← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 177

Sashe 16

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 7 TURHAN POV. Shikenan zan jiraka a waje Ya aje wayar ya nufi gurin da suitcase dinsa yake ya bude ya ciro wani karamin roll on ya murza a wuyan hannunsa sannan ya aje a mirror dake dakin ya sake nufar wayarsa ya dauka ya saka aljihu ya dauki key din dakin ya fice ya rufe dakin. Stairs ya bi har ya sauko daga hawa na uku zuwa na daya, kamin ya karaso kasa ransa ya gama baci domin Turhan ba mutum ne mai son motsa jiki ba sai dole, ko kadan baya son aikin wahala balle kuma wahalar ita kanta da baya hada hanya da ita. Harabar hotel din ya fito yana kallon yadda tsari da kawar babbar hotel din take daga kasa, domin sun sauka sa dare ne a jiya, gajiya bata bashi dama kamar yadda hutu ya bashi a yau da safe ya kalli ko'ina ba. Kusa da wata flower ya tsaya yana kallon ko'ina da kyau, kyam idonsa suka sauka akan wata hallita mai ban tsoro, mutum ne irinsa namiji mai kirar mazaje da jarumtaka, Turhan ya dauke idonsa daga kallon mutumen da shi ma kallonsa yake babu kyabta ido. Ganin sarkar Cross a wuyan mutumen da murdaddiya fuska irin na wanda baya sha'awar dariya, ya saka shi fahimtar addininshi da nasa akwai banbanci, tattoo jikinsa ma ya sanar da hakan. Feeling awkward ya saka shi ciro wayar dake aljihunsa ya fara dannawa, ya dauki lokaci a haka kamin ya sake dagowa ya kalli harabar, a karo na biyu ya sake kallon gurin da mutumen dazun yake tsaye yana kallonsa and wannan karon ma yana tsaye and still kallonsa yake har yanzu, irin kallon nan mai daure kai ga wanda ake yi ma shi, da mace ce take kallonsa sai yace ko tana sonsa ne, amman namiji kamar wannan da zai yi wahala su hada hanya da imani abun tambaya ne a kallon da yake masa, zuciyarsa ta raya masa wata kila yayi masa kama da wani ne da ya sani ne, idan ba haka ba kallon da yake masa yayi yawa, and babu wani dalili da zai saka yayi ta kallonsa haka. Kallo ne mai rikitarwa da mamaki ga wanda ake yi ma shi, hakan ya saka Turhan jin babu dadi kuma ya dan tsorata, ganin ba garinsu ba ne, haka kuma ba gurin da ya saba mutanen ba ne, ko be taba zuwa ba, ya kan ji ana fadar bad side na Lagos, dan haka dole ne yayi taka tsantsan. Takawa ya fara yi cike da izza da takamar da suke zame masa jini ya isa gate din hotel din hannayensa rumgume a bayansa sai kamshi yake zubawa tafiyarma ita kanta ta karbe shi kana ganinsa kasan babban mutum ne kuma dan babban gida. Sai da ya fice daga katon gate din dake bude sannan ya juyo kadan ya kalli mutumen dazun domin jikinsa ya ba shi har lokacin yana kallonsa, ga mamakinsa sai ya ga mutunen yana kallonsa har yanxu, kusan kallon yanxu yafi muni fiye da na dazun, domin a yanzu yana iya hango tsana da harzuka a idanuwan mutumen da be san waye ba, be kuma san dalilin haka ba. Wannan karon Turhan be tsaya shawarta zuciyarsa ya daga wayarsa ya kira Faruk. Wai baka karaso ba har yanzu? I'm not safe here fa, ina jin tsoron irin mutanen da suke a nan gaskiya Gani isowa ranka ya dade, na kusa karasowa, ka kwanta da hankalinka babu komai In Shaa Allahu, Hotel din da ka sauka hotel ce mai tsaro sosai, ba wani matsala In Shaa Allahu, da akwai matsala ai oga Aliyu ba zai bari na sauke ka a wannan hotel din ba Ina fatan haka Ya fada sannan ya sauke wayar tare da jan dogon numfashi, wannan karon be yarda ya sake juyawa ya kalli bayansa ba, balle ya san da wanzuwar mutunen dazun ko akasin haka, sai ya cigaba da tafiyarsa. Kamin ya sake daga wayar ya kira farar uwar data kawo shi duniya. Ringing daya biyu ta daga, daman bata ignoring call dinsa idan tana kusa da waya, tun a lokacin da suke shiri da juna da kuma yanzu da ta sauya mu'amala da shi, banbancin wacan kiran da kuma yanzu, idan ya kira bata kusa bata mayar masa da kiran, kamar yadda ba zata amsa kira da saukin kiransa ba, ba kamar can farko ba da take daukin kiransa da far'a da na jindadi kuma yake kiransa idan ta samu miss calls dinsa, a yanzu sai dai ta amsa masa duk abun da zai fada ne ba a cikin dadin rai ba. Ammy ina kwana? Lafiya Kalau Ammy na sauka Lagos jiya da dare sosai, na yi tsammanin ganin kiranki ki tambaya ko na iso lafiya Gashi ai mun yi magana yanzu, kuma da ba lafiya kake ba dole za a kira a sanar min Wani abu na rashin jindadi ya ji ya ratsa zuciyarsa, jiki a sanyaye ya furta. Haka ne, Ammy na zo nan ne neman Aisha kuma duk saboda ke ne, ba dan ke ba ba zan yi haka ba, ina fatan dacewa ki taya ni