← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 177

Sashe 79

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

shiga" "Mama Baraka shi da kansa fa yace na dawo" "Eh wata kila akwai abun da kika masa ne, ni zan kira shi, zan yi magana da shi duk abun da za ayi karki biye kanenki da yayyenki domin su ba son Aliyu suke ba, ke kuma kina son mijinki, duk yadda za'ayi ki daina bari ana jin kanku, ita mace gona ce ga namiji ka yi gina ka rufe duk abun da kake so babu wanda ya sai idan ta fitar, shi kuma namiji sutura ne ga mace babu mai ganin tsiraicinta sai idan ta bayyana ko ya bayyana, karki nuna masa ma kin fadi abun da ke tsakaninku, kina son komawa dakin mijinki?" Ta daga kai. "Ina son Aliyu sosai Wallahi" "Indai har kina sonshi to ki shirya fuskantar duk wani kalubale akansa, ni zan kira shi da kaina zan yi magana ta fahimta daga ni sai shi, idan ya kama har mahaifiyarsa zan yi magana da ita, amman bana son ki bar Hajiya ta sani" "Ba zan fada mata ba" "Yauwa yanzu na gamsu kina son mijinki, saka min number sa a nan zan kira shi mu yi magana ba zan ma nuna masa kin san na kira ba" Mama Baraka ta mika mata wayarta Kameela ta karba ta saka mata number Aliyu. "Amman fa sai kin taya ni yakin, domin idan ya zo ya nuna yana son ki koma toh ki nuna kina son mijinki kuma kina son komawa idan ba haka ba yan dakinku za su kara bata abun ne kawai" "Na fahimta Mama Baraka" Na fada tana duba dp Emily dake whatsapp ta nunawa Mama Baraka hoton Emily saboda ta ji dadin shawara da karfafa guiwar da ta yi mata. "Kin ga hoton yar iskar yarinyar nan" Mama Baraka ta yi saving number Aliyu sannan ta karbi wayar Kameela tana duba hoton. "Tsohuwar Matar Abokinsa ce fa Turhan har da ya a tsakanin su yanzu haka Turhan din nemanta yake sosai, wai mahaifiyarsa ta yi fushi da shi saboda ita, ni ban gamsu ba wata kila dai ta gudu masa da ya ne, ko da yake Aliyu yace wai be san yana da yar ba, kuma ban san miyasa ya ki ya fada masa ya ganta ba, wata kila saboda sonta yake ko? Idan ba haka ba ai zai fada masa, wata kila kuma ya boye min ne, amman ko minene dai sai na bincika, yanzu ma bake jin karfin guiwar komawa dakin mijina" Duk dogon rattaba zancen da Kameela take Mama Barakat bata ji ko daya ba, gaba daya hankalinta ya tafi gurin kallon hoton Emily kamar mai son tantance wani abu. "Ya sunanta" "Emily amman Aisha ake ce mata" "Tana PH ne tare da shi?" "Eh yanzu tana PH amman yar Lagos ce a wani gidan marayu ta tashi a can ta girma aka ce, kamin ta auri Turhan din ko a ina suka hadu ma Oho" Mama Baraka ta hade abu da karfi yanayinta gaba daya ya canja, ta kurawa hoton ido kai kace ranar ta fara ganin mutane. "Bata fiki da komai ba, hasken fata kawai zata nuna miki, wannan ai bata kai ta kwace miki miji ba, karki daga hankalinki akanta, kuma ita ai ba musulma bace da alama ga Cross a wuyanta" Tana maganar idonta ya cika da kwalla sai dai bata bar Kameela ta gani ba. "Eh kafira ce" "Wata kila ma duk abun da kike zato ba shi ba ne, Aliyu da hankalinsa ai ba zai yarda ya rabi kafira ba, zan yi magana da shi na san zai saurare ki kwantar da hankali" Ta mika mata wayar. "Tashi ki koma bangarenku kar ayi zaton wani abun muka shirya ma" "Tohm" Ta mike tsaye ta fice daga falon tana jin bakinciki dake zuciyarta yana raguwa saboda shawarar da Mama Barakat ta bata da kuma matakin da tace zata dauka, a yanzu kuma tsoron ta daya kar ya fada mata ko mahaifinta cewar ta saka masa guba a abinci, idan kuma har Ummi taji ta san auren ta da Aliyu ya kare har abada, ta san bata kyauta ba, be kamata ta aikata hakan ba kuma ta yi kuskure, da yanzu ta kashe shi wa gari ya waya? Ai ko mahaifiyarsa ba zata fita jin zafin mutuwarsa ba, haka dai ta yi ta sake sakenta har ta shiga bangarensu ta shige dakinta ta kama hoton Aliyu tana kallo da wasu videos da suka yi a tare tana ta jin kewar mijinta da kuma nadamar abun da ta aikata domin ta fi kowa sanin Aliyu yana sonta, ta san ba dan yana sonta ba wata kila da sakinta zai yi gaba daya ba zai tsaya cewa za a duba kwakwalwarta ba ko ya turata gidansu. *** *** *** Mama Barakat ta bi bayan Kameela da kallo har ta fice fuska a raunace, ta yunkura zata tashi kafarta ta hagu ta yi mata nauyi sosai ta gagara daga kafar, zuciyarta ma ta yi nauyi sosai kamar an dora mata dutse. "Aleeya Aleeya Aleeya... Samira Samira..." Ta kwalawa yaranta kira Sameera ta sauko da saurinta tana dariya hannunta rike da waya da alama wani abun take kallo a wayar. "Mama gani zuwa, Aleeya bachi take" Mama Baraka ta daga kai tana kallonta har ta sauko. "Rika ni ina son zan shiga dakina na" Ta fada mata da yaren yarbanci daman da yarenta take magana da yaranta idan su kadai ne a gidan wannan ya saka suke jin yaren sosai. Sameera ta yi hanzarin aje wayarta tana kallon Mama Baraka. "Mama Lafiya?" "Kafata ce ta rike, ina son na tashi na kasa" Sameera ta rika ta cikin karfin hali domin bata iya dagata gaba daya, Mama Baraka mace ce mai jiki, ta mike tsaye daker ta cije baki ta taka dayar kafar dayan kuma ta daga ta, da taimako Sameera suka haura sama suka shiga dakinta Sameera ta dora ta kan gadonta. "Mama ko asibiti za mu je?" "Aa zai saki, ai bata taba min haka ba sai yanzu, tafi dakinku zan kwana na huta" "Okay" Ta fice daga dakin, Mama Baraka ta kwanta saman gadon ta yi ruf da ciki ta danne zuciyarta take mata nauyi ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. [6/16, 2:18 PM] null: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing ABOKIN RAYUWA
Chapter 79 · 0% Book details