Sashe 63
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummi nan gani nan bari adashe manya" Ummi ta shafa kansa ta saka masa albarka sannan ta kai masa rankwashi. "Dan Allah daga min katon banza da kai ka zo ka haye min a jiki" Ya tashi yana dariya. Ramla tana ta daukarsu hoto har da short video. Aliyu ya fito tare da rankiyar mahaifiyarsa har gurin motar da Direban ya bude masa. Aliyu yana ta kallon direban da biyu domin zuciyarsa na raya masa kamar wani abu kamar ba haka ba. "Ya sunanka?" "Khaleepa ranka ya dade" Ya juyo ya kalli Ummi. "Kun canja direba ne?" "aa dayan dai yaje ganin gida, dayan kuma shi yake kai yara Ramla school kasan tsoro ya hana ta iya mota har yanzu, Daddynku yace a karo daya saboda zirga zirga ya zama idan biyun basa nan daya yana nan, shi Daddy kasan ai yana da nasa na musamman ko da wasa baya ara mana shi" "Okay" Ya shiga motar suka yi sallama da Ummi Ramla na daga masa hannu da Aziza, sai da suka yi nisa sannan Aliyu ya ce. "Khaleefa ai ba suna ba ne ko?" "Eh ranka ya dade sunana na ainihi shi ne Hamza" Aliyu ya sake dubansa ta madubin motar, har ya bude baki zai sake wata magana sai kuma ya fasa ya sauke numfashi. Da suka isa Airport din direban ya fito da akwatin Aliyu bayan ya bude masa, sai Aliyu ya sake masa duba na tsanaki ya ce. "Kai dan wane gari ne?" "Kaduna, ranka ya dade" Daga haka Aliyu be sake cewa komai ba Direban ya ja masa akwaitin Aliyu yana gaba yana biye. EMILY POV. A ranar da Kameela ta kirata ta yi mata cin mutunci ta kira da suna kala kala marasa dadi Emily ta kwana da bakinciki da damuwa. Washe gari da ta tashi sai ta tashi jiki babu kwari mood dinta kuma ya canja domin ta kwana da tunani kalakala a ranta. Ko da ta sauko already Chidimma ta gama shirya komai, Fatima har ta wuce school, Vito kuma yana zaune a dinning din falon tare da Chidimma suna karyawa at the same time the same table. To her it's a new thing domin Vito be taba hada table da wata mace ba a gaban idonta balle har ya ci abinci a tare da ita. Kallonsa kawai ta yi ta kalli Chidimma ta dauke kai ta nufi kitchen ta shirya nata breakfast din dabam ta dauko ta fito, a lokacin ne Vito ya mike tsaye. "Good Morning Bae" Bata amsa ba kuma bata kalleshi ba ta haura sama zuciyarta tana mata babu dadi, domin bata gane ma'anar abun da yayi ba a yanzu. Saboda ta yi fushi ne jiya har ta watsa masa ruwa ta mari Chidimma? Ko kuma saboda bata nuna interest dinta akan aurensa ba ne? Ko kuma dai saboda ta yi fada da mahaifiyarsa ne.? Ba zata ce tana kishin karyarwa da yayi a tare da Chidimma ma, amman aikata hakan kamar ya budewa Chidimma din kofar raina ta ne domin a kasan ta take zaune. Ta kasa kai komai bakinta ta mike tsaye ta nufi backyard ta tsaya a gurin tana kallon itacen da suke nan, duk wani abu da yake samuwarta ko kuma ya sameta yana faruwa da ita ne saboda bata da ikon kanta kuma bata da gata, da ace kaddararta bata zo a haka ba, wata kila da salon labarinta ba a haka zai kasance ba. Sai da ta shaki iskar da take jin ta wadatar da ita sannan ta koma ciki ta zauna a one seater ta kai hannunta ta dauki wayarta, sai ta ci karo da sakon Kameela daga wata number dabam ba wacan da ta yi blocking ba saboda yawan sakon da take turo mata da kira. "Idan baki rabu da mijina ba sai na kashe ki, akan mijina bana ji bana gani kuma ban ragawa kowa" "Uhffff" Ta busar da iskar bakinta ta daga kanta sama ta sauke ta shafa kanta ta shafa jikinta gaba daya ta rasa me ke mata dadi. Kamar wasa Vito ya fara shareta kuma ya maida rabin al'amurransa a cikin gidan idan zai ci abinci zai ci tare da Chidimma on the same table, ko da kuwa Emily tana zaune a falon ne, da zarar ya nufi dinning ya zauna sai Chidimma ta tashi ta yi Serving dinsa, idan ta gama sai ya ce ta zauna a nan ta ci abinci ita ma, ya kan tambayi Emily ko zata ci sai ta amsa masa da aa, idan ya shigo ma yana tambayar lafiyarta ko ya rika hannunta, amman ba kamar da ba, hakan kuma yana kona mata rai kuma ya jefata a tunani, a yanzu bata san matsayinta ba, replacing dinta zai yi da Chidimma ko kuma dai yana yi ne saboda ya bata haushi. Da zarar sun fara cin abinci zata tashi ta ba su guri domin bata ita zama tana kallon bakinciki ba, ga