← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 177

Sashe 139

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaki iya ci" Ta dauka ta kai baki sai ta ji abun wani iri domin bata taba ci amman dan tsami tsamin da ta ji ya karbi bakinta dan haka ta cigaba da sha. Kwankwasa kofar falon aka yi kadan kadan kamar bugun yaro, Emily ta kalli kofar da sauri zuciyarta na bugawa da gudu kuma tana raya mata Fatima ce. Aliyu ya mike tsaye ya nufi kofar ya rufe sai ga Fatima ta shigo da gudu. "Uncle..." Har ta rike shi zata rumgume shi sai kuma ta sake shi ta nufo gurin Emily da gudu, Emily ma kasa rike kanta ta yi sai ta zabura da sauri ta rumgume yarta ta fashe da kuka, zata iya yafe komai da kowa amman ban da yarta, ko kadan bata son Fatima ta dandana rashinta domin ta san yadda ta rayu saboda uwarta bata kusa da ita, cikin kuka Fatima ta ce. "Momy ina kika je? Kin dade baki zo ba" "Saboda kin ce baki so na" Sai ta kara rumgume Emily. "Ina sonki ke da daddy ina sonki,. Karki sake tafiya ki bar ni bana son ki tafi" Emily ta rumgume. "Idan baki son na tafi ki daina zabar Mahaifinki kina barina, ko gobe kika ce shi kike so to zan tafi na kyale ki" Sai Fatima ta kara fashewa da kuka. "Amman ina son shi Momy, yana so na" "Who do you love the most? Ni ko Dady?" "You" "Good" Emily ta rumgume ta sosai a kirjinta kamar zata maida ita ciki. Fatima na shiga cikin falon Aliyu ya kalli Turhan dake tsaye bakin balcony din be tako ba, sai ma dukawa da yayi yaje masa wayarsa a kasa. Ya saka hannayensa duka biyu aljihu. Aliyu na ganin hakan ya fita ya karasa gurin da wayar take ya duka zai dauka. "Ka ji kunya Aliyu, ka ci amanata" "Ban ji kunya ba, kuma ban ci amanarka ba, akwai tsarin da na yi sai dai Allah be ba ni ikon cika wannan burin ba har Kameela ta yi abun da ta yi" "Ai baka da bakin kare kanka" "Ba kokarin kare kai nake ba, kuma ba so nake ka fahimta ba, ina fada maka abun da yake gaskiyarsa ne" "Har abada... Ba zan taba barin yata ta kira wani katon banza da sunan Baba ba, yata ba zata yi agolanci ba yana da kyau ka san wannan" "Kai yanzu baka ji kunyar fadar hakan ba? Kai yanzu abun da ya dame ka wa Emily zata aura? Ko wa take so? Baka damu ka san lafiyarta ko samun farincikinta ba? Kana da son kanka Turhan... Kuma har gobe ban yi nadamar taimakin Emily ko kuma boye mata kai ba, saboda ta fada kai ne wanda bata son ganin kuma zaka karbe mata yarta ga shi ka aikata, kai yanzu iyakar burinka Emily ta dawo gareka, idan ta dawo zata dawo ta yi farinciki ko aa ba shi ne a gabanka ba, kaico da zuciyar dake take kirjinka" "Kai kuma Tirrrr da aboki irinki mai fuska biyu, zan baka mamaki Aliyu, kuma ina gargadinka da shiga tsabgar matata da yata, baka da alaka da dukkansu" Aliyu yayi murmushi kawai ya juya ya shiga ciki, Turhan ya tofar da yawu yana jin zuciyarsa tana kuna. Aliyu na shiga falon Fatima ta juya ta kalleshi. "Ka ce Dady ya tafi sai gobe zan koma tare da Momy" "Already ya tafi ai, ni ba zaki min oyoyo ba?" Ya ware hannayensa, sai ta taso tana dariya ta nufe shi da gudu ta rumgume shi ya daga ta sama ya jefa ya chabe yana dariya ita ma sai datiya take tana farinciki domin ta yi marmarinsa da Momynta. Emily tana ta kallonsu tana murmushi. " Kin yi missing din Momy?" "Sosai" Ta fada tana kallon Emily, sai Aliyu ya dauke ta haura sama da ita suna tafe yana mata hira. A ranar Emily ta yi bachin farinciki irin wanda ta kwana biyu bata yi irinsa ba, ta kwanata rumgume da yarta a dayan dakin da Ummi ta bata saboda ta ki yarda ta hau gadon Ummi ta kwanta sai dai kasa, Ummi kuma ba zata iya jurar kallon ta kwana a kasa ba, dan haka ta bata wani dakin ita da yarta. Kamin Fatima ta yi bachi sai da ta yi ta bata labarin abubuwan da Ammy take mata da kuma Dadyta. Washe gari Emily na cikin bachi ta ji an taba ta sai ta bude ido, ta yi zaton Fatima na dakin sai ta yi arba da Mama Barakat ga kayan abinci an jere a gurin kamar dai wacan karon. "Ki yi hakuri na tashe ki kina bachi" Emily ta murza ido ta tashi zaune tana duba gadon har tana kokarin sauka sai ga Aliyu ya kwankwasa kofar dakin, sannan ya turo ya shigo