Sashe 44
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 2 Mun sauka garin Rizaga (Sunan garin kirkiren ne) Da dare sosai kusan sawun mutane da yawa ya dauke. Daga tashar garin ya dora ni a babur shi ma ya hau daya muka kama hanyar gidansu, tafiya muka yi mai nisa sannan muka isa. Da duk inda muka bi muna ganin mazan garin kwance wasu a bakin kofafin gidajensu wasu kuma a fili. Bayan mun sauka ya biya mai achaban su biyu sannan ya nufi kofar gidan data kasance katuwa da aka yi da gambun kwano. "Su waye a nan?" Na ji an tambaya, sai Khaleefa ya nufi daya daga cikin maxan da suke kwance a wajen yace ni ne baba, mutumen ya dauko fitilarsa ya haska fuskar Khaleefa duk kuwa da kasancewar akwai hasken wutar nepa. "Lafiya? Hamza kai ne a dare haka?" "Lafiya kalau Kawu, bari na shiga ciki" Sauran mazan duk suka tashi zaune suna gaisawa da shi suna tambayar lafiya ya ce musu lafiya kalau. "Da muka a kuke tare?" Ya tamabaya bayan ya haska fuskarta. "Zuwa da safe za ku ji komai ba Kawu" Ya nufo ni muka doshi cikin gidan, Tun kamin mu shiga gidan na gama fahimtar gidansu family house ne, ashe kuwa na canka daidai da muka shiga ciki sai na bangare bangare na gidan, yana gaba ina biya har muka isa bangare da mahaifiyarsa take, tana cikin bachi ya tasheta ta zabura tana daura dankwali. "Hamza lafiya? Saukar dare? Kuma baka fada mana zaka zo ba?" "Lafiya kalau Inna, ga dai bakuwa na zo da ita a bata gurin ta kwanta, kuma idan akwai abinci a bata ta ci zuwa sa safe za mu yi magana" Ta kalleta daga sama har kasa a lokacin ina sanye da jean sai hijab din da Khaleepa ya siya min "Sannu da zuwa zo nan ki zauna" Na gaisheta ta amsa min, na karasa na zauna a inda ta nuna min zuciyata cike da tsoron abun da na aikata da kuma wanda zan tarar. Tuwon gero aka kawo min da miyar kuka, luma daya na yi na gagara ci domin ban san miye tuwon gero ba a lokacin, miyar kukar ma ban taba jin sunanta ba sai a ranar. Haka na kwana da yunwa, washe gari tun da asuba na ji garin ya karade da kiran sallah, Wallahi idan na ce ban jidadin sautin da na ji ba na yi karya, natsuwa ta sauko min, sai na ji kamar ina cikin wata duniyar ta dabam... A daki aka maida min shimfidar su kuma suka yi sallah a ciki, tun da na shiga bachi mai nauyi yayi gaba da ni, ban farka ba sai karfe tara na safe, ban sani ba ashe Khaleefa yana nan yana rigima da iyayensa akan cewar ba zai maida ni domin shi a yanzu tsoron komawa garin Lagos yake, kuma ni na yarda na biyo shi ba cilasta ni yayi ba. Suka kira ni aka tsare ni a gaban manyansa suka tambaye ni, da amincewata ya taho da ni na fada musu cewar eh ni na mince masa na ce masa mu gudu domin iyayen dake rikona ba za su bar ni na aure shi ba, kasancewar shi musulmi ne, suka sake tambayata shin zaki musulunta ki auri danmu? Na amsa musu a take cewar eh zan musulunta. Sai suka yi farinciki suka nuna jindadinsu musamman mazan, amman mahaifiyarsa kamar bata yaba da hakan ba. Da yamma aka aiko mai gari yana neman yarinyar da aka zo da ita da kuma Khaleefa. Muka tafi har da iyayensa irin bayani na yi a nan shi na yi a can shi kuma haka, mai garin ya gamsu yace gobe idan Allah ya kaimu za a kai ni gurin limamin garin na musulunta kuma a daura mana aure, suna tambaye ni wane suna kike so nace musu Aisha Muhammad, haka nake son sunana ya zama. A lokacin farinciki ne kamar ragagge ne, sai ya zama ban ji wani dauki na auren ba sosai ba, wata kila kuma ishara ake min cewar babu alheri a ciki. Yadda mai garin ya fada haka aka aiwatar washe gari aka kai ni gurin wani limani na musulunta kuma suka daura mana aure, kusan kowa zuwa yake kallona har sai an boye ni, abubuwa biyu ke kawo su, jin cewar ni ba musulma bace da kuma yanayin hallitata. A dakin mahaifiyarsa na fara zama kamin ya gina mana karamin dakin da zamu zauna a tare a bangaren mahaifiyarsa, ya siya mana katifa da zanen gado da dan abubuwan bukata na aikin gida domin ni ba ni da kowa kuma bani da kudin siya. Sannnu sannu ya fara koya min sallah karatun sallah da wasu gajerun addu'o'i kasancewata mai saurin gane abu sai na fara fahimtar yadda zan yi ibada ta. Kusan a lokacin bani da wata matsala kamar yadda idan na gaishe da mahaifiyarsa take amsa min kamar dole, ga kuma rashin iya girki, ya siya min gawayi da murhun gawayi ina girki da