Sashe 111
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 4 "Kina son zama da ummi na ko hotel za a kama miki? Ko da yake Hotel ba tsoro, ke ma kuma baki jin magana, dan haka zaki zauna da Ummi" Bata kula shi ba sai kuka take rarewa. "Emily kina son karasa ni ne, hawayen ki nan na san akwai kaso na a cikin zubarsu, ba ni da lafiya ki gani, zubar hawayen nan na ki kuma ya saka zuciyata nauyi, so kike na mutu ne?" "Babu wanda zai fahimce ni, ni kadai na san wahalar da na sha, ni kadai na san damuwar da take cikin kaina, ba ni da kowa wannan ma kawai ya ishe ni bakinciki, yanzu kuma ya karbe min yarinya, be kamata ka kalleni ka fada min wannan maganar ba, Khalifa da Turhan ba ni da makiya irinsu a duniyar nan" "Na fada miki ne, saboda shatawa kaina da ke da duk wanda zai rabe ki layi, abu ne da yake a hukunce ba ni na dora miki ba" Ta kara fashewa da kuka har da buga kafa a kasa kamar yar yarinya, Aliyu ya tashi zaune kenan Ummi ta turo kofar dakin ta shigo, ganin Emily na kuka ya saka ta kalli Aliyu. "Me ka mata?" "Me zan mata Ummi ni da nake haka?" "Toh dadi ya sakata kuka kenan?" "Aa saboda na fada mata har yanzu akwai aure tsakanin ta Turhan ne" Ummi ta dafata ta mikar da ita tsaye. "Taso yata share hawayenki, ki daina bari ana ganin rauninki" "Ummi zaku je da ita gida zata zauna saboda nan bata da kowa sai mu" "Ita kuwa take da kowa tun da take da mu, je waje ki jirani kinji" Emily ta share hawayenta ta fita dakin. "Ka kwanta ka huta, zamu je da ita gida" "Ummi karki bari ta gudu, kuma dan Allah ki kula da ita ki kwantar mata da hankali, Wallahi bana son damuwar Emily ko kadan, kuma ki fada mata da zarar na ji sauki zan dawo mata da yarta, sannu a hankali komai zai zama daidai" "Zan kwantar mata da hankali, amman dai karka manta kai ma fa ka fada akwai igiyar auren Turhan akanta, karka manta da wannan" Aliyu ya kalleta. "Eh kuma hakan ba zai hana na taimaka mata ba, ko kwantar mata da hankali" "Amman dai kar a wuce gona da iri, kar a tsallake iyakokin ubangiji" "Subhanallahi, Wallahi ba abun da kika tunani ba ne Ummi sam sam sam babu wannan ko kadan, kawai dai ina tausayinta ne kuma ina son ta samu farinciki, ta dawo tafarkin musulunci" "Ka san ni uwa ce, na kan iya hango abun da zai taho tun kamin ya taso" "Toh gaskiya a nan baki hango daidai ba" "Toh ga mu zuwa, Allah ya baka lafiya" "Ameen, zan baki mamaki Ummi" "Daman Mamakin nake son ka ba ni ai" Ta shafa kansa ta yi murmushi. "Zan je na girka maka abinci mai kyau, kamin na dawo na san ka samu yin bachi" "Okay, can i have my phone please?" Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya, Ummi ta mika masa wayarsa sannan ta fice dakin taja masa kofa a hankali, a tsaye ta samu Emily ta rika hannunta suka fara tafiya Ummi na kwantar mata da hankali har suka isa gurin motar da aka kawo Ummi ita da Ummi suka shiga baya, daman front seat din akwai dan sanda daya a ciki, direba yaja motar yana tukawa a hankali har suka isa Family house dinsu Aliyu wato gidan da Ummi take zaune a Kaduna tare da Daddy, direban na faka motar harabar katon gidan dake cike da yan'uwa da abokan arziki da suka ji abun da ya faru da Aliyu kuma sun tafi Asibiti ba a barsu sun shiga ba. Ummi ta bude motar ta fita tana amsa wayar Daddy dake sanar mata yanzu jirginsa zai taso daga Abuja zuwa Kaduna, ta doshi Entrance din gidan, Emily ma ta bude ta fito ta bi bayanta sai ta ji an kira sunanta da muryar da bata wayanci ko ta waye ba. "Emily..." Ta juyo domin jin dalilin kiran arba ta yi da direban da ya kawo su a yanzu, sai dai har ga Allah bata wayance shi ba domin rabin fuskarsa a kone take, ta sake juya domin be ce mata komai ba ita ma kuma ba ce masa zata yi ba saboda bata san waye ba. "Emily... Ni ne Khaleefa ne.. Baki gane ni ba? Ni kam ba zan iya mantawa dake ba duk yadda kika chanja, tun da kika shigo motar nan na gane ke ce" Yana magana cikin rawar jiki da rawar murya kamar mai shirin yin kuka. Tun da ya furta cewar Khaleefa ne Emily bata juyo ba ta cigaba da tafiya, a lokacin ne Ummi ta juyo bayan ta kare wayar da take sai ga Emily ta biyo bayanta Khaleepa kuma ya biyo ta yana mata magana. "Dan Allah ki taya dan girman Allah ki saurare ni" "Kin san shi ne?" Ummi ta tambaya. Sai Emily ta tsaya a gabanta "Tsohon mijina ne, shi ne ya fara cutar da ni, shi ya budewa kowa kofa, shi ne mutumen da ya fara raba ni da gata, shi ne ya fara karantar da ni rauta tata, shi ya janyo min duk masifar da nake ciki yanzu, shi ne uban da har ana ya mutu ba taba ganinsa ba, shi ne mutumen da ya koreni da tsohon cikin dansa, yan'uwansa suka juyo min baya, su suka fara kirana da tubabbiya" Ummi ta matsa daga gaban Emily fuska a hade ta kalli Khaleefa. "Karka sake ko da wasa ka sake mata magana, taya zan shigo da bakuwa ka tari gabanta ba tare da neman izini ba? Direba ne kai a nan karka manta da wannan" "Tohm Hajiya ayi hakuri" Ya fada yana tare hawayen da suka cika idonsa. Ummi ta kama hannun Emily suka shiga ciki kowa sai kallonta yake saboda dress din dake jikinta ga kuma sarkar cross, Ummi ta shiga da ita ciki ta kaita dakin da Aliyu dake gidan. "Nan dakin ana ne Aliyu, ki zauna a ciki ki yi duk yadda kika so, ki sake jikinki kamar kina cikin gidanki" Emily ta kalli dakin. "Idan kin bani dama zan je na dan ji da bakin da suka zo mana jaje" Emily ta saki hannun Ummi ta nufi gadon da Aliyu yake kwana a lokacin da yake gidan ta zauna. Ummi kuma ta juya ta fice, kwantawa Emily ta yi kan gadon ya lumshe ido zuciyarta na mata wani irin zafi. "Wayyo Zuciya" Komai ya taru a zuciyar ya tsaya mata... TURHAN POV. "Kamata yayi kawai na koma na daukota, to miyasa amfanin barinta a can ma? Macen da na shekara nawa ina nema yanzu na ganta na bari wani katon banza yana controlling dinta" "Idan ka je daukar ta zata yarda ta biyoka ne? Tun da fari da baka bata komai ba, ai duk haka ba zai faru ba, ni na ma manta ban tambaye ka ba, sakinta ka yi ko guduwa ta yi?" "Guduwa ta yi ni ban sake ta ba" "Amman ka munana mata a zamantakewarku?" "Ba cancan ba, sai dai wani abun ta dauke shi da zafi saboda bata son zama da ni yanzu, kuma dole za a samu abubuwa da ba za su mata dadi ba, Ammy saboda Al'adar ba daya ba, kuma kin ga ina da mata, ko ma dai minene Ammy abun da ya wuce ai ya wuce yanzu ake fuskanta, tun da gashi har da yarinya a tsakaninmu, kuma matar nan ita muke da ni ma saboda gyara kuskuren da na aikata, ke da kanki fa kin ce na gyara abun da na bata" Ammy ta sauke numfashi. "Tun da har an ganta, to komai ya zo da sauki, balle kuma har ga ya tsakani, ka rika bin abubuwa a hankali, yanzu idan ka ce zaka yi rigima ai zaka karawa kanka bakin jini ne kawai a gurin Emily" "Amman kuma sai na bar wani katon banza yana kallar min mata yana jin sautin muryarta yana karanta mata karya da gasjiya akaina" Ya mike tsaye. "Zan je na yi magana da ita zan bi duk wasu matakai da suka dace ta ruwan sanyi tsakanina da ita, kuma zan jawa Aliyu kunne, shi yana da tasa mata ni kuma yana son ya kashe min aure saboda ya bata tsakanina dake kuma da Fatima, ni na rasa me na tarewa Aliyu ne Wallahi, ashe haka hassada take" "Karka je" "Ammy me yasa kike hana ni abubuwa ne? Miyasa kika kin goya min baya a komai, yau na tabbatar da ace ni na na aikata abin da Aliyu ya aikata Wallahi ba zaki goya min baya ba, amman da idona na ga Ummi ta fito ta rungume Emily sun shiga tare, kin ga ta goyawa danta baya kenan da saninta ake komai waya sani ma ko Emily a gidanta take, shiyasa har Kameela ta san da komai" "Turhan..." Ammy ta kira sunansa, ya kalleta ba tare da amsa ba. "Zauna" Ya koma ya zauna. "Mahaifinka ya fada maka ni na dauki cikinka wata ta haife ka ne?" "Aa" "To taya kake tunanin zan fi son wasu da kai? Duk abubuwa na nake maka ko nake fushi da kai akansu saboda ina kaunarka ne, na aura maka yarinyar nan saboda na samu ka yi kusa da ni, kuma ita ma ina hango mata jindadi a zamantakewarku, saboda ta auri wani bata dace ba, ina ganin idan aka kyautata mata kamar an yi ma musulunci hidima ne, daga lokacin da ta gudu ta bar min bakar wasika na san zamanku be tafi a yadda na yi tsammani ba, shiyasa ban taba tambayar ya kuka yi zaman ba, amman a zuciyata na ji babu dadi kuma na ji idan har baka nemo yarinyar nan ba, ni da kai ba mu gyara abun da ka bata ba, ba zan samu salama ba, na yi fushi da kai ne saboda na auna hakikan abun da yake zuciyarka da gaske zaka iya min biyayya ko aa kuma zaka so abun da nake so ko aa, daga lokacin da ka dage kana neman yarinyar nan zuwa yau data bayyana a garemu, ya tabbatar min da