yana dauke da Fatima. "Mama Ummi tace min kin shigo yanzu" Ya fada yana kallon Mama Barakat. "Eh ku yi hakuri na yi muku sammako, bana son Emily ta karya da komai ne sai abun da na dafa" "Wacece wannan?" Fatima ta tambaya tana nuna Mama Barakat. "Kakarki ce, ita ce ta haifi Emily" Fatima ta wara ido kamar wata babba tana mamaki. "Muna da kowa a nan ina farinciki da zama a nan ba za mu koma can ba ko Momy? Ashe ke ma kina da Momy" Emily ta daga mata kai. Aliyu yayi murmushi. "Karki yi zaton ko na shigo na same ki a yanayi marar kyau ne, ita ce ta farka da kanta ta fito tana bin daki har ta same ni, wai ta yi zaton ko na tafi ne" "Momy mun yi sallah mun yi sallah da shi kina bachi" Emily ta yi murmushi tana kallonsu. "Aci dadi lafiya ni zan sauka, Emily idan kin gama da wannan sai ki sauko na mu breakfast din yana jiranki, Ummi ma sai fada take wai Mama Baraka ta dako sakko baki farka ba kuma ta san zata shirya miki abun karyawa" Mama Barakat ta yi murmushi. "Ka bata hakuri, na tashi tun karfe uku na fara shirya komai saboda kar na makara, zan yi farinciki idan ta ci" "Zata ci, ai Emily bata da matsala ko kadan kamar ruwa haka take, kifi ce musulmi nama" Ta fada sannan ya juya ya fita yana dauke da Fatima dake tambayarsa miyasa Emily bata kama da Mama Barakat? Bayan ita tana kama da Turhan. Emily ta shiga bandaki ta wanke bakinta da sabon brush da ta gani ta yi fitsari ta fito ta zauna bakin gado, sai Mama Barakat ta sauka kasa ta bude abincin gaba daya tana tambayar wane zata ci. "Ina son na kira ki da Aisha ban san ko kina son haka ba, Ummi ta fada min ana kira Aisha amman Emily ya fi karfi, amman sunan da na saka miki Aisha ne ba Emily ba, musulma na haife ki ba kirista ba" Emily ta dube ta. "Kina so na haka kika bar ni? Har yanzu na gagara gane wane laifi na aikata miki, na wahala an wulakanta saboda ba ni da kowa, anyi min gori, abubuwa na suka banbanta da na sauran masu iyaye, ban san gata ba ban iya komai sai guduwa daga wannan gurin zuwa wani, fada da kika yi cewar da saninki kika jefar da ni kuma baki taba tunanin ki waiwaye ni ba ya tsaya min a rai, mu ma yaya muna da hakki akan iyaye, baki yi adalci tsakanina da sauran yayanki ba, su kika zabi haifarsu da aure kuma kika zauna tare da su, ni kuma kika watsar da ni, baki yi tunanin waca kalar rayuwa zan yi ba, wane kalubale zan fuskanta ba, kin yi komai saboda gujewa kunyar duniya, shin ba na ji ku musulmai kuna cewa lahira akwai hisabi ba? Saboda kin haife ni ba da aure ba ni miye laifina? Ba shawara aka yi da ni kamin a haife ni ba, ya kamata ki yi tunanin idan kika jefar da ni wace kalar rayuwa zan yi? Zan rayu ko kuma zan mutu ne? Baki tunanin ni ma ina da hakki akanki? Taya kika iya kwantawa ki yi bachi alhalin kin san kina da ya a wani gurin da baki san wane hali take ciki ba? Wace irin uwa ce ke? Taya zaka sha wahalar ciki wata tara da nakuda kuma ka jefar da yaron? Shi ma fa rai ne? Uwa tausayi aka sani da ita ke da iyayen da suke haka ba ku kyauta ba, miye laifin wanda aka haife? Wai illar kawai saboda ba shi da uba, kuma ba da aure aka haife shi ba, miyasa baki yi tunani ba kamin ki haife? Wallahi na Wahala na wahala na wahala, ni kadai na san yadda na yi na Wahala na wahala na wahala na wahala na wahala........... Ahk ahk ahk..." Ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya da on rai. Mama Baraka ta bar inda take ta dawo kusa da Emily ta zauna ta rumgume ta tana kuka. "Ki gafarce ni, ki yafe ni na yi kuskure na sani, ki yi hakuri Emily ki yafe min..." Emily kuka Mama Baraka kuka babu mai iya rarrashin wani... ______________________ Ga iyayen da suke haifar yara ba da aure ba su jefar, shin kun san kuna daukarwa kanku hakki ne? Hakkin zina hakkin haihuwa ba da aure ba hakkin jefar da yaro, ba ku san wane hali zai fada ba wace rayuwa zai yi a wane hali zai girma ko ya samu kansa ya rayuwa zata kasance, wasu yaran ba za su taba haduwa da iyayensu ba sai Alkiyama. Allah ya tsaremu, ka tsarkake zuciyarmu. [8/4, 9:55 PM] : https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t ABOKIN RAYUWA
Chapter 139 · 0% Book details