shi, akan girka shimkafa ko taliya, ko indomie na girka chabewa take saboda ban taba girki ba, shi kuma yana da saurin fushi, ko kirana yayi na dade ban amsa ba ko ban zo ba sai ya fusata, ya fara fushi da ni, ko gaba, idan ya fara gaba da ni sai ga na zama kamar marainiya yake kula ni, domin ba ni da kowa a garin, gashi mutanen gidan sun ki su saba da ni, ni ma naki sakewa da su, kullum ina ciki daki. Abun da na fahimta bayan aurenmu shi ne Khaleefa yana da farin jinin yan matan garin, shi ka kansa ya fada min kuma kanwarsa da ke dan leko ni muna taba hira wani sa'in ta fada min. Ban kuma yi mamaki ba domin yana da kyau ni kaina kyaun ne ya dauki hankalina a lokacin, gashi ya iya wanka idan ya shirya ba zaka taba yarda a kauye yake zaune ba, su kan shigo gani na wasu wasu kuma idan na fita tsakar gidan nake ganinsu ko su gan ni. Akwana a tashi dan abun da Khaleepa yake da shi ya kare domin ciki muke ci, ga mahaifiyarsa ko gishiri ya siyo min sai ta karba ta raba biyu ta bani rabi, taliya ma idan daya ce to rabi zamu aje mu bata rabi. Da kudinsa suka kare sai ya rika karbo mana abincin da suke, da safe kunu ko dumame, da rana kuma sai dai ayi kwado ko kuma asiyo abunci na siyarwa a ciki da dare kuma tuwon gero. Bana iya cin tuwon kunun ma kadan nake sha domin babu suga, da rana kuma sai na wuni da yunwa, na ga alamar yunwa zata halaka ni idan aka ba ni tuwon geron sai na dukula na hada da ruwa na rika hadewa ba sai na saka miya ba. Washe garin ranar Inna da kanta ta sallama min na fito ta ba ni tabarya wai ai da ni ake cin abinci yanzu, ta saka ni turfe ban iya ba amman haka na rika yi ba, daker na samu yayi na kwashe mata, na dawo daki ina duba hannayena da suka yi kwancin jini suna ciwo. Sai yace "Da sannu zaki saba, mu a nan garin yawanci duk gidan da ake cin tuwon gari a gidan ake surfe, Inna ma bata yi, amman da kin lura dayan bangaren ai har na siyarwa suna yi" Ban ce masa komai ba, gudun kar na yi wata maganar ya fusata. Wasa wasa matar nan ta fara sani surfen siyarwa idan aka kawo kudin kuma sai ta karba tace za a hada a kudin cefane. Gashi haka nan nake wuni da rana babu komai a ciki, domin Khaleefa be da kudin siya min abinci yanzu, sai can wata rana idan an yi kwado ta aiko min idan na ci cikina yayi ta ciwo, da dare kuma abinci kadan nake ci haka da safe. Kan kace me na rame na lalace ba kadan ba, idanuwana suka cicciko suka fito fuskar ta koma karama, kassana suka bayyana. A lokacin ne Khaleefa ya dauki katifar dakin ya siyar mahaifiyarsa ta hada masa da wasu kudi yayi kudin mota ya tafi Nijar gurin nema, ya bar ni babu komai sai damuwa, kullum da fargabar daka nake kwana nake tashi, ga abinci bana iya cin na kirki. Sai aka fara rade r aden wai ina da kanjamau shiyasa na yarda na biyo shi. Wata rana ina cikin surfe matar da muke zaune da ita gida daya wadda take kamar matar kawunsa ce ta dube ni tace. "Aisha amman kamin Khaleefa kina da wasu samari ko?" Na yi murmushi ina gyara rigar atamfar da ta yi min yawa, daman tufafina gaba daya kala shida ne a gidan. "AA ban taba yin saurayi ba sai Khaleefa" "Ban yarda ba gaskiya yadda kike da kyaun nan haka ai sai maza sun yi ta kawo miki hari, ko da yake ance ku baku dauki wannan komai ba, ance dan miji ya yayi mu'alama da ku ba komai ba ni shiyasa sai an gwada mace ake aurenta" "Ba kowa ba, wasu dai suke yin haka" "Toh Allah yasa wannan rama taki dai ta yi yawa" Ban fahimci inda ta dosa ba dan haka ban maida hankali akan zancenta ba, na gama surfen na dauka na wanke na kawo na aje na nufi dakina. Na shimda tabarma na dora zane na kwanta, nan da nan sai bachi yayi gaba da ni, can cikin bachin na ji ana tashina kanwarsa ce wai na tashi na yi sallah, na tashi ina jin kamar na yi kuka, domin sallah na daga cikin abubuwan da suke wahalar da ni a lokacin saboda rashin sabo haka dai nake daurewa na yi. Bayan ta fice na dauki buta na zagaya bandakin, kamar ance saurara ki ji sai na ji muryar mahaifiyarsa kasancewar bandakin yana like da dakinta ne ta gafe. "Badan halin Hamza na son karya, shi gaba daya rayuwarsa ta karya ce ta son burge mutanen, ka tsallake garinku jiharku ka tsallaka har kudu kudun ma Lagos ka dauko mata, Allah kadai ya san dalilinta na biyosa, wannan ramar da take yanzu na fara tsorata da ita" Na kai hannu ma