Sashe 3
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zan yi ki fahimci na yi nadama? Mi zan yi ki yafe min? Ina cikin damuwa ina cikin matsala Na yafe maka Turhan na dade da fada maka haka Ba irin wannan yafiyar nake so ba, irin wanda idan zan bar kasar nan kike kewata, idan na zo kina murna da zuwana, mu zauna mu yi hira mu yi wasa da dariya, Ammy me zan ki min irin wannan yafiyar Ya tambaya yana shirin fashe mata da kuka. Zan maka irin wacan yafiyar da kake tsammani ne, only if Aysha ta yafe maka... Ya girgiza kai. Ammy karki yi haka, idan kika alakanta yafiyarki da Aysha to ba zaki taba yafe min ba, domin ban san ina Aysha take a yanzu ba, ban san inda zan ganta ba, Ammy idan kika yi haka ba ki min adalci ba... A take ta daka masa tsawa. Kai ka yi min adalci kenan? Saboda kai yarinyar nan ta bar addinin musulunci, duk wani gata da na so na yi mata na addinin musulunci ka ture, duk wata shimfida da na yi na yaye mata damuwar da wani ya saka ta ka nade shimfidar ka jefar, na shirya zama mata uwa saboda bata san wannan gatan ba, duk wani buri da nake da shi akanta da akanka ka ruguza shi, aikinka da yadda ka riketa yadda ka wulakantata ya goge duk wani karatu da na shimfida a cikin kanta cewar mu musulmai halinmu ba daya ba ne, a ranar da ka sauke ta garin nan da idona na ganta a gaban coci tana rokon su taimaketa, saboda tana ganin mu musulmai mun gaza. Turhan ka saka Aysha ta ji cewar mu musulmai ba ma iya kaunar wanda ya shigo musulunci, ka saka ta ji cewar ba mu da kirki, da karfi da yaji kun cire mata son addinin musulunci, da karfi da yaji kun nuna mata tubabe ba shi da gata a addinin Musulunci, duk wani buri da nake da shi akanka da ita ka rusa shi... Ka zabi Masarautarku, ka bi mahaifinka, to ka dawo na yi maka? Ammy kamar kin fi son Ay... Be karasa ta wanka masa mari. Na fi son Aysha da kai Turhan, haka ne baka yi karya ba hashenka a daidai yake, da ka rike ta a yadda na so wata kila da rikon zai iya zame min silar shiga aljanna, duk wani hali da ta shiga ko zata shiga kai ne sila... Ba ni ne sila ba... Ammy ba ni ne mijinta na farko ba, kuma ban mata wulakancin da kike tunani ba, yadda kike daukar abun be kai haka ba Ya fada yana hawaye shi dai kokari kawai yake ya fahimtar da ita kuma ya wanke kansa. Sai ta nuna masa kofar fita falon. Tashi ka fice min daga falo, ai kasar nan bata cikin rikon ubanka ko? Iyakar mulkin sarautarku da ikonku ya tsaya a Sudan ne, to tashi ka koma can ka rike sarautarka da matarka da yan'uwanka da mahaifinka, ka bar ni da nawa Ya mike tsaye kai a kasa ya fice daga falon. Ammy ta bishi da kallo har ya fice sannan ta juya ta kalli Amal dake tsaye stairs tana kallon abun da ke faruwa. Ammy dai kin yi hakuri na ga... Ammy ta kalleta fuska babu alamar wasa. Idan kika furta wani abu akan matsalar nan, to zaki hada kayanki ne ki bar min gidana Ta rufe bakinta da sauri ta juya ta koma sama. A mota Turhan ya samu kansa ya jingina da sitiyarin gaba daya ya rasa me ke masa dadi. Wayarsa ya dauka ya amsa kiran dake shigowa yana gyaran murya domin damuwa ta gama cinye karfinsa. Ihm ihm Hello Sai aka amsa masa daga dayan bangaren. Hello Turhan ya gidan? Lafiya Kalau Ashe ka shigo kasar, dazun nake ji a gurin Uzee Haka ne amman dai yau zan koma Why? Ba dadi, Aliyu har yanzu babu wani abu sabo, Ammy ta ki karbata, ga damuwar abubuwa da yawa suna rufe ni, na rasa me ke min dadi Har yanzu babu labarin Aysha? Babu, kuma yau Ammy ya tabbatar min ba zata yafe min ba, sai Aysha ta yafe min, ban san inda zan ga Aysha ba Bana jin fa tana raye, domin da tana raye neman da ka yi mata da yadda aka zuba kudi da yanzu an gane ta, ni ma ta gurina ba wani labari gaskiya, ina ganin abun da zai fi, ka koma nan da kwana biyu idan na duba time da ya fi sai ka dawo muje tare mu samu Ammy mu rarrasheta wata kila zata yafe maka Abu ne da kamar wuya, ta hau sosai ta yi fushi Aliyu Karka karaya, za mu samu kanta In Sha Allahu, ba wai mu kadai zamu tafi ba sai mun gayyaci mutane, ka yi magana da amininka ku tattauna idan kun yi shawara da kuke ganin ya kamata mu shigo ciki sai mu shiga Toh Allah yasa ta yafe min, ko da ya yafe min dole zan cigaba da neman Aysha, ina da bukatar ganinta ina son ganin... Yayi shiru be karasa ba. I will