da Kalmar duk saboda ke ne, ya tsayawa Ammy a rai lallai ne ta sani danta yana son farincikinta da albarkarta haka kuma yana nuna cewar har a yanzu bana son zabin nata kawai dai zai nemi Aisha ne saboda gyara laifina ba dan tsantsar nadama da kaunarta ba. Fatan nasara Turhan Mohamed Abdo Tana fadar hakan ya aje wayar. Ta lumshe ido ta hade bakinta guri daya ta gum e tana maida numfashi a hankali. Jawahir ta rufe magazine din dake hannunta tana kallon Ammy cikin yanayi na damuwa. Ammy kina daukar abun nan da zafi ne sosai, ni da Maama dukanmu yayane a gurinki, be kamata ki yanke shawara ko ki yi wani hukunci mu saka baki ba, amman bahaushe yace mai shawara aikinsa baya baci, sai dai ba shi da sirri, kuma mai shawara ba ya nadama, amman na san ranki ya bace sosai akan Yaya Turhan amman ya kamata ki yi hakuri... Bata karasa ba Ammy ta bude idonta ta kalleta, tsoron furuci ko fadan da zai fito a bakin Ammy ya saka ta yanke maganar da bata karasa ba. Ammy ya gyara zamanta da kyau tana kallon Jawahir. Jawahir mahaifinki ya taba baki labarin cewar bayan haihuwar Turhan ban sake haihuwar kowa ba? It take her 5 seconds to answer. Ammy abu ne da kowa ya sani a familynmu bayan Turhan baki sake haihuwa ba Amman ya taba fada dalilin da ya saka bayan Turhan ban sake haibuwar kowa ba? Aa be taba fada mana ba, Abba baya zama yayi hira da mu yadda kike yi Ammy Ammy ta yi shiru tare da dora hannunta daya akan daya. Dauke breakfast din nan Baki ci komai ba Ammy Ammy ta daga mata kai, Jawahir ya tashi tsaye da dauke breakfast din ya fice, Ammy ta mike tsaye ta nufi karfen dake balcony din ta tsaya yana kallon harabar gidan. Ammy na jin lokacin da Jawahir ta bude kofar falon ta fito balcony din da Ammy ta fi yawan zama musamman da safe idan zata karya ko kuma da yamma. Mahaifinku ya taba fada muku cewar na zauna a gidan kaso? Mamaki ya cika fuskar Jawahir. Gidan kaso kuma? Yari fa kenan Ammy Ammy ta daga mata kai ba tare da ta juyo ba. A zamanin da na yi yan matancin, a cikin yayan sarakuna musamman na yankin arewa bana jin anyi wata yar sarki mai farinjini irina, ba nufin sarautar gidanmu ko kudin mahaifina ba, ina maganin farin jini ne wata baiwa da Allah ke hallita bawa da ita Ammy ta juyo tana murmushi ta kalli Jawahir dake tsaye. Ba ni da kyau sosai, haka kuma ni dan ba za a kalleni ace min mummuna ba, kamar yadda ni ba fara ba amman ba fi fararen matan kyau da shiga zuciyar maza, bana zama a guri na tashi wani be so ni ba, na yi farinjini sosai, yayan manyan mutane da manyan mutane sa kansu sun nuna sha'awar kulla danganta da mahaifina ta hanyar aurena, a lokacin da ace za a titsi ni na fitar da wanda nake so ba zan iya ba, domin hankalina ba a kan soyayya yake ba, kuma dukan masu neman aurena suna kyautata min yadda ya kamata na so su, mahaifina kuma yana alfahari hakan Ta nufi kujerar data tashi ta zauna Jawahir ma ta zauna a kujerarta tana kallon Ammy fuskarta fal da mamaki. Wata rana mahaifina ya karbi babban abokinsa kuma babban sarki garin Khartoum, masarautarmu ta san da zuwan sarkin kusan kasar ma ta san da haka, domin ya gana da shugaban kasar wacan lokaci kamin ya iso masarautarmu, bayan tafiyarsa mahaifina ya shigo cikin masarauta ya saka aka kira ni, na zauna a gabansa kaina na kasa ya sanarmin cewar ya kyautar da ni aure a gurin dan Sarkin Khartoum, a wacan zamanin idan iyaye suka yanke shawara ba a musawa ko da a gurin bayi ne balle kuma yayan sarakuna, wacan lokacin yayan sarakuna basa aure sai yayan sarakuna yan'uwansu, na amsa masa babu musu, a lokacin ba zan iya amsa cewar ina son kyautar da mahaifina yayi min ko akasin haka ba, iyakar abun da zan iya shaida an aurar da ni ga mutanen da ba su san darajar dan'adan ba, mahaifina ya kulla alakar ne saboda ya karfafa zumuncinsu, kuma yayi bugun kirji cewar Balarabe ya auri yarsa Maryam ta yi farinjini, sai dai mahaifina ya manta cewar balaraben Asali baya son kowa sai balarabe dan'uwa, kadan ne suke son wani yaren, sai dai ko kadan basan son bakar fata, kuma basa son girmama ra'ayinsa, basa kallonsa da kima, balaraben mutum baya son bakar fata ko kadan, da fari sun nuna kamar za su janye, domin mijin da aka ba shi kyautata be shirya karin wani auren ba bayan wanda yake da shi da farko, ban san miya ja ra'ayinsa ba, sai kuma ya amince Ammy ta share hawayen da ya sauko mata. Daga lokacin da aka daura min aure, aka dauke ni akai kai a masarautar, sai na fara fuskantar kalubale, tun
Chapter 16 · 0% Book details