← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 177

Sashe 70

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba sai ya sam miki ki karya" "Kawai na zo nan ne na.... Na..." Emily ta makale a maganar ta ki ta fita, Kameela ta karasa kusa da ita tana murmushi ta dafata. "Karki damu, ba sai kin min bayanin komai ba, ki gaishe min da yarki Fatima" Ta nufi kofar fita ta bude office din ta fice, Aliyu yayi saurin bin bayanta, sai suka sauka kasa tare. "Muje na sauke ki gida" Ya fada yana kallon yanayinta har lokacin bata nuna masa komai ba. "Okay" Ta bi bayansa suka isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya zagaya ya shiga yaja motar, bata ce masa komai ba har suka isa gida shi kuma sai sake saken yadda zai bullo mata yake ba dan yana tsoron ta ba sai dan yana gudun bacin ranta, kuma ya san ko da ace bata da wannan zafin kishin idan ta ganshi da wata dole zata yi kishi balle tana da shi. Sai da ya faka harabar gidan sannan ya ce. "Da zaka min uzuri ki fahimce ni Kameela..." Bata bari ya karasa ba ta tari numfashi. "Dan Allah kar mu yi wannan maganar da kai, ka kaddara ban ga komai ni fa yanzu na yarda da kai, ba ni da matsala ko cikin mata dubu zaka shiga na san zaka fita, hakan be daga min hankali ba ko kadan" Ta bude motar ta fita tana murmushi. "Allah ya tsare me zan dafa maka?" "Anything" "Okay I Love you" Shi dai mamaki ya hana shi amsa mata da I love you too sai kallonta yake kamin yaja motar ya fice. Ya faka a inda ya gurin da aka tanadarsa domin aje motarsa sannan ya fito ya shiga cikin ma'aikatar ya shiga Elevator ya sauka hawa na biyar ya shiga office side dinsa, fada Sosai yayima Nick. "This isn t professional behavior, why would you allow anyone into my office without notifying me first?" "Apologies, sir. I allowed her in because I recognized her as your wife. As for Emily, she's one of our staff, and you had previously instructed that any staff member who needs to see you should be allowed in. That s why I let her through" "That policy is now revoked" Aliyu ya fada a fusace. Nick ya amsa masa cikin ladabi da girmamawa. "Understood, sir. I apologize and will be more careful going forward" Ya wuce ya shiga office dinsa. Zaune ya samu Emily ta hade kanta da guiwa. "Miya faru minene matsalar?" Kamar jiransa take ta dago. "Miye ma be faru ba? A wane dalili zaka aikawa Vito da jami'an bincike masu tu'ammali da miyagun kwayoyi? Me ya maka" Aliyu ya dan yin kamar mai tunanin waye kuma Vito. "Vito.. Vito... Oh Vito? Me zai saka na yi haka toh? Miye alaka ta da shi?" "Ni dai na fada maka, idan wani abu ya same shi kamar ni ya sama, domin shi yake dauke da ni, kuma shi ne mutumen da ya taimake ni a lokacin da babu mai taimakona, shi ya maida ni a yadda nake a yau, ko farcensa bana son wani abu ya sama" "Ahh ahhh ni kika gani kofar gidansa ne? In banda dai kina son ki dora min laifi?" "Indai kana son na cigaba da aiki a nan na cigaba da mu'alama da kai, to ka cire Vito a idonka" Ta fada masa har tana nuna shi da yatsa. Ya kalli yatsanta ya kalleta be ce komai ba ya nufi kujerarsa ya zauna ita kuma ta juya ta fice daga office din. Sai da ta koma office dinta sai ya fara jin haushin abun da ta yi ma Aliyu bata san lokacin data fashe da kuka ba, ya wuce makadi da rawa amman bata da zabin da ya wuce haka, saboda gudun jefa Aliyu a matsala, ta san watan wata rana Vito zai iya ganowa kuma komai zai iya faruwa idan ya sani, haka kuma ba ta so wani abu ya samu mutumen da ya tallafawa rayuwarta