call you Back Okay ALIYU POV. Ya sauke wayar tare da bude bakinsa ya karbi plantain din da Sultana take kai masa baki. Uhmm so kike cikina ya fashe ko? Ta yi dariya tana jan hancinsa. Eh so nake cikinka yayi kato kamar nawa Ya saka wayar aljihu ya kai hannunsa ya shafa cikin nata. Ai da ba zaki zauna da ni ba, amman yanzu saboda kin ga saurayi kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa shiyasa kike zaune da ni Ta bude baki. Sai kace ba ni na saka ka yi kyaun ba, kamin na aure ka ai baka da kiba amman ina aurenka ka yi kiba ka kara kyau Ya zagaye cikinta da hannayensa. Ke ma dai kin ce na kara kyau, that's mean ina da kyau tun farko shiyasa kika rude kika ce ke sai ni Ta kai masa yatsina a fuska har sai da ya matsa baya yana dariya. See this girl Zaka yi latti fa, ka tafi ko na kira Momy na fada mata Sai nace mata ke kika rike ni kika hana ni tafiya aikin, kin ga idan ta min fada sai na rama akanki Juyar da shi ta yi ta fara turashi har sai da ya fita daga falon dan dolensa. Ni da gidana a rika korata Ka dame ni ne, and Point of correction gidana ne ba naka ba Dawowa yayi kusa da ita ya sumbance ta ya shafa cikinta. I Love you, sai na dawo ayi min addu'a mai ciki A take ta kai masa rankwashi akai sai ya zuba da gudu gurin motarsa yana dariya Allah ya kiyaye ya tsare min kai, dan kyakkyawana Amin yar kyakkyawata Ya dago mata hannu ta daga masa sannan ya shiga motar yayi addu'a yayi mata key yayi horn mai gadin da ya kasance inyamuri ya bude masa gate ya fice, zuciyarsa cike da so da kaunar matarsa. ____________________ Share fagen sabuwar tafiyar kenan. Da fatar zaku karbe shi da hannu biyu. Khadeeja Candy... +2348036126660 A hankali ta tura kofar dakin da danta yake ta shiga sautin dariyarsa ya saka ta farinciki tun kamin da karasa gurin da yake zaune. Vito ya juyo ya kalleta ko kadan babu murmushi a fuskarsa sai ka rantse da Allah ba shi ne yake yi ma London din wasa ba yana dariya. Kallonta yake har ta karaso kusa da shi gurin da danta yake zaune, ta rage tsaye ta kai hannu ta shafa fuskar danta, shi kuma ya kai hannu zai shafa fuskarta sai ta kauce ta yi saurin mikewa tsaye, a nan ma da kallo ya bi ta, wani irin so yake mata wanda ba zai iya dorashi a mizanin awo ba. Karfe nawa zaki dawo? Ta kalli agogon hannuna. Ban sani ba, sai idan na tafi Karki zauna da yunwa idan babu abinci a can ki fada min zan aiko a kawo miki Ta kalleshi kawai ta dauke kai sannan ta sakarwa danta murmushi, ta sake rage tsayinta tana kallon danta. London zan fara fita aiki yau, zan wuni ba a gida ba, kai kuma zaka wuni da Chidimma your Nanny... Bata rufe baki ba ya girgiza mata kai ya bata fuska zai yi kuka. Ni bana son zama a tare da Chidimma ina son zama tare da Uncle Vito Ta saka hannayenta biyu ta rike fuskarsa tana masa magana a hankali, domin karami abu ne ya birkice mata a take. Uncle Vito zai fita yana da aiki, amman idan na dawo.... Zan zauna tare da shi Vito ya amsa mata yana kallon gefen fuskarta. Ba tare da ta kalleshi ba ta ce. Amman kana da gurin zuwa Ba karamin abu ba ne London ya sake jiki da mutum, ya fara cewar baya son zama gurin Nannynsa so let him be with me, ko kuma ke ki fasa tafiya aikin ki kula da shi Ta cire hannunta daga jikin danta ta mike tsaye Ka zauna da shi ni zan tafi Ta juya ta nufi kofar dakin ta bude ta fice, da kuzari ta fito cikin gidan ta nufi gate mai gadi ya bude mata ta fice. Tafiya sosai ta yi sannan ta samu taxi ta shiga sai da ta zauna sannan ta fada masa gurin da zai kaita. Direban ya saka sauti mai dadi yayi kasa da volume din yana tukin a hankali. Idanuwanta ta maida gefen titin tana kallon hanya da ababen hawa da kuma shagunan suka yi ma hanyar ado, sai dai gaba daya hankalinta yana wata duniyar da ta kasa mantawa da mutanen cikin da kuma rayuwar da ta yi a ciki. Idan baki iya larabci ba karki gwada, ba a nigeria kike ba, al'adunmu sun shan banban, saboda haka bana son ki yi magana har zuwa lokacin da zaki koma gida, zan sanarwa kowa cewar ke kurma ce Saboda me? Saboda bana son kowa ya san wani abu a tsakaninmu, addininmu da na ki ya shabanban, ina da daraja mai girma a nan, ni dan sarauta ne jinin sarauta, ina da iyali da rayuwa a nan Ni ma musulma ce ai a yanzu Kowa ya ganki ya ji muryarki ya san