Sashe 129
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 WATTPAD https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy Page 5 Jirginsu na sauka mutumen dake kusa da ita ya kalleta ya ce "Ki biyo ni zan miki ragora, Dr A-B ne yace a kula da ke" Ta kalle shi sai, tun da ta zauna yake a gurin amman be ce mata komai ba sai a yanzu. Yana tashi ita ma ta tashi ta bi bayansa duk inda ya shiga tana biye da shi har suka isa gurin motar da aka kawo, sai ya bude mata baya ta shiga shi kuma ya shiga gaba ya shiga ya rufe aka ja motar, Emily dai na zaune shiru har suka isa unguwar manyan mutane, ba ka ganin komai sai gine gine daga hawa biyu sai uku sai ka tona zaka ga mai hawa daya. Gaban wani katafaren gida direban motar ya tsaya yayi horn security ya bude masa gate, gida ne babba sosai mai dauke da gini mai kyau na burgewa ga shuke shuke ta ko'ina amman ko kadan hankalin Emily be kai can ba saboda tunanin yana wani gurin dabam, direban na fakawa aka bude gefen da take data dago kai sai ta yi arba da Dr AB fuskarta dauke da murmushi ya miko mata hannu. 'Haka rayuwa take tafiya da ni? Daga wannan sai wacan?' a tambayi kanta tana kallon hannunsa kamin ta mika masa nata hannun ta rika shi ta fito motar. Tsaya ta yi a gabansa yana ta kallon fuskarta zuwa cikin idonta, kallon karantar damuwarta ne yake, idonta ya nuna alamar bata samu bachi ba, fuskarta kuma na nuna alamar damuwa, sukuku kamar wanda aka yi ma mutuwa. "How are you Emily" Ta daga kafadunta ta tabe baki kadan kamar mai son fashewa da kuka. "Na shiga damuwa, komai ya chabe min" "Is okay" Ya rika hannunta yaja ta tafiya mai nisa sannan suka isa entrance din shiga falon ya taka yana rike da ita ya tura kofar falon ya shiga yana janye da hannunta, falo ne babba mai dauke da kawa da abubuwan burgewa amman Emily bata kula komai ba, ita dai tana biye da shi har suka haura sama hawa na farko ya tura wani daki ya shiga da ita, da kansa ya zaunar da ita kan gadon dake dakin. "Nan ne dakinki, akwai bandaki ki shiga ki yi wanka wardrobe tana cike da tufafi ki saka marar nauyi, za a kawo miki herbal tea ki sha, kamin ki ci abinci, zan tafi asibiti ana jirana daman saboda ke na dawo" Ya mike tsaye ya dauke hannayensa daga kan kafadunsa. "Na gode" Ta furta, sai ya juyo ya kalleta cike da tausayi be ce komai ba ya fice daga dakin. Kwantawa ta yi akan gadon tana tunanin duk wani abu da ya faru da ita na farinciki wata rana da ta yi farinciki sai fa Emily ta tuna ta a ranar sai gata tana murmushi da hawaye, can kuma ta kai hannunta ta murza wuyan hannun tana tuna agogon da Aliyu ya bata ko a ina ta jefar da shi bata sani ba. Ta mike tsaye ta share hawayenta ta shiga bandakin ta tube tufafin jikinta ta kunna shower ta zauna a kasa ruwan yana dukanta ta rufe ido tana maida numfashi a hankali. Ta dade a haka sannan ta yi wanka har kanta sai da ta wanke sosai sannan ta fito daure da tawul ta bude wardrobe din ta cire doguwar riga mai yalwa marar nauyi ta saka. Wata Cristian maid ce ta shigo sanye da short skirt da bakar riga ta kawo mata tea, daga baya kuma ta shigo mata da abinci da ruwa. Emily ta dauki tea ta shanye ta zauna bakin gadon tana jin ina ma bata jefar da wayarta ba da ta kalli hoton yarta ko zata ji sanyi. Bata ankaro ba ta fara jin bachi sai ta kwanta tana lumshe ido da hamma kamin kace me bachi yayi gaba da ita. Bachi ta yi sosai na tsawon awa hudu ko da ta farka yamma ta yi sosai. Tashi ta yi zaune tana murza ido madadin ciwon kan ya sauka sai ta ji ya karu, ta sauko da kafafuwanta kasa kenan AB ya turo kofar dakin ya shigo rike da leda, ya zauna kusa da ita. "How are you feeling now?" "Kaina yana ciwo sosai" "Yeah saboda kin kwanta da tunani ne, kuma bachin be isheki yadda ya kamata ba, amman ga magani zaki ji sauki" Ya bude ya dauki wani sabon Water bottle da aka kawo mata ta bude ta dauki cup din ya zuba ruwa ya balla maganin ya mika mata ta karba ta sha tare da ruwa, sannan ya bude sabon abincin da aka kawo mata tana bachi ya zuba mata kadan ta sauka kasa ta zauna ta ci, bayan ta gama ya sake bata wani maganin. "Ki wake shiga ki yi wanka, amman da ruwan normal ba mai dumi ba kuma ba mai sanyi ba, za a sake kawo tea anjima ki sha, zuwa gobe da safe idan kin