Sashe 80
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... Page 3 Ta hade yawun bakinta tana kallon agogon da Aliyu ya bata. ***. ***. "Matar da na fa a gidanta neman taimako, har aka ba ni abinci ita ce mahaifiyar Turhan, a lokacin da na bashi shinkafa sai ya dauke numfashi, hankalina ya tashi sosai na yi zaton London ya mutu a wacan lokacin a take na fara girgiza shi ina ihu, matashiyar yarinyar da ta kawo min shimkafar ta fito da sauri tana tambayar lafiya, ya mutu shimkafa na ba shi sai ya dauke numfashi, na shiga uku na mutu ba ni da kowa sai shi. Shi ne abun da nake ta fada ina hargowa, sai ga Hajiyar ta fito tana tambayar me ya faru? Bana iya amsawa sai sambatu nake ina ihu, sai tace a kira direba ta shiga da kanta ta dauko mayafinta ta karbi Yaron ta shiga mota na shiga direban yaja mu zuwa wata babbar asibiti, muka zuwa aka karbi Ibrahim suka bude nasa file suka masa duk abun da ya kamata, likitar data karbe shi mace ce a take ta rufe ni da fada a wane dalili zaki ba shi shimkafa jariri kamar wannan, baki da hankali? "Ba ni da ruwan nono ne kuma ba ni da wani abun ba shi" "idan baki da abun bashi sai ki bashi abinci yaushe kika taba ganin an bawa jariri abinci? Haka kika ga ana rainon jarirai" Na girgiza mata kai ina hawaye. "Ban san yadda ake ba, ba a taba haihuwa a gabana ba, ba a taba rainon jariri a gabana ba" Na bata amsa, sai Hajiyar ta dube ni. "Daga wace duniyar kike?" "A gidan marayu na taso, ban san duka wadannan abubuwa ba" Na durkusa kasa ina mata godiya "Na gode Hajiya na gode" Sai ta rika ni ta mikar da ni tsaye. "Sunana Ammy karki damu ki kula dai ko ruwa karki sake ba shi" "Amman idan be ci komai ba ai zai iya mutuwa ko?" "Za a kawo abincin da zakiba shi, yanzu zaki zauna ki yi jinyarsa har zuwa lokacin da za su sallame shi, akwai wanda kika sani nan?" Na girgiza mata kai. "Ban san kowa ba" "Labarin yana da tsaye kuma idan na fada miki ba lallai ki yarda ba" "Zan yarda, saboda na yarda Ubangijina ba zai bari a cutar da ni ba, amman tun da kin ce labarin yana da tsayi ki aje har zuwa lokacin da za mu samu zama" Na amsa mata da tohm sai ta tafi tare da likitar aka bar ni a gurin, can kuma sai ga likitar ta dawo tace na tafi Ammy tana jirana gurin mota wai zan bita mu koma gida saboda jariri zai zauna a hannunsu ne har ya samu sauki, zuciyata bata gamsu da haka ba dan haka na ki yarda saboda ina tunanin kamar sace min yaro suke son yi, ganin haka ya saka dole aka bar ni a asibiti, Ammy tasa aka kawo min abun shimfida da abinci, aka kawo madara ta jarirai ana bawa yaron, kullum za a kawo min abinci, amman bana iya ci saboda hankalina yana gurin yarona, aka kwana biyu sai Ammy ta dawo duba ni a lokacin ne take tambayata ko na san yarona yana da wata rashin lafiya nace aa, sai tace min likitoci sun fada mata yarona yana da sickle, ban ma fahimci ciwon ba sai da ta yi min bayanin cewar jinina da jinin mahaifin yaron ne ya zo daya, tace min kar na damu zata dauki nauyin maganin yaron, haka kuwa aka yi naira biyar ban taba kashewa ba a tsawon zaman da na yi na asibiti na wata daya, a tsawon watan da na yi asibitin nono be kawo ba saboda bana iya cin abincin kirki kullum cikin tunanin butulci da Khaleefa yayi min da kuma makomar yarona, ban san ina da hawan jini ba sai a lokacin kuma ashe idan mace ta haihu wanka ake mata da ruwan zafi ko kuma a bata magani ban sani ba hakan ya saka na yi ta kumbura, ina jin akwai canji a jikina amman saboda babu mai kula da ni ban damu da lafiyata ba, har sai da Ammy ta same ni ta tambaye ni ina da wani ciwo ne da yake saka ni kumbura haka domin na zama wata babba uwar mata, nace mata aa sai idan abun ya same ni ban sani ba, sai saka aka bude min file aka bincika ni, a nan aka gane hawan jinin da na samu da cikin dana be sauka ba, kuma ba a gasa min jiki ba shiyasa nake ta wannan ciwon. Ni ma gadon suka ba ni ana kula da ni, a tsawon wata daya da na kara a asibitin Ammy ce take kula da ni ni da dana, ta saka mai aikinta tana jinyata har na samu lafiya amman jiki be sauka ba. Da aka sallamo ni sai na amince na dawo na gidanta na bar London a asibitin, ta ba ni daki daya a cikin dakunan da suke cikin gidanta kuma suke kusa da dakinta, daman tun ina