Sashe 96
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 4 Tausayinta da na mahaifiyarta ya ratsanshi ya saka ya tare hawayen yana murmushi sannan ya shafa kanta. "Aa Lafiya za mu isa In Shaa Allahu, kawai wani abu nake saurare na ji tausayinta shi ne" Ta yatsina baki irin na su na yara tana wani iyayi. "Ni bana yin kuka wa mutane, mutum idan yana da matsala ai shi zai yi kukansa ko?" "Eh amman tausayawa yana da kyau, ana son haka" "Okay" Ta amsa ta cigaba da kallon da take. "Mun kusa sauka" "Okay" Ta amsa ba tare da damuwa ba. Aliyu ya sauke numfashi a hankali idonsa basa masa gizon komai sai fuskar Emily, and he remember yadda suka tsabanin kira har ta yi ta masa dariya a waya, sauti dariyar nata dawo masa, ya tuna haduwarsu a office da tsabanin da suka samu na shiga Elevator da lokacin da ta yi masa tambaya har ta so ma magana da yaren da bata yi zaton yana ji ba, tunani na ya jefo masa ganin da yayi mata na karshe da yadda take ta murmushi kuma murmushi yayi mata kyau a cikin bakar abayarta kamin ya ankara sai gashi yana nasa murmushin a take. "You deserve happiness..." Fatima ta amsa masa da sauri tana dagowa ta kalleshi. "Yes i deserve it" Kakkaurar dariya ce ta subuce masa irin mai gunna da kal kal. "Yeah you deserve happiness too baby" A rasa kuma sai ya ce. "And now i know why Vito hate you, idan baki son mutum ya shiga uku wannan baki naki is something else" Ya kunna dayan voice din wanda shi ne na karshe ya cigaba da saurare, wanda a cikin yake son tabbatar da wani aukuwar wani abu ko akasinsa. ***. ****. ****. Daga lokacin da na shaki wannan hodar ban sake sanin inda hankalina yake ba, ban kuma san tsawon awanin dana dauka cikin gushewar hankalin ba, ni dai na farko da karfi ina jan numfashi, numfashi yana janyewa sai dakin da duk abin da yake ciki yana ta juya min ina jin jiri ga jikina a jike da alama ruwa suka zuba min. "Yarana yarana yayana, su kadai gare ni yarana" Yarana kawai nake nema domin su ne a raina, ruwan suka kara watsa min aka kama kaina aka soma a cikin wani bokiti dake cike da ruwa aka cire suka rike gashin suka jijjiga ni da karfi, a take na fara amai domin akwai yunwa a tare da ni ga kuma abin da na shaka warin da nake jinsa wani iri a hancina yana kai min har makoci, ga kuma jijjigar da suke min. Yar indomie da na ci ce na amayar na kwanta a gurin a wahale ina ta kiran sunan yarana. "Fatima ta... Ibraheem.... Yarana..." "Ke musulma ce?" Ita ce tambayar dana fara ji, na dago na kalli mai tambayar daker har lokacin ina dan ganin jiri ga jikin nawa ya kara mutuwa. "Mu kashe ta kawai boss, duk yadda aka yi budurwarsa ce ko kuma ta san wani abu kansa kawai tana wasa da hankalinmu ne" Na ji dayan ya fada da halshen igbo, sai dayan ya ce. "Ko ma ba matarsa bace wannan ai kazama ce daga ganinta, zamu iya kashe ta dai saboda ta san mu muka aikata kar ta kara a gaba ta fada" "Dauko wuka" Wanda yake babbansu ya fada a take na tashi zaune na ce. "Wallahi ban san wanda kuka kashe ba, bani da alaka da shi, ku yarda da ni mana" Na amsa musu da yaren Igbo sai duk suka cika da mamaki, ogan na su ya taso ta zo inda nake ya turani da kafa na koma kwance ya dake wuyana. "Taya kika san me nake fada?" "Ina jin yaren igbo" Na amsa daker har bakina ya fara zubar da jini domin talkamin da ya take ni da su masu zafi da nauyi ne. Ya daga kafarsa "Ya kike jin yaren?" "Saboda na zauna a Lagos" "Wacece ke?" "Labarin yana da tsayi" "i don't care ki fada min yanzu" A dole na takaita labarin na fada masa abubuwa masu muhimmanci har zuwa inda ya gan ni. Kamin yace komai dayan daya dauko wuka yace karya nake na tsara komai ne. "Me zai saka na tsara komai?" ai ba biyana za ku yi ba, ba wani abu nake nema daga gareku ba, me zai saka ba za ku bincika ba?" "ina da mutane a ko'ina har Lagos zan saka a bincika min Idan karya kike zan kashe ki" "Na yarda" Na amsa a take, sai ya saka aka dauko masa takardar na bada address din guraren da komai ya faru ya rubuta sannan ya tashi ya fita ina tambayar ina yarana. Har ya fice be amsa min ba, bayan ya fita wani ya shigo min da yaran London yana ta bachi kai langabe wata kila ya dame su da kuka ne suka shaka masa irin abun da suka shaka min, Fatima kuma tana ta tsosai hannu