huta stressed din ya rage sai ki gaisa da Momy" Ta daga mishi kai, ya mike tsaye ya kunna tv dake dakin ya kama channel din dake nuna abubuwan ban dariya, ya rage sanyin ac sannan ya kalleta ya sakar mata murmushi ya fice, ta bishi da kallo tana mamakin yanzu shi baya cikin wata damuwa shi sam be san wani abu damuwa ko rashi ba, ba kamar ita ba dake da tarin matsaloli. Yadda ya fada mata haka ta yi bayan ta gama ta zauna tana kallon tv sama sama bayan magari aka kawo mata fruit sai madara da ruwa ta ci fruit din rabin plate sannan da shanye madarar da bata da yawa, after like one awa aka shigo mata da tea ta shanye, nan ma babu jimawa ta yi bachi. Sai tara ya shigo dakin ya kashe tv ya lullube ta ya rage hasken dakin sannan ya fita. Washe gari kamin kowa ya shigo dakin shi ya fara shigowa sanye da kayan bachi, shigowar shi ce ta tasheta daga bachi ta farka. "Good Morning" Ya fada da murmushi a fuskarsa sai ta murza idon ta tashi zaune. Ya zauna kusa da ita. "How are you feeling now?" "Much better" "Kan yana ciwo?" Ta girgiza kai. "Good, me kike so for breakfast?" "wannan tea din ina son na yi bachi" "Zaki yi bachi, ana bin ka'ida ne ba a son bachin yayi yawa ne, kina cin kwai? Domin shi ne best abun da nake son ci da safe kwai sai tea" Ta daga kafadunta. "Okay, za akawo miki amman yanzu ki fara shan maganin nan" Ya dauko maganin ya bata kamar dai jiya ta karba ta sha. "idan kin karya ki sha irin wanda na baki jiya, zan fita aiki kin san bama samun zama, ina son ko da zan dawo na same ki kin shirya sai ki haura sama ki gaisa da Momy" Ta daga mishi kai. "Na gode" When ever she says ta gode sai ya ji zuciyarsa ta tsinke. Ita kuma tana jin ita din ba dole ne a kula da ita ba, domin mahaifiyar data haife ta ma ta jefar da ita, duk wanda zai ganta ya taimaka mata ya cancanci godiya a gareta. "Idan na dawo zamu gaishe da Momy karki manta" Ta daga mishi kai, sai ya ja kumatunta yana murmushi ya mike tsaye ya fice. Be dawo ba sai after ta yi lunch sannan ya shigo da ice cream da chocolate ya kawo mata, sai da ta ci sannan ya riko hannunta suka fito, ta yi zaton kasa za su sauka sai ta ga sun haura hawa na biyu a nan ma wata duniyar ce mai zaman kanta, wani apartment ne guda mai dauke da komai daya yafi na kasa kyau da tsari, banbancin falon kasa ya fi fadi da yalwa ma sama kuma ba wani mai girma ne sosai ba, falo ne har biyu ga kuma dakuna da suke cikin falon, ta cikin falon akwai view din falon kasa da kuma gefe dayan gefen kuma harabar gidan ce. Ko'ina na view din glass ne da manyan curtains da aka sako aka bude su da wadi sosai iska na kadawa, dama da falon kuma wani center ce mai dauke da books ga chairs na zama, dayan gefen kuma dinning area ne an yi shi sama kadan sai ka tara stairs biyar sannan ka hau guri. Ga wani katon Tv mai kamar majigi, ta ko'ina sanyi ke bugowa, ya zaunar da ita kan kujera sannan ya shiga one of the bedrooms da suke falon babu jimawa ya fito tare da wata mace da gani daya Emily ta yi mata ta gane wacece. "Barka da zuwa gidanmu" Emily ta mike tsaye, matar ma kallon Emily take har ta zauna tana sanye da short gown da sarkar cross a wuyanta, AB ya zauna kusa da ita. "Zauna mana, ni sai nake ganin kamar na san fuskarki" Emily ta zauna tana rike da hannayenta. "Mun taba haduwa wata rana a Sudan, ke kika zo da ni Nigeria" Da mamaki matar ta sake kallon Emily. "Anyi haka, ke ce? Wannan baiwar da aka ba ni sadaka?" Emily ta daga kai, AB kuma ya shiga rudani. "Kun taba haduwa?" "Yeah, kai ya ka hadu da ita?" Ya fada mata, sai ta kalli Emily tace. "Meyasa kika gudu a gidan matar da na hada ku?" "Saboda na miki karya a wacan lokaci na fada miki an siyar da ni, ba siyar da ni aka yi ba, wani na aura dan sarki garin shi kuma yaje da ni a matsayin baiwa" "Zan iya saninki? I want to know more about you, why do you lie" Emily ta fara hawaye. "Saboda ba zaki yarda da ni ba idan na fada miki dan gidan nake aure, kuma ba zaki yarda ki taimake ni ba" Dr AB ya kalli mahaifiyarsa. "Momy wannan ba lokacin da ya kamata ayi wannan maganar ba ne please" "Why? Ya kamata mu san wacece ita, saboda ita ka yi ma mijina karya ya bada jirgi aka dauke ta, and because of her ka roki mijina ya kula da duk wani responsible nata tun daga