Sashe 52
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2 Ta dauki wayarta da sauri ta kira Vito. "Ban ga London ba ko'ina na duba baya nan, kuma na yi waya da Chidimma tace ta bar shi gurinka ta fita" "Ina Lisa?" Fatima yake nufi domin haka yake kiranta wani sa'in saboda ya tsani sunan hausawa da aka saka mata. "Tana.... Fatima tana...." Ta juya ta kalli agogon falonta lokacin dawowarta daga makaranta har ya gota. "Ina kika je? Jiya ma kin fita ina kika je?" Ta kashe wayar ba tare da ta ba shi amsa ba. Vito ya kalli wayar har ya aje sai kuma ya dauka ya kira Chidimma. "Hello ranka ya dade" Ta amsa da nishadi da girmamawa. "London yana gurinki?" "Aa ai tare na barku da shi da zan fita" "Baki koma gidan ba? An duba ba a ganshi ba" "Wata kila ko yaji muryar mahaifiyarsa ne ya boya, dan yanzu rashin kulawar da take ba shi ya saka baya son zama kusa da ita, madam bata kula da shi yadda ya kamata" "Chidimma ki yi hankali da bakinki, ki daina fada min laifin Emily, idan ma wani abu take marar kyau ki bari na gani da kaina, karki sake fada min tana gida ko bata nan sai idan na tambaye ki, madadin na ga laifinta ke zan tsane ki ne" Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya dauki rigarsa dake aje kan gadon ya saka ya fito dakinsa sai ya samu mahaifiyarsa a falo tana hira da mai dafa masa abinci. "Fita zaka yi" "Eh" Ya amsa a takaice sannan ya dauki daya daga cikin keys din da suke lake a kofar fita falon ya fice. Ta dayam bangaren kuma Emily na aje wayar ta nufi harabar gidan tana tambayar mai gadi ko Fatima ta dawo? Sai ya fada mata bata dawo ba amman direban dake daukota daga school ya fita da mota tun dazun. "Amman ka ga London ya fita?" "Aa be fita ba indai ba Oga ne ya fita da shi ba a mota a kafa kam be fita ba wani kuma be fita da shi ba" "Ya bata ban ganshi ba" "Kin duba ko'ina?" "Eh" Ta amsa masa sai ta nufi kofar gate din ta bude ta sauri ta fita tana ta kalle kalle bata yarda yana cikin gidan ba domin ta duba ko'ina bata ganshi ba, haka ta fi hanya ko talkami babu a kafarta tana tafiya tana kalle kalle idan ta ga mutane sai ta tambaya ko sun ga wani yaro, kowa yace mata a'a. "Yaro ne sosai fari yana ihu idan ya ga mutane wani lokacin yana da jin tsoro kuma yana yin abu kamar marar hankali amman ba mahaukaci ba ne Autism ne, yana da matsalar data shafi kwakwalwa" "Ba mu ganshi ba" Gungun mashayan sun fada suna kallon cinyoyinta dake waje. Ta dora hannu akai har zata fasa kuka sai kuma ta karfafawa kanta guiwa ta kara gaba tana nemansa. Sai da ta kusa kai karshen unguwar tana duba kwararo ko lungu bata ganshi ba kuma kowa ta tambaya sai yace be ganshi ba. Can wata zuciyar ta raya mata ko ya bi direban da zai dauko Fatima makaranta gashi bata fito da waya ba balle ta kira, ta juya ta koma da sauri duk nisan hanyar bata gani ba cikin mintuna ta dawo gidan ta buga gate din da karfi mai gadin ya bude yana kallonta sai dai be ce komai ba ita ma bata bi ta kansa ba ta nufi cikin gidan da gudu sai ta samu kofar falon a bude Fatima na zaune rike da jakarta ta makaranta tana kallon mahaifiyarta a tsorace. Da sauri ta nufeta ta dafa ta. "Fatima kin dawo? Da direba zai je daukarki a school tare da London aka je? Ya bata ban ganshi ba" "Be bata ba, ruwa ya fada Vito ya zo nan ya tsamo London a swimming pool ya tafi ya kai shi asibiti" Emily ta fadi zaune idonta na cika da hawaye wata sabuwar fargaba na tunkarota, tunaninta be bata zai tafi can ba even though ta leka bata ganshi ba amman bata saka ran zai fada ruwa ba. Ta saki Fatima ta nufi staircase ta haura sama zuwa dakinta ta dauko wani makullin motar domin wacan motar data fita da ita da safe tana can gurin aikin su Aliyu ta baro. Ta sauko da sauri tana jin numfashi na sama kamar zai dauke gudu take amman kamar ana daure mata kafafuwa haka take ji, rashin kuzarin nan da ya same ta a office din Aliyu a dazun bayan ta gama gutsura masa labarinta ya dawo mata a yanzu. Gurin shiga motar ma sai da ta yi da gaske sannan ta iya bude motar ta shiga, cikin karfin hali ta yi ma Motar key ta yi reverse, a hanya ma tana jan motar motar na janta sai ta taka burki ta tafi sai kuma ta tsaya ko ta yi baya kamar wanda ta sha wani abu haka ta samu kanta duk wanda ya ganta sai yayi zaton ko ta sha wani abu ne, fakawa