da ita ta waya ba ya duba agogon hannunsa ya kalli time sai ya juya ya kalli Fatima. "Sweetheart zamu je mu fadawa Momy zan yi tafiya dake, idan ta aminta sai mu tafi, idan kuma tace aa sai na tafi ki ki zauna" A take Fatima ta lake kafada ta fashe da kuka. "Aa ina son na tafi, Momy ba zata bari ba, zan tafi nidai ina son tafiya please" Ta shiga yi masa magiya tana kuka. "Okay zamu tafi ba sai ta sani ba" Ya amsa mata ne kawai saboda ya samu ta yi shuru domin ta fara hargitsa motar da ihunta tana shure shure da kafafuwanta. WhatsApp dinsa ya shiga sai ya tarar Emily ta aje masa voice ne mai yawa and part part, ko be tambaya baya san ba zai wuce labarin da tace zata karasa masa ta nan ba. Sai da ya aje mata nasa sakon ta whatsapp ganin bata online ya saka shi aika mata the same sako ta layin karta kwana sannan ya sake kiranta still bata daga ba kuma bata maido masa da amsa ba. Dan lokacin da ya rage masa a airport din ya karasa shi har zuwa lokacin da suka fara shiga jirgi bata maido masa da amsa ba, suna shiga jirgin ya saka wayarsa Airplane mode. Sai da suka taba hira da Fatima dake dan jin tsoro a lokacin da jirgin ya tashi, ya bata wayarsa tana game sannan ya saka airpods ya yi connecting da wayarsa, ya shiga WhatsApp dinsa ya bude chat din Emily ya fara sauraren Voices din data turo masa..... _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [6/23, 9:05 PM] : https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ABOKIN RAYUWA