← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 177

Sashe 122

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 5 Sai da Emily ta fice daga gidan sannan Ammy ta saki hannunsa, ta juya ta nufi stairs ranta a bace zuciya kuma ta yi mata nauyi, bata yi zaton abubuwa za zo a haka, ko ba komai kyautatarwa da ta yi ma Emily bata cancani yi mata hakan ba, and ba ita kadai ce mace da za'ace an fara sakawa a damuwar a namiji ba, balle ace ita ce ta karshe, mata da yawa an yi musu abun da ya fi nata ciwo da kuna wasu ma sukan yafe tun gabannin a nemi yafiyar balle ita da har an jefa kai a kasa saboda ita, ga kuma yarinya me yasa ba zata kalli wannan ba? Ai ta san yadda rashin uba yake da ciwo me zasa ba zata yi ma yarta fatan rayuwa a karkashin inuwar uba ba? Ta zauna bakin gado, wani bangare na zuciyarta yana raya mata wata kila ba laifin Emily ba ne, domin gaba daya wannan ba rayuwarta ba ce, ba mamaki zugata aka yi, indai har zata iya amincewa ta auri Turhan saboda Ammy to taya zata iya kallon idonta ta fada mata magana kuma ta tsaya tsayin daka a cikin gidanta akan lallai sai Turhan ya sake ta, idan an ciza ai hurawa ake, ta san danta be kyauta ba, amman a yanzu yayi nadama, kuma idan danta be yi daidai ba me yasa ita zata saka ta a ciki? "Lallai makashinka yana tare da kai" Ta furta tana jinjina kai, Aliyu da Ummi take hararowa, ba iya alakarta da Ummi ba, daman gaisuwa ai ba sosai suke ba, amman Aliyu da Turhan abokai ne be kamata Aliyu yayi ma Turhan haka ba, ko dan abotarsu da kuma ganin idonta, ta yarda da zancen Emily cewar ta roke shi kar ya fada saboda bata son suna san rana raye, amman bata gamsu wannan ce kadai hujjar da Aliyu zai rike ya ki fadawa Turhan inda Emily take ba bayan kuma ya san har da ya a tsakaninsu, wannan rashin kunyar da da dagiyar ma saka mata su aka yi akai ba nata ba ne. Sai dai dalilin da zai saka Aliyu ya aikata hakan ne bata gano ba har yanzu, sonta yake mana, daman can Emily tana da kyau balle kuma yanzu, amman abun kunya ne ace Ummi ta goya masa baya, idan ba haka ba ai matarsada ba zata yi kishi ba. Ta dago ta kalli kofar dakin Fatima ta turo ta shigo tana rike da teddy. "Dadyna ya ce na shigo zai tafi ya dawo, yace na zo gurinki" Ammy ta yi murmushi ta bude mata hannayenta, Fatima ta tafi ta shiga jikinta, Ammy ta rungume ta sosai tana sauke ajiyar zuciya har tana jin kanta na ciwo, burinta ta yi zuriya ta samu rayuwa mai kyau ta gurin danta domin ita tata rayuwar ta lalace, amman hakan ya gagara. "Ina son ki sosai Fatima, ina son ki saka wannan a ranki, ni da Mahaifin ki muna matukar kaunarki" Fatima ta dago ta kalleta. "Ke ce kika haifi Daddyna?" Ammy ta daga mata kai. "Kin san waya haifi Momy na?" Ammy ta girgiza kai. Sai ta maida kanta ta kwanta jikin Ammy. Ammy ta sauke numfashi a hankali, tana kallon kofar dakin zuciyarta na raya mata Turhan ya bi bayan Emily ne. "Ina son Dadyna, ba zan bi Momy ba ba zan tafi gurin Vito ba, i hate him" Fatima ta fada ta daga kai ta kalli Ammy. "Momy zata zauna a nan ai ko?" "Haka muke fata, abun da ni da Mahaifin ki muke ta kokarin yin kenan" Ammy ta amsa mata yanayin fuskarta na sauyawa, tana mamakin Emily ta dayan bangaren kuma ta yi mamakin Aliyu, ta kara rumgume Fatima... TURHAN POV. Sai da Ammy ta yi minti talatin a dakin sannan Sauke Fatima ya nuna nata teddy dake kan kujera. "Dauki Teddy dinki, ki tafi gurin Ammy ni zan fita na dawo" Ya fada mata da hausa yana mata na kurame domin ita ba fahimtar hausa take ba, shi kuma be gwane a turancin ba, ya sumbance ta ya nuna mata kumatunsa ta sumbance shi tana jin dadi. "I love you" "I love you Too" Ta mayar masa sannan ta yi masa bye bye, tana hawa tana daga masa hannu har sai da ya fice sannan ta haura sama gaba daya rike da Teddy. Motarsa ya nufa ya bude ya shiga yayi mata key, ya bi bayan Emily, shi kansa ya san be kyautu ace ya sake ta ba, amman saboda Ammy ya aikata, sai dai sakin ba yana nufin ya barta ta cigaba da rayuwa a gidansu Aliyu ba, kattan banza suna kallon matarsa ba, gashi ba wani suturta masa jikin take ba, kuma ta tafi da fushisa yana bukatar ya same ta su tattauna mafita, domin shi kam a yanzu be hangowa kansa rayuwa babu ita ba, ko ba komai ta ba bashi abun da kudi ba sai siya ba, ita ce mace ta farko da ta maida shi uba wannan farinciki da jindadin da alfaharin