tana sauke ajiyar zuciya irin na babyn da ta yi kuka ta gaji. "Ba zaki fada mana gaskiya ba ko?" Na kalleshi na rasa me zan sake cewa, shirun da na yi ya saka shi fiddo wata karamar wuka ya yanki kafata da ita sai da na fasa ihu. "Ban san komai ba gaskiya na fada" Na matsar da yarana na rumgumesu domin na lura Fatima yake kallo zai iya cutar da ita. Ya mike tsaye ya fice haka na zauna a dakin har dare jini na zubar min a kafa ga aman da na yi a gurin ga kunzugun da na yi ina son na canja ba ni da wanda zan saka nonona na dauke babu ruwa saboda ban ci komai ba, ga tsoron ban san me zai faru da mu ba, ga kuma ana be farka ba har lokacin, abubuwa suka hade min goma da shirin. Ina cikin wannan halin shugan na su ya sake shigowa ya kalleni yana toshe hanci. Ya haska ni da kyau ko'ina na jikina. "Waya yanke ke ni a nan?" "Wannan ne ya yake ni, kuma gaskiya na fada muku ban yi karya ba" "Waye?" "Wanda ya kawo min yarana" Ya juya ya fita be jima ba ya dawo tare da mutumen ya haska min shi. "Wannan ne?" "Eh" Mutumen ya bude baki zai yi magana Shugaban na su ya ciro bindiga ya harbe shi a ramen wuya a take ya fadi kasa yana karkari jini ya samu hanya kamar ruwa, ni kuma na shiga aikin ihu yana daka min tsawa bana ko ji sai ihu nake, jikina na rawa hankalina ya tashi ban tana ganin an kashe wani a gabana ba sai ranar, ban daina ihun ba sai da suka shaka min wani abun a hanci hankalina ya sake bacewa. Da na sake farkowa farkowa sai na gan ni a wani daki na dabam yarana suna kusa da ni sun sai kuka suke, ashe tun da suka shaka min ban farko ba sai safe. Na kama su na rumgume ina jin jikina ba karfi, can anjima sai ga wani ya shigo ya tambaya me nake bukata yanzu? Na fada masa ina son abinci. Sai ya fita ogan da kansa ya shigo min da abinci ya aje min babu ko zancen wanke hannu balle baki a take na bude shinkafar na fara ci, Ibrahim ma ya rika ci da sauri ko minti biyar ba mu yi ba muka cinye abinci har muna neman kari. Shi dai yana tsaye yana ta kallona. "Akwai bandaki a nan ki yi wanka, za a kawo tufafi ki canja tare da yaranki, and why are you bleeding?" "Saboda sabuwar haihuwa ce" Ya juya ya fita. Ya kawo min tufafi dogayen riguna da pad da panties ga kayan yara na maza da na jarirai. Haka na yi rayuwa a dakin na tsawon kwana uku a yan kwanakin nan na samu kulawa da abinci mai kyau wanda rabon da na ci shi tun bayan da na bar gidan Ammy, ko a sudan tura abinci kawai nake ba dan ina iya ci ba kuma ba dan ina jindadinsa ba sai dan babu yadda na iya. A ranar da nake cika kwana hudu ya shigo ya same ni ina zaune a kasa domin a kasa muke kwanciya ni da yarana gashi tiles ne, Fatima har tari take, Ibrahim kuma yana zazzabi har kuma lokacin ban san a wane gari nake ba balle unguwa azo kuma zancen gida. Ya zauna kasa kamar yadda nake zaune yana kallona. "Emily na bincika labarinki a Lagos, here in Kaduna places din da kika zauna da Kaduna, a Sudan ne kawai ban bincika ba, and you're right akan abun da kika fada baki da alaka da mutumen da kika nake zargi, this is the first time da na ji tausayin wani ya kamani sosai wani da ban sani ba, and na ji dadi da ban kashe ki a take ki ba. Emily ina da kyakkyawan sako a gareki" Shirun da yayi ne ya saka na kalleshi sai da ya karanci natsuwata sannan ya ce. "Wannan ne karo na farko da nake son na kyautata rayuwar wani, na yi abun alheri a gareki, Emily ina son ki zauna a karkashina zan baki kulawa zan miki gata ke da yaranki, zaki zama a cikin ikona ni kawai cin amana ne bana so, wanda kika ga na kashe ma amanata ya ci, kina son haka" Na daga masa kai. "Tohm amman fa bisa sharadi daya, zaki bar wannan addinin ki koma addinin ki na asali, domin babu abun da na tsana kamar musulunci da musulmai, kuma kin zauna da su a yanzu kin fahimci yadda suke, idan kin yarda ki fito waje ki same ni, yau zan bar garin nan" Ya tashi yayi tafiyarsa, a lokacin zuciya da tunani suka fara min rawa, har na kasa zaba tsakanin addimai guda biyu, an kai ruwa rana daga zuciyata zuwa tunani kamin na fahimci komawa asalin addinina na shi ne gata ne, kuma shi ne rufin asirina ko da yake ban sani ba a lokacin ko shi ma zai ci amana ta ne, amman ba ni da wani zabi domin na gaji da rayuwar dake. A take na dauki Fatima