← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 177

Sashe 32

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daya saba yi ya karasa gaban mahaifiyarsa ya zube kasa ya zauna. Barka da yamma Ammy Barka Labarabe Ya dan dago Kadan ya kalleta ya maida kansa kasa. Ammy ki yi hakuri da abubuwa da suka faru, na yi ina yina a yanzu amman ban samu ganin Aysha ba Allah yasa hakan shi ya fi alheri Ameen Ammy ta mike tsaye da nufin bar masa dakin sai ya sha gabanta da fadin. Na yi zaton komai zai wuce idan na dawo, Allah dai ya gani na iya yadda zan iya akan yarinyar nan abu ya gagara, Ammy ki daina bari ana zuga ki kina juya min baya Jin haka ya saka Ammy ta dawo ta zauna. Su waye suke zuga ni? Jawahir mana Ammy, ita take tare da ke kullum wasu abubuwan ita zata saka ki yi min, saboda bata san zafinki ba, ba ke kika haifeta ba Kai da kasan zafina ai gashi nan na aura maka yar mutane ka watsa min kasa a ido Dan kuskure kadan ne na aikata Ammy, dan haka Ya nuna kan akaifarsa. Amman gaba daya kin canja min, kuma iyakar biyayya ni na san na miki, bana son yarinyar nan kika ce na aureta na daure a haka na aureta, addininmu ba daya ba, na san a lokacin da na aureta ta musulunta amman yawanci ai musuluntar karya suke yi saboda su yi makirci, kaskanci ne a gurin namiji irina, jinin sarauta kuma jinin larabawa ya auri mace irin Emily, sam bata cikin irin matan da nake so, ya kamata ki duba min Ammy Fuskar tausayi ta bayyana a fuskar Ammy. Baka fada min baka sonta ba a lokacin da na hada aurenku ba ba zan cilasta maka ba, Allah kadai ya san kalar azabar data sha a hannunka da masarautarku, baiwar Allah Ya dago yana kallon Ammy cike da mamaki, shi a tunaninsa idan na fada mata duk wannan zata tausaya masa ne, madadin haka sai ta kara jin tausayin Emily din ma. Haka ne, kaskanci ne auren wanda ba bata tashi a addinin musulunci ba, kuma wanda ba yarenka ba, ba yar sarauta ba ina mai baka hakuri akan hakan Dan sarauta Ta mike tsaye ta fice daga dakin. Da ace zan samu damar yin ido biyu da Emily a yanzu, tabbas zan bata hakurin saboda Ammy, amman bayan kwana biyu sai na hada ita da bokanta na kashesu, yarinya kamar mayya gaba daya ta tafi da zuciyar Ammy, ita wacan katuwar kafirar maganin be kamata ba sai Ammy, ni kadai ta haifa a duniya amman yanzu ta tsane ni saboda wata shegiyar yarinya.. Yama fadar yana wargar da hannu, be san kaskanci da wulakanci ba sai da Emily ta duro gidansu, tashi yayi ya fice daga dakin ya shiga dayan dakin yayi waya da matarsa da mahaifinsa sannan yayi wanka ya fito falon. Tun kamin na yi aure, ina addu'ar idan na yi aure Allah ya bani ya mace, sai gashi kuma da na yi auren na haifi namiji, sai ya zama ba zan sake haihuwa ba, a lokacin da Aysha ta zo gidan nan sai na ji kamar addu'ar da nake yi ce a can baya Allah ya karba min ya ba ni ya mace ta wani bangaren da ban yi zato ba, yarinyar nan ta tsaya min a rai Labarin da ya sauko ya samu Ammy na bawa Jawahir kenan, Jawahir din kawai ya kalla yana ayyana munafurcinta a zuciyarsa ya fice ba tare da ya taba abincin da aka jera masa a dinning ba. Bayan fitarsa Jawahir ta kalle Ammy. Dan Allah Ammy ki yi hakuri ki cire Aysha a zuciyarki, ki kaddara ta mutu, ki shirya da Ya Turhan ku dawo kamar yadda kuka a da, Wallahi tausayi yake ba ni Ammy ta kalleta tana murmushi. Baki san waye mahaifin Turhan ba shiyasa yake baki tausayi, larabawa suna da zuciya mai tauri, shi kuma ai jinin mahaifinsa, nonon ma na larabawa ya sha ba nawa ba, kar yi mamaki idan aka ce miki ya sake aikata kuskure bayan wannan Jawahir ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai cike da tausayi. ALIYU POV. Tun jiya da aka kawo ki asibitin nan kike fushi da ni, ko dan rantsuwa da alkawarin da na daukar miki ai ya kamata ace kin yarda da ni Cikin alkawarin da rantsuwar ai na ga chat dinku Ke yanzu ko a mafarki aka ce miki ina son Emily zaki yarda Ta dube shi kamar zata yi kuka. Har ka rike sunanta ma Turhan fa ya auri yarinyar nan kuma har sun haihu da ita, Turhan kuma abokina ne mahaifiyarsa kamar uwa take a gareni, taya zan iya soyayya da ita ma balle har nace zan aureta? Kuma addininmu ba daya ba, ba abun da kike tunani ba ne Yanzu dai gashi nan ai ka janyo min nakuda Edd na be cika ba amman gashi nan nakuda ta same ni, kuma gashi sun ce idan ban haihu da kaina ba za su min CS Ya rumgumeta. Zaki haihu da kanki lafiya In Shaa Allahu Me yasa ba zaka fadawa Turhan