Sashe 151
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 6 Turhan ya kalli Ammy dake sanya da Hijab tana zaune can gefe, ya dube manyan Bakin da mahaifinsa ya zo da su. Sai ya zube gaban mahaifinsa yana jin farincikinsa ya ninku marar misaltuwa. Ya kwashi gaisuwa ya sake kwasa sannan ya hannun mahaifinsa ya sumbanta ya shafa goshinsa a kai. "Ihlan beek ya far omri, sharraftna ya baba w nazalt fi b t al-mara illi hia _Maraba da zuwan mutumen da shi ne farinciki, na jidadi ganinka mahaifina na jidadin da ka sauka a gidan macen da ita ce Rayuwata._ Mahaifinsa ya yi murmushi kadan babban abokinsa da yake tare da shi ya ce. "Mun biyo sawunka na, domin mun lura idan ba mu yi haka ba na zaka gane cewar kana da muhimmanci a gurinmu ba" Ya kalli Mahaifinsa yana murmushi "Na san inda da muhimmanci tun a ranar da ka saka siya ticket aka yi min fatan sauka lafiya, soyayya ce ban tabbatar da ita ba sai a yau, ko a mafarki ban taba saka ran kafarka sata iya taka gidan nan ba, ta ina kuka samu adireshin?" "Ta hanyar Mai Martaba" Ya nuna Ammy da bata ko kallon inda suke zaune. "Gurinsa muka fara sauka, shi ya saka yi mana jagora har zuwa nan" Abokinsa mahaifinsa ne yake amsa masa mahaifinsa be ce komai ba sai hannu da ya kai ya shafa kan Turhan. "Ya labarin mata ta samu?" Sai a lokacin ya tambaya, Turhan ya rage murmushin da yake. "Har yanzu bata saurare ni ba, bata aminta zan iya kula da ita ba, bata yarda zan bata kulawa ba" "Baka fada mata an sarakuna basa karya ba?" "Bata duba komai daga sarautarmu ba, zuciyarta ta bushe da kiyayyata, ko wace gangar na buga bata ara" ar wane Sarkin ce?" "Ita din ba jinin sarauta ba ce" "Tana da tsada ne har haka? A nawa za mu siye ta?" "Kudi ba matsalarta ba ne, ko nawa za a zuba ba zai siyeta ba, amman zan jira zan biyaya har na yi nasara domin na fara ganin alamar hakan a yau" "Kar jiran wasu Iyalin ya saka ka, ata wasu Iyalin ko na manta kana da mata a gida?" "Ban manta ba, ba zan yi kuskuren aikata wani kuskuren ba, nakan kirata bata amsawa na aika mata sako babu amsa, ni kuma sai na zabi daga mata ka fa har ta huce, na maida hankalina gurin gyara abun da na bata, kuma an samu lokaci da ata" "Ina sanyin idanuwan take?" Sarkin ya tambaya da nufin Fatima. "Tana tare da mahaifiyarta, ta kan zo ta kwana biyu ta koma" Ya kama hoton Fatima ya nuna Mai Martaba a wayarsa. "Wata kila har yau baka bata damar sanin ainahin waye kai ba, baka tunanin idan muka saka baki zata amince?" Turhan yayi shiru yana nazari... "Da ace babu wanda yake zugata, babu mai saka baki, na san zata saurare ni, wani abun ba halin ta ba ne, a gidan da take zaune ne suka tsara mana komai, saboda abokina ne yana neman ya bata ni a gurinta shi kuma ya gyara kansa, wannan dalilin ya saka suka kiraka suka sanar maka saboda su bata ni a gurinka..." Ya labarta masa kadan daga abun da Aliyu yayi masa. "A ina iyayenta suke?" Turhan sai ya ki yarda da fadawa mahaifinsa asalin wacece Emily, saboda kar ya rage mata ima a idon mahaifinsa. "Mahaifinta Bature ne, nan yake zaune ba, mahaifiyarta kuma kawar Ummi ce wannan dalilin ya saka Aisha take zaune a gidansu Aliyu karkashin kulawar iyayensa" Shiru ya ratsa falon Mai Martaba be sake cewa komai ba, Turhan ma haka, ganin hakan ya saka Ammy ta mike tsaye, suka bita da kallo har ta haura sama. Mai Martaba ya kai hannunsa da kansa ya dafa kafadar Turhan. "Akwai kyakkyawan mata da yawa a jinsin larabawa, idan har matarka bata maka, akwai daga dangi na nesa da kusa, kai din mutum ne mai kima, ka yi iya yadda zaka iya ta fahimci, idan ta zabi ba zata zauna da kai ba, wannan ma shi ya fi alheri" "Matsalar ba ta neman yafiyarta ba ne kawai, ta neman soyayyarta ne" "Muna bautawa mata muna nuna musu soyayya da girmamamwa, amman balaraben mutum be yarda a wulakanta shi, be yarda mace ta taka shi, suna girmamamu muna ba su hakkinsu, karka manta kai namiji ne, kuma an sarauta, karka bari ta gano rauninta, kuma karka bari makiyinka ya gano inda zame yake a jikinka, tun da har abokinka ya shiga gabanka to ka yi kokarin ganin be illataka" Mai martaba ya mike tsaye baya ya zuba masa wannan karatun a cikin kai. "Za mu tafi, wata kika za mu dawo kamin tafiya, wata kila kuma zan tafe tare da kai ne, ta kan iya yiyuwa na tafe na jira zuwanka, ka mika gaisuwa ga mahaifiyarka" Ya fara takawa cike da kasa mutanen da suke tare da shi suka rufa masa baya, sai da suka fice sannan Turhan ya fita ya