Sashe 149
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* Page 6 Mama Baraka ta gabatar mata da yaranta suka gaisa da Emily suka rumgumeta. Emily ta zauna tana hawaye. "A tsawon rayuwata, na yi ta ne ni kadai, idan na hango wani mai dangi ko iyaye sai abun ya burge ni, saboda na yi tunanin ni ba ni da kowa, ba uwa ba uba ba yan'uwa ban san yadda ake ji ba, amman hakika iyali suna da dadi" Dr A-B ya kai hannunsa ya rika nata. "Wani lokacin kaddarori sukan faru da mu, wadanda ba mu isa mu canja komai daga karesu ba, idan ka hango wani yana rayuwa mai kyau sai ka ji ina ma kai ne, idan kuma wani yana rayuwa marar dadi sai ka ji dadi da ya kasance ba kai ba ne, hakan yana nuna mana ba mu da ikon canja komai daga kaddarar mu, domin da za mu iya da mun zama irin wadancan da su ke burge mu, tun da ba za mu iya ba, ai sai mu yi hakuri mu da yadda muka samu kan mu, abun da duk ba zaka iya canja shi daga halitta ko kaddara halayya ba toh be kamata ya zama abun damuwa ba" Emily ta daga mai tare da kai dayan hannunta ta rike hannunsa daya da duka hannayenta, ita kadai ta san me take ji lokacin da bata da kowa, haka kuma a yanzu ita kadai ta san yadda take ji da ta samu yan'uwa. "Na san idan Daddy ya ganki zai yi farinciki domin ko yayansa da suke can ba su yi kama da shi sosai kamar yadda ke kike kama ba, kuma mutum ne mai son yara, na kan ziyarce once in a while" Ta yi murmushi ta sauke kai kasa tare da kai hannunta daya ta share hawayenta, jin an taba kofar falon ya saka ta dago ta kalli kofar sai suka yi ido hudu da Turhan, murmushin dake fuskarta ya gushe ta kalli Mama Baraka dake zaune, sai Mama Baraka ta girgiza mata kai ta juya ta kalli Turhan da ya tunkaro inda Emily take zaune, idonsa a kanta zuciyarsa na bugawa ganin hannun Emily cikin na Dr A-B. "Ban ce ya zo ba, ban san da zuwansa ba, yana zuwa nan mu yi magana amman yau ban fada masa zaki zo ba, kuma ba saboda shi na shirya wannan ba, na shirya miki wannan liyafar ne saboda ina sha'awar ki zo kusa da ni, kuma ina nufin baki mamaki da Dr A-B ne, ba Turhan ba" Mama Baraka ta fada cike da tsoron batawa Emily rai. "Ni na ce ya zo" Emily ta kalli Dr A-B. "Ya kamata mu zama masu yafiya Emily, dukanmu muna laifi wa junanmu, kuma akan daga mana kafa a yafe mana, na san abun da ya aikata be kyauta ba, kin ba mu labari, shi ma kuma ya maimaita min cikin nadama, kusan shi ne dalilin zuwa ba wai domin Madam Baraka kawai ba" Emily ya maida kanta kasa tana jin kamar suna son mata dole ne. Dr A-B ya matsa kusa da ita yana mata magana a hankali yadda zata fahimta. Turhan ya zauna a kujerar dake fuskantarsu yana maida numfashi da karfi, be tana sanin yana kishin Emily har haka ba sai a yau da wani wanda ba Aliyu ba ya zauna kusa da ita kuma ya rike hannunta, saukin abun ma tana da alaka ta jini da shi, da ba haka ba wata kila na zai iya zama ya kalli wani yana kallar masa mata har ya rika hannunta ba. "Ni ma na ba shi rashin gaskiya na abun da yayi, kuma ya karba ya nuna min ya fada min kuma na ga hakan cewar yayi nadama, ban fadawa Madam Baraka ba, amman ya fita matsawa na zo saboda yana ganin ina da alaka da ke kamar idan na saka baki zaki iya yafe masa" "Na yafe masa ai, na fadawa Ammy tun satin da ya wuce, komai ya wuce yanzu gaba nake hari" Dr A-B yayi murmushi. "Haka nake so, daman na san baki da wahalar sha'ani, na gode" Turhan yayi murmushi, Dr A-B ya daga ya kalleshi. "Ka yi farar dabara da ka biyo ta gurina gashi ya yafe maka" "Na jidadin hakan, kuma ina son na kora da bayanin yadda aka yi na san Dr AB dan'uwanki ne, na biyo ta bangaren Mama ne, na fada mata komai kuma na roki yafiyarta na roki ta nema min taki, sai ya zama ita ma tana jin tsoro, hakan ya saka na yi kamun kafa da Dr Adam bayan Mama ta fada min komai na rayuwarki, Congratulations Aisha yanzu komai ya samu, ina miki murna" Emily ta kalleshi kawai ta dauke kai. Emily bata sake sakewa ba a falon saboda Turhan yana ciki, not because of bata yafe masa ba, ta yafe masa har zuciyarta sai dai ta kasa jin walwala saboda yana kusa da ita, idonsa akan duk wani motsi nata. Da suka hadu dinning gurin cin abinci Turhan ya zauna saitin da Emily take, abincin kadan ya ci, Emily ma kadan ta ci tana murmushin dole. "A yanzu nan zaki zauna ne?" Dr A-B ya tambaya. "Aa ina zama gurin Ummi ne" Ya