gaskiya ba, bayan kasan nemanta yake idan har baka da wata manufa akanta? Ka san yadda Turhan yake son haihuwa amman baka fada masa yana da ya ba, idan baka da wata mummunar manufa akansa miyasa ka yi haka? Tana maganar tana cige baki tana numfashi da karfi. Idan Allah yasa kin haihu lafiya wan warware miki komai Allah dai yasa na haihu lafiya, Allah yasa na tashi Wallahi babu wanda zata aurar min miji Wallahi Allah kuwa na rantse Shi dai kallonta kawai yake be yi zaton tsananin kishinta ya kai haka ba sai yau. Ummi bata iso ba har yanzu? Ta iso kin san ai ta fi kusa, ta sauka gida ne sai ta yi wanka zata zo, su Hajiya ma suna hanya Ka min addu'a Aliyu Ina ta yi Ya shafa kanta yana ta karanta mata addu'o'i. Misalin karfe goma sha daya na safe iyayen Kameela suka iso asibitin, a lokacin nakudar ta taso mata gadangadan ya fito waje sai addu'a yake yana kai da kawo. Da waya ya kwatanta musu gurin da yake har suka iso, kana kallon mahaifiyarta zaka fahimci tana cikin tashin hankali haka ma yayarta. Cikin ladani ya gaishe su kamar yadda ya saba mahaifiyar ta amsa rai a hade domin Kameela ta labarta mata komai ta waya. Hajiya ai da kun wuce can gidan kun dan huta tun da ni ina nan Aa kara dai zamana kusa da yata, tsayuwarka a nan wani amfani yayi mata, ba kai ne sanadin duk wannan ba A take Anty Shafa wacce ta kasance yayar Kameela ta karbe zancen Hajiya ta dora da nata. Gaskiya Aliyu baka kyauta ba, kasan matarka tana da ciki be kamata kana yin wasu abubuwan ba Aliyu ya kalli Anty Shafa da duba na tsanaki. Me tace na yi.? Ta yi shiru bata ce komai ba, sai dauke kai da tayi. Ya ciro wayarsa yana amsa kiran mahaifiyarsa. Okay Ummi bari na zo na dauke ki Ya sauke wayar, ya kalli sarakuwarsa. Zan je na dauko Ummi daga gida yanzu Ta amsa masa a takaice cikin bacin rai. Aliyu ya saka kai ya fice cikin rashin jindadi, daman ya san za a rina domin Kameela bata da sirri ko kadan mu'amalar auratayya ma sai ta fadawa kawaye ta, be yi mamakin dan ta fadawa iyayenta sanadin nakudarta ba, wannan halin nata na rashin sirri yana bata masa rai sosai. Ko da ya isa ya samu Ummi a harabar tana jiran isowarsa. Ummi madadin ki zauna a ciki kika fito waje Idan ka iso ai zaka iya dadewa shiyasa na tsaya jiranka a nan, mu tafi Kamin ta shiga motar ya fito da sauri ya zagayo ya rumgume ta. I miss you Ummiiiiii Kai wai baka san ka girma ba, baka jin kunyata You're my best friend my first love Ya je zai sumbance ya ta tureshi ta bude motar ta shiga, dariya yayi ya koma motar yaja suka fice daga gidan, suna tafi suna hira har suka isa asibitin ya zagaya ya bude mata ta fito ya suka jera zuwa gurin da ya bar su Hajiya dazun. Ummi na hango Hajiya da Anty Shafa ta kalli Aliyu. "Kasan ka fadawa iyayenta sun zo to ni miye na fada min na zo? Ke ma ai mahaifiyarta ce Idan ba mahaifiyarta a kusa ba Ummi ta dan sham kamshi domin ko kadan bata son raini. Anty Shafa ce ta fara gaishe da Ummi sannan Hajiya ma ta miko mata gaisuwa. Lafiya kalau Daga Hajiya har Ummi babu wanda yacewa wani an iso lafiya. "Allah dai yasa ta haihu da kanta, idan ba ita ba haushe zaka dauki halin da namiji ka saka a zuciya Cewar Anty Shafa. Ummi ta yi kasa da ido tana saurarenta, kamin ta dago ta kalleta tana murmushi. Shafa ya yaran? Ya Step Mom dinku? Har yanzu dai shiru kin ki kawo mana kati? Ina nan ina lalabe Ummi kin san mazan sai a hankali, yara suna lafiya Ta amsa cike da gatse. Haka ne Allah ya kawo na gari Ameen Ta amsa. Aliyu ya ciro wayarsa dake ringing ya fice daga gurin, Ummi kuma ta nemi guri ta zauna Hajiya nata safa da marwa tana daga hannu tare da rokon Allah ya saukar da Kameela lafiya. Ameen ya rabbi, idan ba sakarci irin na Kameela ba, yaushe namiji zai maka alkawarin ba zai kara aure ba ka yarda, gashi nan ta jawa kanta nakudar dole Hajiya ta juyo ta kalleta. To miye laifinta? Allah dai ya bude mana idonta lafiya? Ameen Ummi dai bata ce komai ba sai saurarensu take, ta san kuma saboda ita ake yi dan ta ji. After like one hour Kameela ta sauka lafiya sai dai abun da ta haifa be zo da rai ba. Hakan kuma be hana iyayenta mijinta da surukar murna ba domin ita dai ta haihu lafiya bayan ta sha wahalar nakuda. Sai da Aliyu ya rada ma yaron suna sannan aka yi masa sallah aka binne shi a makabarta musulmi dake garin Part-harcour. Ko kadan Aliyu be jidadin yadda yaron ya zo babu rai ba, sai dai babu yadda xa'ayi da hukuncin Allah
Chapter 32 · 0% Book details