asibiti ta kawo min tufafi sai ta kara min wasu tace idan ina son abinci na sauka na ci kuma na sake jiki kamar gidana. Na jidadi ta karammani a lokacin ba tare da sanin wacece ni ko daga ina nake fito ba. Kwana biyu da dawowata aka sallamo London sai aka dawo da sh i gida, sai ta siya masa tufafi kusan kala goma sha biyu bayan pampers da madara da ta karo ta siya masa gadon yara da tawul, mai aikinta take masa wanka ta goya shi wani lokacin kuma ita da kanta zata dauke shi ya wuni a hannunta. A haka na kwashe wata uku a gidanta, kuma a tsawon lokacin nan bata taba tambayar labarina ba, bata tana nuna min banbanci ba, idan ta ga ina ja baya gurin shiga lamuran gidan sai ta rufe ni da fada, wai na kasa sakin jiki, ita ta lura da wani bangare na ibada ta daya kamata na gyara sai ta fara koya min a lokacin take tambayar a gidan marayun da nake ba a koya mana ibada ni. A ranar na fayyace mata komai na yadda kaddara ta tsara min rayuwa. Ta yi kuka ta tausaya min kuma ta yi min alkawarin zata zame min uwa, itace ta fara saka ni a makarantar islamiya na fara koyon addini. Sannu a hankali na sake jiki na zama kamar yar gidan, wata rana ina zaune falo ta same ni tace Aisha ina jinki kamar yata daman ina sha'awar ya mace Allah be bani ba, samunki a yanzu ya saka na ji kamar Allah ya maye min gurbinki da wanda ban samu ba ne, fadar hakan da tayi sai ya kara karfafa min guiwa na jidadi, ta fada min yaro daya ta haifa amman baya hannunta matashiyar da na gani a lokacin mai suna Nana rikonta take, yanayin yadda take mu'amalantar danta abun sha'awar ba dan na gani ba sai dan labarin da ta ba ni da kuma yadda take idan ya kirata ko ta kira shi, na fahimci tana matukar kaunarsa ne ta yadda take fada min hallayensa da dabi'unsa, har ta fada min idan ya kan shekara biyu kamin ya zo gurin, amman wnnan karon idan ya zo akwai shirin da ta yi masa, ban fahimci me take nufi ba ashe aurena da shi take son ta hada amman bata fada min ba. Sai dai tana yawan ce min musulmai suna da dadin zama kuma Allah zai min sakamako da miji na gari. A haka har yarona ya shekara daya ina kula da shi, Ammy kuma tana siya masa magani da madara, sai dai ni kam jiki be sauka ba, duk kuwa da kasancewarsa na samu lafiya sosai ga wadata ta abinci, na zama kamar wata babbar mace fari ya fito jan gashina yayi kyau saboda yana samun gyara a yanzu komai a wadace. Wata rana na yi wanka na shirya cikin shudiyar atamfa wanda ta yi mjn kyau sosai, na fito harabar gidan na zauna ina shan iska, da kuma mamakin yadda har zuwa lokacin Khaleefa ba neme ni ba, ba dan ina da bukatarsa ko wani abu daga gareshi ba sai dan cikin da ya sake ni da shi, da kuma irin halin da ya bar ni, amman be biyo sawuna ba. Da ace ban hadu da Ammy ba wata kila da ina nan cikin gararin rayuwa amman be damu ba. Be yi tunanin alhakina ba ko na dansa. Ban san ba, ashe ina tunanin hawaye suna saukowa min amman ban jin ba saboda zuciyar ta yi nisa gurin tunani har sai da Ammy ta fito ta zauna kusa da ni tana fadin. "Me kika tuna? Domin na san kin samu lafiya yanzu ballantana nace ciwo kike ji" "Bana tunanin komai" "Ga hawaye a fuskarki Aisha karki cutar da kanki mana, ki dauke ni a matsayin uwa bana son kina boye min komai" Na kai hannu na taba fuskar sai na ji hawaye. "Kawai ina tunanin yadda Khaleefa ya juya min baya ne, kuma yadda be waiwaye ni ba har yanzu, be damu ta sanin halin da dansa yake ciki ba" Sai ta yi murmushi. "Yarinya ce ke shiyasa baki fahimci rayuwa ba, ai a yanzu ne yake cikin shauki da jindadin yaudara, ba zai neme ki a yanzu ba, sai a lokacin da nemanki ba shi da amfani a gurinsa, kuma ina baki shawarar idan ya dawo miki karki saurareshi ban ce karki yafe masa ba, amman karki yarda ki sake saka kafarki a gurin da aka wulakanta ki aka nuna baki da daraja. Aisha maza na gari suna tsada, ba kowa ne yake iya aure ya rike amana ba, amman ina mai tabbatar miki nan gaba kadan zaki samu samu wanda zai mantar da ke komai zai so ki ke da danki, ni ma na sha wahalar rayuwa a aurena na farko kuma banbanci abun da aka miki da nawa kadan ne, ke kin yi ma arziki an barki da yaron, ni nawa karbe yaron yayi kuma ya hana na shayar da shi, sai da na shekara ashirin kamin na samu ganin dana a ido