Chidimma din sai daukar wanka take tana ta nishadi a yan kwana biyun nan. Ranar Laraba tana zaune a dakinta Fatima ta shigo sanye da uniform ta jefar da Jakarta a gurin haka ma lunch box dinta. "Yunwa naka ji" Emily ta dago ta dube ta kamin ta sake maida dubanta gurin wayarta dake hannunta tana karanta sakon da ya shigo mata. "Kina da Sako a wajen gate ki fito kamin mai gadinki ya hana shiga da sakon" Ta karanta sakon da aka turo da wata bakuwar number. "Momy I'm starving Chidimma bata nan ki zuba min abinci" Fatima ta fada a tsawace kamar yadda ta saba yi mata magana cike da rashin tarbiya. Sai dai ko kadan hankalin Emily baya gurinta tana gurin sakon da ta karanta, bata san waye ba, bata san sakon miye take da shi a waje ba. Kamar ya san tsoro take ji sai ya sake aiko mata da sakon sunansa. "Aliyu ne, sakonki yana waje" When she read the name sai ta ji she's safe ko da yake bata da tabbacin shi din ne ko Vito yake shirya mata wani abu? Ko kuma matar Aliyu dake neman rayuwarta. Ta sauka daga kan gadon da kafafuwanta dake sanye da safe ta fito dakin Fatima ta biyota bayanta. Ta isa gate din ta bude da kanta ta fita sai ta ga motar Aliyu fake nesa da gidan amman tana facing din gidan. Fatima ta janyota da karfi cikin ihu tace. "Na ce miki yunwa nake ji yunwa nake ji baki ji ne? I hate you" Emily ta kalleta kamar mai tsoronta. "Okay" Ta juya zata koma Aliyu ya bude motar ya fito ya doso inda suke tsaye, Fatima na ganinsa a take fuskarta ta cika da murmushi sai ya ware mata hannayensa ta je ta gudu ta rumgume shi ya daga ta sama. "I miss you" "I miss you too, ina ka tafi kwana da yawa?" Ya sauketa kasa yana kallon Emily da ta yi rama sosai "Ina nan, aiki ne yayi mana yawa, shiyasa na zo nace mamanki ta shirya ta koma aiki, kin ga da tana zuwa aiki ai kullum za mu rika haduwa ina siya miki chocolate da ice cream ina kaiki yawo" "Mi kake yi a nan?" "Na zo na fada miki ki shirya gobe ki koma aiki, office dinki yana nan yana jiranki, amman ba a karkashin Amal zaki yi aiki ba a yanzu, idan kuma baki ra'ayin aikin motarki tana nan kije gobe da kanki ki dauka karki aika kowa" Ya rage tsawonsa ya mikawa Fatima key din motar. "Ki bawa Momy" Fatima ta karba ta mika mata. "Good girl, ga ki kyakkyawa ga ki da jin magana to miyasa kike yi ma momy tsawa?" "Na ce ta zuba min abinci bata zuba min ba" "Okay amman ba a yi ma uwa tsawa, saboda ni da ke ai musulmai ne ko?" Ta daga kai. "Yauwa shiyasa kike burge ni, kina da saurin fahimta da ganewa, ga wayo" Ta kyalkyale da dariya. "Mu musulmai bama ma yima iyaye tsawa, muma musu ladabi da biyayya ne, idan kina son mu zama friends ni da ke toh karki sake yi ma Momy tsawa, baki ganin ke kadai kika rage mata ma? Tun da London be nan? Ki daina cewa i hate you idan wani yace miki haka zaki ji dadi?" Ta girgiza kai ta turo baki. "Ita ma bata sona bata min abun da nake so? Ko London ya mutu yanzu amman bata ba ni sunan Babanshi ba, yan makarantar mu suna min dariyar sunana na mata ne duka uku, ka gani Fatima Emily Aisha" "Sunana ne kawai matsala? Idan Momynki ta dawo aiki zan dauke ki mu tafi makaranta a canja miki suna daga Fatima Emily Aisha zuwa Fatima Aliyu" Farinciki ya cika fuskar Fatima. "Da gaske? Ka yi alkawari" Ya mika mata karamin yatsansa. "Na yi ke ma ki min alkawarin ba zaki yi ma Momy tsawa ba daga yanzu, idan ma kin manta kin yi za ki bata hakuri" Ta daga mishi kai sannan suka kulla Pinky promise. "Okay now say sorry to your momy, ask for her forgiveness" Fatima ta kalleta a shagwabe ta ce "I'm sorry Momy please forgive me" Aliyu ya kama kunnunsa yana daga kansa ya kalli Emily. "Kin yafe mana ko Momy?" Ya mike tsaye still yana kallonta. "Please Unblock me, ina tunanin ban cancanci haka daga gurinki ba" Ya shafa kan Fatima sannan ya nufi motarsa yana daga mata hannu, har ya wuce Emily bata motsawa daga inda take tsaye ba balle ta ce wani abu. _______________________ Sannu yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe inki da kaya masu kyau, masu ima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da ta awa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet inmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau i ne sosai. Muna nan a Kano