ta sanadinta ba, ko da yake bata da tabbacin Aliyun ne, wata kila Vito ba zai rasa makiya ta wani bangaren ba tunanin haka ya kara jefa ta a damuwa. Kasa aikin komai ta yi duk kuwa da kasancewar ta yi waya da Vito ya fada mata babu wata matsala har sun tafi, amman kunya da nauyin abun da ta yi ma Aliyu be bari ta iya komai ba a ranar. ALIYU POV. Sai da lokacin tashi aikinsa yayi sannan ya sauko compound din ma'aikatar ya nufi motarsa ya shiga ya saka basket din da Kameela ta kawo masa dazun be taba komai ba, yana shiga motar ya amsa wayar mahaifinsa, ya fara tukin da hannu daya dayan hannun kuma manna da waya a kunnensa domin fitar da yayi ta dazun da gaggauwa be bar shi ya fita da Bluetooth dinsa ba. "Shikenan Daddy na gode sai mun yi magana" Ya fada sannan yayi ma mahaifinsa sallama ya aje wayar a cinyarsa ya cigaba da tukin har ya isa gida ya faka ya kashe motar sannan ya dauki wayarsa ya bude motar ya fita ya dauki kwando. Taku goma sha daya ya kai shi entrance din shiga cikin gidan, ya tura kofar falon ya shiga da sallama kamar yadda ya saba duk kuwa da ya san ba lallai yau a tarbe shi a yadda aka saba ba domin yau ya bata ran uwargidan ba kadan ba ko da yake bata nuna masa ba. "Sannu da zuwa" Ta fada a yanayin da ba na fushi ba kuma ba far'a sosai ba, sai dai kuma ba ta tarbe shi kamar yadda ta saba ba. Hakan be hana shi isa inda take zaune ya sumbance ta ba sannan ya aje basket din a gurin. "Sannu da gida Gimbiya wannan ado haka?" "Duk na ka ne kai kadai, je ka yi wanka ka zo ka ci abinci" "Okay" Ya haura sama ya shiga dakinsa, tufafinsa ya fara cirewa ya aje wayarsa ya shiga bandakin yayi wanka ya fito ya saka tufafi marasa nauyi ya fito falon domin bawa cikinsa abun da yake wajibun, yunwa yake ji sosai saboda be yi karin safe ba, dan haka ya zauna a seating room din ya nade kafafuwansa Kameela ta zera masa tuwon da miyar taushe ta kawo masa ruwan wanke hannu da kuma na sha da lemun kwakwa, sannan ta zauna gabansa tana game da wayarta. Da ya kalli yanayinta sai ya ji babu dadi, saboda ya san akwai damuwa a tare da ita, amman ta nuna masa kamar babu komai, sai ya ji kamar be kyauta ba. "Kameela da zaki fahimce ni ki yi min uzuri, da rayuwa bata wahalar da ke ba, na san kina jin babu dadi a zuciyar kuma kin biye ko kin aje a ido kuma kina min kallon rashin fahimta, Wallahi Wallahi Wallahi babu soyayya tsakanin da Emily, abun da zuciyarta ta raya miki ko zata raya miki ko idonki ya gani Wallahi ba soyayya ba ce, kuma na miki rantsuwa na fada miki ne a yanzu ba dan ina tsoronki ba sai dan ina son farincikinki, kuma ina sonki, tsabani ko kadan bana son yana shiga tsakaninmu, farko cikinki a koda yaushe shi ne burina, idan kin yarda da ni shikenan idan kuma baki yarda da abun da na fada miki ba a yanzu shi ma duk daya" Ya karasa tare da bude Warmers din zai fara zuba abinci, sai Kameela ta yi karaf ta dauke miyar fuskarta dauke da damuwa. "Karki ci wannan bari na zuba maka wata" A matukar kidime Aliyu ya kalleta ya samu kansa cikin wani kalar firgice da be taba samun kansa a zamansa da Kameela, ta nufi kitchen da sauri sai yayi hanzari tashi ya bi bayanta ko da ya shiga ya samu tana juye miyar a sink. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ayatarwa duk a farashi mai sau Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sau in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke ha uwa. [5/28, 9:27 AM] : https://chat.whatsapp.com/HQSJMqxBuI985hZVzy0S03 ABOKIN RAYUWA
Chapter 70 · 0% Book details