ta yi gefen hanya ta dora kanta a sitiyarin motar tana ta sauke ajiyar zuciya ta rufe ido tana maida numfashi, ta yi hakan ya fi a kirga sannan ta samu kuzari ya dan zo mata, ta sake tuka motar ta nufi asibitin da aka saba kai shi a duk lokacin da bashi da lafiya. Ta faka motarta a emergency ta fito ta rufe motar, ta nufi entrance din Emergency din tana kokarin daga kafarta ta taka gurin gabanta ya fada ras ras ras dudududummmm har sau uku, kamar wadda ta tuna wani abu sai ta fasa bata dora kafar, ta ja baya ta tsaya tana kallon Kofar Emergency din dake can ciki wato second door da mutane suke fitowa, ta kasa shiga ta gagara komawa ta tsaya a gurin har na tsawon minti 5. Tana tsaye a gurin sai ga Vito ya fito tare da wani yana hangota sai ya tsaya da sauri kamar mai jin tsoro, sai kuma ya taka ya karasa inda take tsaye. "Mu tafi gida" "Dana ya mutu ko? London ya mutu?" Vito ya dafata kamin ya sake cewa komai ta ce "Na jiya a jikina, an sanar min saboda ni ma uwace, ban taba samu kaina a irin yanayin da na samu kaina a yau ba, ban taba jin abu makamancin wannan ba, saboda ban taba rasa makusanci na jini ba sai yau, na ji abun da ake ji, na ragu yau na koma daga ni sai Fatima" Tana maganar wasu masu tsananin zafi suna sauko mata. "I'm sorry, zan kasance a tare da ke a cikin kowane irin hali Emily" Ta fasa wani irin ihu kamar mahaukaciya Vito ya rike kamin ta kai kasa, wani irin kuka take daya saka hankalin kowa dawowa gareta, bata san yadda ake ji idan an rasa wani ba sai a ranar domin bata taba rasa kowa ba sai yau. Shi ya saka ta mota ya tuko zuwa gida wanda suke tare kuma ya taho da gawar London, ta shiga falonta tana kuka Fatima ta tarbeta ita ma tana Kukan domin tun a dazun jikin yayi sanyi saboda yanayin yadda ta ga an ciro dan'uwanta a ruwan kamar tsumma. "Ya mutu Momi" Emily ta kasa magana ta rumgumeta tana ta kuka. Vito ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa ya runfe ido, domin ba kadan yake son London ba, dama Fatima ce wata kila ba zai ji damuwa da bakinciki kamar haka ba, amman London yana son yaron yaron ma yana sonsa, shi ya canja masa suna Ibraheem zuwa London ya canja masa addinin kuma ya yarda, ba kamar Fatima ba dake nuna masa kiyaya da rashin kunya, kuma ta ki yarda da sunan Lisa da ya saka mata, haka kuma har gobe idan ibadar ta tsikareta sai ta yi sallah ko taje Islamiyar da mahaifiyarta ta sakata. Chidimma na shigowa falon ita ma ta fashe da kuka, kusan idan aka cire Vito London ya fi sabo da ita fiye da mahaifiyarsa musamman a yan kwanakin nan da baya yarda da Emily. KAMEELA POV. "Hhmmm sai yau kika tuna da ni?" "Ke tunawa kike, ke da ba kira kike ba sai dai a kira ki?" "Baki san na haihu ba halam?" "Tohm yaushe?" "Yau kwana takwas, amman abun da na haifa be zo da rai ba, ina gida" "Allah sarki Allah ya bada rayayye" "Ameen kina PH har yanzu" "Eh mana kin san sai na yi shekara a nan ai" "Okay Allah ya taimaka" "Ameen, shi mijinki yana nan kenan?" "Tasmia ina ruwanki da mijina da har zaki tambayi mijina bana fa son haka" Tasmia ta kalkale da dariya "Kameela kina bani mamaki, wai ke lafiya kike kar kishi ya haukata ki fa" "Ke ya haukata ni din ina ruwanki? Toh miye na tambayar mijina" "To ai na ga yadda kike da kishi ne na yi zaton ko ba zaki iya barinsa a can ba tare kuka zo wanka gidan" "Mtssschesssss" Ta yanke kiran. Tasmia ta kyalkyale da dariyar mugunta. "Yau da kin san abun da mijinki yayi da sai kin kusa kashe kanki dan kishi, gashi nan daga tafiyarki ya tsallaka gurin wata da ba addinmu daya ba" Ta sake fashewa da dariya. "Ko da yake gayen ya hadu dole ki yi kishi ki yi taka tsantsan ai" Ta fada tana murmushi kamin ta tashi daga kwancen da take ruf da ciki ta yango Food flask dinta mai two set da ya siya gurin Khadeeja Candy ta bude ta zubawa kanta tsemo da miyar agutsi. Ta sake daukar wayarta ta kira layin Emily sau biyu tana maka miss calls sai a uku aka daga. "Hello..." "Wacece wannan" "Kawar tace" Dip ta ji an kashe wayar ta duba wayar tana mamakin waya daga? Ta sake jira sai ta ji wayar kashe. Ta tabe baki ta aje wayar kusa da ita ta cigaba da cin abincinta. ALIYU POV. Ya kalli harabar gidan da iska mai dadi ke kadawa sannan ya amsa. "Ina gida" "Gida a ina?" "Compound" "Me kake yi a nan toh?" Yayi murmushi.