dan tabe baki. "Haka Madam Baraka ta fada min, gidansu wannan yaron ko?" Emily ta kalleshi tana murmushi "Aliyu ba yaro ba ne" "Yayi kamar ni?" "Aa amman dai ba yaro ba ne" "Okay, idan kina zon zama can ba laifi, amman dai ki kula da kanki" "I will" Ta aje spoon ta mike tsaye. "Zan shiga bandaki" "Muje na nuna miki" Daya daga cikin yaran Mama Baraka ta fada, ba musu Emily ta bita zuwa sama ta nuna mata bandakinsu sannan ta fito. Emily na shiga ta maida kofar dakin ta rufe ta jingina ta busar da numfashi. "It's okay Emily, that's how life is komai ya wuce, Turhan shi ne uban yarki, na zaki iya canja wannan ba, dole alaka zata shiga, akan yarsa kawai ba akanki ba, yanzu komai ya wuce" Ta fadawa kanka da nufin karfafawa kanta guiwa, sannan taja numfashi ta sauke har sau uku ta bude kofar ta fito. Ta sauko sai ta zauna a sitting room bata koma dinning din ba, ba su san ta sauko ba sai da suka gama cin abinci suka taso. Sai kuma ga Mahaifin Kameela ya shigo cikin sakin fuska ya mikawa Dr A-B hannu suka gaisa. "Ban san ka zo ba, sai da muka yi waya da Mai gida yake tambayar ya ka sauka kuma an mata tarba mai kyau" "Tafiya ce ta gaggauwa shiyasa ban fadawa kowa ba, shi ma ya sani ne saboda wasu dalilai, na zo ne saboda kanwata Emily fatan na same ku lafiya" "Alhamdulillah, muna maka maraba da zuwa, mu shiga ka gaisa da sauran yan gidan mana" Mahaifin Kameela ya rike hannun Dr A-B suka fita falon suna magana ya shiga da shi bangarensu Kameela ya gaisa da su da sauran yaransa, yayi hakan ne saboda Dr A-B da duk sauran business partners dinsa ba su san Hajiya ba, Mama Baraka aka sani da ita yake yawo, a yanzu kuma basa tare. Da suka fita sai ya zama falon daga Mama Baraka sai Misra second born dinta after Emily, and Turhan. Mama Baraka sai jan Emily take da hira sama sama a kasan zuciyarta kuma bata jidadin abun da mijinta yayi ba, domin da ya shigo be kalleta ba balle yayi ma Emily yayi magana, ko da yake a yanzu ba zata kira shi da mijinta ba sai dai uban yayanta. Turhan kan idonsa na kan Emily wani irin kallo yake mata da ya tafi da hankalinsa ya kusa hango masa yadda jini yake yawo a jikinta. Emily ta mike tsaye. "Bari na jira Dr a waje" Mama Baraka ta kalleta. "Ba a nan zaki kwana ba" "Aa maybe wata rana amman ba yau ba" Turhan ya bita da kallo har ta fice falon sannan ya kalli Misra dake kallonsa ya kalli Mama Baraka ya ciro wayarsa ya shiga tabawa. Da Emily ta gaji da tsayuwa sai ta fita gaban gate din bangaren Mama Baraka tana kallon katon gidan, hakan yayi daidai da fitowar Dr A-B bangarensu Kameela suna tafe Alhaji na masa hira, Kameela da yan'uwata da kuma Hajiya suna tsaye jikin gate din bangarensu. Alhaji be karaso ba ya tsaya nesa da bangaren Mama Baraka, Dr A-B ya karasa shi kadai ya kama hannun Emily da bata san Turhan na tsaye bayanta ba domin nata idanuwan suna gurin Kameela dake aiko mata da wani kallo mai cike da tsana da kiyayya. "Ka dawo" Mama Baraka da fitowarta kenan ta fada. "Eh zan wuce yanzu, mun gaisa da su, ashe kina da co-wife ban taba sani ba sai yau" Mama Baraka ta yi murmushi. "Ka ga zuwan ai yayi amfani, daman ba ni kadai ba ce mu biyu ne ita ce uwargida" "Maa Shaa Allah, Emily a nan zan barki ne ko kuma zaki raka ni Airport?" "Zan raka ka Airport" "Okay" Ya mikawa Mama Baraka hannu. "Thank you so much Madam Baraka i appreciate everything" Mama Baraka ta gaisa da shi, kusan abu nw da ya sana shaking hands da kowa. Sannan ya dafa kafadar Emily to him ita ce kadai yar'uwa ta jini da yake da a kusa a yanzu yana jin muhimamcinta fiye da baya. Tare suka nufi mota ya bude mata gidan baya ta shiga shi ma ya shiga yana dagawa Alhaji hannu. Mama Baraka ta shiga dayar motarta tare da Misra. Kameela ta bisu da kallo har motocin suka fice zuciyarta kamar zata fashe saboda bakinciki. "Hmmm, wai ni aka zo a nuna bakinciki, ga mijinta a gafe ta hada da nawa Aliyu ta zabi wanda take so ko? Ga wani yayanta wai shi mai kudi, ga ubanta bature, ga ta kyakkyawa arziki na daya ma ba da aure aka haife ta ba, da yanzu ina zan kai bakinciki nan? Ga Mama Baraka tana kishi da uwata, diyarta kuma ta karbe min miji, ta hada da nata, wannan bakinciki da me yayi kama? Shekarar nan idan ba so ake na haukace ba me ake so na yi?" Ta fada cikin kuka bayan mahaifinta ya bar gurin. "Ke yanzu miye hadinki