tsaya kofar falon yana kallon manyan motocin har aka wuce da su, sannan ya juya ya koma ciki jiki a sanyaye ya shiga gurin Ammy ya sameta tana waya da wata kanwarta, ya zauna har sai da ta gama. "Ban yi saton ganin Sarki a gidan nan ba" "Yana sonka mana, ba abun mamaki ba ne" Ammy ta fada. "Yayi miki wata magana kamin na zo? Ya fada ai zuwan ba nawa ba ne kadai har da duba lafiyarki" Ammy ta dan yi shiru, da halshe larabci ta maimaita masa abun da ya fada mata. "Yace sun kawo jira, kuma sun zo neman afuwa da rokon na bari dansa ya zauna tare da shi wai yana fatan ban rike shi a rai ba" Turhan yayi murmushi. "Wata kila da Mai Martaba ya shige min gaba, da Aisha ta fahimce ni, ko da yake zugata suke ba lallai ta fahimta ba" "Kai kana ganin idan Mahaifinka da kansa ya nema maka aurenta zata ce aa? Ai iyakar kyautatawa fa mun mata, ba zama lallai ta duba wannan ba, amman a matsayinta da kuma indai mutum kamar mahaifinka zai nemi aurenta zata amince mana, be kamata ace ta bar zuciyarta ta kone akan kuskure da kowa yana yi ba, wasu ma mazan sun fi haka munanawa, ni kam dai na sauke zancenta tun da ba yar gwal bace, an san an bata mata amman ba amfanin rike abu kayi ta jayayya ko dan yarinyar nan ba zata duba ba, amman ka tsaya tsayin daka kai dai a yanzu ita kake so wata kila kana tunanin kamar idan ba ita ba ba zaka sake samun haihuwa ba? Toh, Allah yasa ta zama alheri gareka kai ma ka zame mata" "Aa Ammy ba haihuwar ce kawai nake dubawa ba, ina duba rashin kyautar da na yi kuma Allah ya tashi ba ni haihu sai ya ba ni da inda ban yi zato ba, ta cancanci komai a gareni saboda mahaifiyar Fatima ce, kuma...." Yayi shiru ya sauke kansa kasa. "Ammy ina son Aisha.. Ina sonta sosai ina sonta sai a yanzu na gano haka" "Tohm Allah ya baka ita cikin sau i, ni ma ina son zamanku tare da farko, bayan abubuwan nan sun faru sai na ji ta fice min arai saboda abubuwan da ta yi kuma ta kalli tsabar idona ta fada min bata sonka, Turhan duk wanda baya sonka bana son shi Wallahi, kuma saboda Aliyu da iyayensa ina son ka maida matarka, na yi kuskure da na cilasta maka sakinta" "Wani lokacin abubuwa sukan subuce a hannunmu, ko a halshe bama iya rike su, sai dai ki taya ni da addu'a" "In Shaa Allahu, amman kasan akwai abubuwan da ya kamata mahaifinka ya sani a game da ita kuma baka fada masa ba" "Bana son na sanyaya kudurinsa ne, inda Emily tana tare da ni duk abun da zai biyo baya mai sauki ne" "Gobe zan je na yi na yi magana da ita, bana sin bata ran Mai Martaba kuma zan koma ko dan na shirya da matata, zan rika zagayowa lokaci zuwa lokaci" Ammy ta sauke numfashi kawai bata ce komai ba. EMILY POV. Bayan Mama Baraka ta wuce, Emily ta haura sama ta shiga dakinta ta zauna bakin gadon dake dakin zata kishingida kenan ta jiyo sauti karatun qur'ane a wajen Window da murya mai dadi. Mikewa ta yi tsaye ta yaye labulen ta bude Windows din sai ta hango Aliyu zaune akan beach chair Fatima na zaune akan cinyoyinta hannunsa rike da waya yana karatun kur'ane. Ba wannan ne karo na farko da ta taba jin karatun kur'ane ba, amman wannan ne karo na farko da taji kira'ar da ta yi mata dadi sosai ta tsuma jikinta ta tsara zuciyarta har ta zubar da hawaye, bata jin komai daga kalman labarancin amman jikinta da zuciyarta suna karbar sakon. Juyawa ta yi ta nufi wardrobe dinta ta dauko karamin mayafi ta rufe kanta fito dakin ta sauko kasa kuma sai ta yi sa'a babu kowa a falo, ta bude kofar ta fita ta zagaye ta kofar garden, cikin san a ta bude kofar saboda kar ta yi kara, ta shiga tana takawa a hankali ta kusa isa inda yake sai ta zauna a kasa tana kallon bayansa domin ya bawa kofar shigowa baya ne. Tagumi ta yi da hannayenta biyu tana kallonsa, hawaye take irin hawayen da suka sha banban da wadanda ta saba yi, wata kila saboda Aliyu ne yake karanta ya saka ta ji dabam, wata kila kuma a yanzu sakon yake son isa ga gabobin jikinta. Sai da ya gama karatun ya kashe wayar sannan ya sauke Fatima daga kan kafafuwansa ya mike tsaye ya rike hannunta. "Muje ciki" Ya juyo tare da ita, arba da Emily zaune a kasa ga fuskarta da hawaye ya daga masa hankali sosai duk kuwa da murmushin da yake gani tare da hawayen. A take ya saki hannun Fatima. "Fatima tafi ciki zan yi magana da Momy" "Miyasa take kuka" "Shi nake son na ji" Fatima ta fice gurin tana yi tana waigen Emily. Sai da ta fice sannan Aliyu ya karasa ya urkusa gaban Emily. "Lafiya? Me ya faru? Mama Baraka ta yi wani