ba zai taba gushewa a gurinsa ba, kuma a yanzu ya shirya gabatar da ita a gaban kowa, gashi ma har mahaifinsa ya sani which be san ta iya ya ji haka ba... He can risk anything to be with Emily yanzu kam, abubuwan daya bata sai ya gyarasu sannan hankalinsa zai kwanta, idan ya gabatar da ita a matsayin baiwa a yanzu yana son ya gabatar da ita masarautar a matsayin mace mai tsada kuma mai cikakke ikon a gurinsa, domin Emily ta gama masa komai a yanzu, ta haifa masa ya, kuma ita ce macen da mahaifiyarsa take so. Farat daya tunanin abubuwan da yayi mata suka fado masa a rai sai ya rasa ina zai saka kansa, yana tunkin yana kawar da da wasu wata zuciyar na ba shi shawarar yadda zai gyara wasu. Ya karasa gidan Aliyu sai da ya tsaya a gurin gate din sannan ya tuna Aliyu ma ai baya nan kuma Ammy ta fada masa a gidansu Aliyu ta samu Emily, a take ya juya Motarsa ya dauki hanyar gidansu Ummi daman babu wani tazara sosai. "Kina takurawa kanki ne kawai Aisha, duk wani abun da za su fada miki ko su nuna miki na karya ne, hakika ba ki dace da kowa sai ni" Ya fada yana tuka motar, ko kadan be so sakinta sai dan babu yadda zai yi ne, wani nauyi yake ji a kansa kamar shi aka saka ba wai shi yayi sakin ba. Daf da zai karasa gidan wayarsa ta yi kara alamar kira, ya duba sai ya sake arba da number mahaifinsa a nan ma sai da ya faka sannan ya amsa wayar ba tare da ya kashe motar ba. "Hello Abie" "Ka bar duk abun da kake ka dawo gobe ina nemanka" Ya fada masa da larabci kamin ya amsa masa ya kashe wayar. Turhan ya kifa kansa da sitarin motar ya cije baki, yana jin bakin cikin yadda aka yi mahaifinsa ya sani ma, waya fada masa me yasa aka fada masa a yanzu, yana da shirin gabatar ma mahaifinsa da komai amman ba a irin wannan yanayin ba, yayi nufin sai idan abubuwa sun gyaru shi da Emily ga kuma yarsa. Yanzu be isa ya ki tafiyar ba, alhalin kuma be shirya mata ba, domin a yanzu baya son abun da zai saka shi yin nisa da Emily. Ya dago cikin damuwa ya cigaba da tukin har ya isa bakin gate din gidan yayi horn mai gadin ya tambaya ya fada masa ciki zai shiga gurin Ummi sai ya bude masa gate, Turhan ya shiga ya faka harabar gidan ya fito yana wani shan kamshi ya doshi Entrance din da Ummi take tsaye tare da wata mata da be san waye ba sai rusar kuka take. Da takunsa na kasaita ya karasa gurin ya tsaya, sallama ce kawai ya gagara yi amman ya gabatar ma da Ummi gaisuwa domin har lokacin safiya ce. "Barka da Safiya" Ya kalli Takardar Hannun Ummi da kallonsa kawai ta yi ta dauke kai zata sauka Entrance din. "Na zo gurin Aisha ne?" "Me kake nema a gurinta? To muma nemanta muke ba mu san inda take ba" Yayi murmushi jin yadda Ummi take son raina masa wayo, calmly ya ce. "Haba Ummi ko na saki Aisha ai har duniya ta nade ita uwar yata ce kuma har yanzu ban gama sauke nauyin hakkin da musulunci ya dora min ba akanta, dan Allah ina son ganinta" Ummi ta juyo ta kalleshi. "Fitsare marar kunya, fita ka bar min gida ko na saka a yi maka wulakanci yanzu nan, an fada maka yarinya ta bata kana fadawa mutane maganar banza" "Taya zata bata bayan daga gidan ta tafi can direban kuma ya dawo da ita..?" Ummi ta sauka Entrance din tana sauraren mai fadin wani yace ya ganta a hanya a kasa dazun amman be san inda take ba a yanzu. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un ina yarinyar ta tafi? Ko dai ta ji maganar da muke ne? Bari na dauko wayata" Ummi ta juya da sauri ta koma ciki, a nan Turhan ya fara fahimtar da gaske Emily bata gidan domin tashin hankalin da ya gani a fuskar Ummi da kuma kukan da matar nan take yayi yawa, ya juya ya nufi motarsa ya bude ya shiga yana mamakin taya zata bata? Ba gidan ta dawo ba ne ko kuma yaya? No ta dawo gidan mana ba gashi har ya ga takardar da ya bata ba a hannun Ummi, hakan yana nufin fita ta yi daga gidan ko kuma me? Yaja motarsa shi ma ya shiga nemanta na dan ya san inda zai ganta ba sai dan ya gwada sa'arsa, ya san abu ne mai wahala ace ta gudu daga garin gaba daya saboda Fatima, amman hakan be hana shi tafiya har tasha nemanta ba, tun yana jin natsuwa da abun har hankalinsq ya fara tashi sosai gashi ba shi da layinta balle ya kira. Amman saboda me zata tafi? Bayan Ummi da Aliyu sun rike ta, ko kuma dai su ma suna cutata mata ne? Ko kuma cilasta mata karbar fatima suka yi da hakan ya gagara
Chapter 122 · 0% Book details