Sashe 110
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
rika yawan magana" Yayi murmushi. "Ummi tana tsoron rasa dan autanta" "Autan da baya jin magana ma? Ashe har guba yarinyar nan ta saka maka amma... Dai bari ka ji sauki tukuna, sai na ci mutuncinka Wallahi Aliyu" Yayi murmushi, ita kuma ta mike tsaye ta mika masa wayar. "Cire min password din" Sai ya fada mata password dinsa sunanta ne tare da numbers, ta yi murmushinn jindadi ta fice daga dakin, sai da ta fita waje sannan ya kira Emily da wayar Aliyu. "Hello... Aliyu" Emily ta amsa da muryar kuka. "Ba shi ba ne mahaifiyarsa ce, kina ina" "Ina wajen asibitin na zo an hana ni shiga, Aliyun yana lafiya" "Daidai ta ina?" Ummi ta tambaye ta tana ina Emily ta fada, sai ta fita da kanta ta isa har gurin da Emily ta fada mata, Emily na hango Ummi ta mike tsaye gabanta na faduwa ta yi tunanin idan Ummi ta karaso gurin zata mata fada ne ko ta tuhumeta, sai da Ummi ta kawo sai ta ce. "Ke ce Emily?" Emily ta amsa ta hanyar daga mata kai a hankali cike da tsoro abubuwa biyu ta ci mutunci ko kuma ta fada mata wani abun ya sami Aliyu wanda ba shi take fata ba. Sai kawai ta ga Ummi ta rumgumeta. "Ki yi hakuri, ba a kyauta miki ba kuma hakika an zalince ke" Emily ta fashe da kuka Ummi ta dagota ta kama hannunta. "Zo muje ki ga Aliyun" Taja hannunta suka koma cikin asibitin Ummi ta shiga da ita har dakin da Aliyu yake. "Gata nan ka yi a hankali ka san dai yanayin da kake ciki da kuma abun da likita ya fada" Cewar Ummi sai kuma ta kalli Emily take share hawaye ta sake kallon Aliyu ta ce. "Kuma ka bi a hankali karka kuskura ka ce zaka fada mata wata magana marar dadi, ka san dai ta fika tarin damuwa, ba zan lamunci hakan ba" Aliyu ya kalli Ummi cikin wani irin jindadi da alfahari na furuncin da ta yi a yanzu, Emily ma ta kalleta tana mamaki da tunani. Ummi ta juya ta fita daga dakin ta rufe musu kofa. Sai shiru ya biyo baya Aliyu ya kasa kallonta ita ma ta kasa kallonsa sai jan majina take tana yawo da ido. A lokacin da ta yi jihadin dagowa ta kalleshi a lokacin ne shi ma sarkin ya fada masa ya kamata yayi nasa jihadin. "How are you Aliyu" "How are you Emily" Suka hada ido da baki gurin tambayar junansu ya kowanensu yake, shi ya damu ya san halin da take ciki a yanzu bayan rabuwa da yarta da kuma abubuwan da suka faru, ita ma kuma ta damu ta san ya yake ji a jikinsa na abun da ya same shi domin ta ga bandage a kansa da kafarsa da jikin ya nuna alamar duka ta ko'ina. Shi ya fara sauke idonsa daga barin kallonta yana jefar da tambayar da amsar ta yi masa nauyi gurin dauka. "Har yanzu akwai igiyar auren Turhan akanki? Da igiyar aurensa kika gudu?" "Ba shi da amfani, na rika na sake shi, ba ni da wata alaka da shi yanzu" Yayi murmushi ya koma ya jingina da ginin dake jikin gadonsa ya rufe ido. Ba shi da dalilin rashin jindadi amsarta, dan haka ba zai ayyana abun da ya ji a yanzu a matsayin rashin jindadi ba, sai dan tausayin rayuwarta da kuma na yarta, ko da yake yadda Turhan yake neman haihuwa yasan ba zai cutar da Fatima ba, ita ma kuma yadda Ammy ta juya masa baya ba zai yarda ya aikata abun da zai saka ya sake rasa Emily ba. "Kin manta baki fada min wannan ba a cikin labarinki" Ya fada bayan ya bude idonsa. "Ba shi da amfani, na riga na sake shi" Yayi murmushi mai nauyi. "A musulunci mace bata sakin kanta, ke matarsa ce har yanzu" "Ni ba musulma bace a yanzu, kuma a addininmu mace sakin namiji idan bata ra'ayi" "Ai amman idan ta yi signing papers ko? Ke baki yi ko daya ba" "Saboda ba a coci aka daura mana aure ba ko kotu" "Shiyasa kike matarsa har yanzu" "Duk tsawon lokacin nan? Duk bayan abun da yayi min?" "It does not matter ke kika gudu ba shi ya barki ba, Emily you're still his wife" Ta matsa kusa da shi ciki bacin rai. "I hate you for telling me that" "I know" Ya amsa mata, ta nuna idanuwanta. "Na yi bakinciki wannan hawayen da na zubar saboda kai, hankali ya tashi saboda abun da ya same ka yanzu ka farka kana fada min I'm still Turhan wife, i hate you Aliyu... I hate you... I hate you... I hate you... So much" Ta furta da karfi ba tare data daga murya ba, sai yayi murmushi mai sauti. "i hate myself more, what else?" "Na tsane ka da ka kasance abokin Turhan" Ta juya zata fice sai ya ce. "Idan kika fita baza su bari ki sake shigowa ba, and we need to talk akan gurin da zaki zauna da kuma Fatima" Sai ta juyo kawai ta fashe masa da kuka ta zube a gurin zaune, komawa yayi ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. [7/10, 1:55 PM] : https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ABOKIN RAYUWA