← Book details Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 177

Sashe 108

Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadeeja Candy* Page 4 Ta isa asibitin ya sauka kan achaba ta biya shi kudinsa ta Emergency ta shiga tana dubawa yawo ta yi bata gane dakin ba domin asibitin babbar Asibiti ce Emergency ma biyu ce ta shiga dayar ta nan ma ta binciki bata gane ba sai da ta sake kiran wayar aka fada mata, sannan ta gane dakin bayan ta isa aka hana ta shiga domin dakin na tsare da jami'an tsoro. A dole ta dawo waje ta zauna ta dafe kanta, duk abun da take Turhan na biye da ita, shi dai be san me ke faruwa ba, be san wa aka kawo ko ta zo gani asibiti ba, kuma be isa ya tunkarenta ya tambaya ba, dan haka ya zauna nesa da inda ba zata ganshi ba yana kallonta. Can kuma ya ga ta fashe da kuka sosai hakan ya karantar da shi ko ma minene abu ne mai muhimmancin sosai a gurinta, karfin hali yayi ya tashi daga inda yake ya taka cikin takunsa na kasaita kamar wanda baya son taka kasa ya karasa inda take zaune tana kukan ya tsaya daga gefenta ya kalli mutanen da suke gurin yana kirga mutane nawa ne, domin ya san Emily zata iya disgashi ya lura gaba daya an hure mata kunne, har ya kalli inda take zaune kamar ya zauna amman ba dama ya san zata iya tashi ta bar shi a gurin. Ya tsaya a gabanta kamar wani hoto ya kalleta ya kalli harabar ya kasaita ta hana shi bude baki ya tambayi me ya saka ta kuka, baya son ta zubar masa da kimarsa just because yana nemanta kuma yana neman gyara abun da ya bata, sai dai kuma tunawa da Fatima ya saka shi kawar da komai, domin samun Fatima a yanzu yana jin Emily ta gama masa komai, ya hade yawu zauna a gurin, jin alamar mutum ya zauna a kusa da ita ya saka ta mike dago kanta daman tun da ya iso gurin ta ji alamar mutum amman bata dago ba sai da ya zauna kusa da ita. Ganin Turhan ne ya saka ta mike tsaye da sauri sai yayi hanzarin mikewa tsaye ya riko hannunta. Juyowar da zata yi sai ta juyo da shirinta na sauke mata yatsunsa biyar na dayan hannun a fuska, yayi hanzarin saka dayan hannun ma ya rike dayan hannun. "Zaki iya marina ki ci mutuncina yadda kike so idan muna daga ni sai ke a guri a gurin da jama'a suke kai da kawo ba, Aisha kin fa san waye ni na san kina jin haushina amman..." Be kai aya ba ta buga masa kanta a hanci ba shiri ya saki hannayenta. "Ya Rabbi ya Allah..." Ya furta yana jin wani gishirin bala'i a hancinsa yana ratsashi har cikin kai, ya kai hannu ya taba hancin nasa har yana huro iska ya ji ko hancin yayi jini, bata tsaya a gurin ba ta kara gaba, bata wani san asibitin ba da tambaya ta isa gurin da ruwa suke ta tara hannunta ta wanke da kasa sannan ta tara hannunta ta dauraye. Turhan na can daga nesa yana kallonta ganin ta wanke hannun ya saka jin wani iri ya kalli hannayensa even though ya san hannunsa are clean. Karfin hali yayi ya karasa gurin da take duke ya tsaya daga bayanta. Duke take a gurin tana ta kuka, abubuwa sun chabe mata a yanzu, Vito yayi fushi har ya cutar da Aliyu, ga Fatima bata hannunta ga shi ta hadu da daya daga cikin manyan makiyinta wato Turhan, Aliyu yana raye ko ya mutu bata sani ba, but no matter what bata so wani abu marar kyau ya samu Aliyu ba, balle kuma ace sanadinta ne. "Ina son na san dalilin kukan ne wata kila zan iya taimaka miki, ki fada min me ya kawo ki nan kuma me ya faru ba dan ni ba sai dan Fatima" Ta runtse ido cike da bacin rai, yanzu kuma ta rasa dalilin wannan mutumen na bibiyarta, da ace tana da iko da ta toshe kunnuwanta daga sauraren muryarsa. Mikewa ta yi tsaye ta juyo ta kalleshi. "Har abada, har kasa ta rufe idona, har duniya ta nade ba zan taba karbar taimako daga gareka ba, balle kuma har na nema, da zaka iya da ka taimakawa kanka ka nisanta kanka daga ni da duk wani abu da ya shafe ni, idan ka aikata hakan rayuwarka zata tsawaita ka cigaba da zalunci da ka sakawa gaba, kuma saka ceto kanka daga wulakanci, idan akwai muryar da na tsani ji kamar mutuwata to taka ce, idan akwai fuskar da zan iya kwakwale idanuwana na zubar da su saboda kyamar kallonta to taka ce, idan kana kallon Fatima a wani tsanin hawa to ka yi kuskure domin Fatima bata da uba, ko a tsintuwa ta zo ba zata taba zabarka a matsayin uba ba, mutumen da ya kalli uwarta ya aibanta surarta, ya kaskantar da ita a matsayin baiwa a fadar da ya kamata ace an girmamata, ya kira ranar auren uwarta da bakar rana, ya kira ranar da ya kebe da uwarta har aka samu cikinta da bakar rana, ya fadi cewar ba zai taba son abun da ta haifa ba, ya watsa mata yawu a fuska, wai duk saboda kawai ta aure shi dan ta farantawa uwarsa rai, ya kira uwarta da tubabbiya, ya kira dan'uwanta da shege yana musa cewar ta sunna aka same shi, ya bar uwarta ta wahala a titi ta haife ta a titi ta raine ta a titi kuma yana raye yana da hali da Ikon da zai iya kula da yarsa, ya juya mata baya sai a yanzu da yarinya ta yi wayo zai dawo yace shi ne ubanta? Yarinyar da na gina rayuwarta da tsanarka? Yarinyar da bata taba yarda ta zo duniya da uba ba? Kai kan wane irin mahaukaci ne? Har kana da idon da zaka kalli Fatima ka fada mata kai ubanta ne? Allah ya waddaran namiji irinka, Allah ya kwashewa rayuwarka Albarka, ka yi hasara" Kallonta yake kallon da ya hango tsanarsa a cikin idanuwanta ya karantar da shi kiyayyarsa a cikin kalamanta da muryarta, ta tuna masa da abubuwan da ya manta kuma yake ganin kamar ba komai ba ne, ta yi gaskiya shi din be cancani ya kalli Fatima ya fada mata shi din ubanta ne ba, amman hakan ba zai karya guiwarsa ba domin komai ya faru ne saboda rashin sanin inda take da kuma cikin da take dauke shi. Ya bi bayanta da kallo ganin rashin dacewar tufafin dake jikinta. A sanyaye ya juya ya nufi gurin da ya aje motarsa ya shiga ya zauna kalamanta na ta yi masa yawo a cikin kai. Be kyauta ba ya sani, kuma ya zafafa da yawa a yanzu ya gane hakan, kuma ya fahimci kirjinta ya cika da tsanarsa da kiyayyarsa tana ina ma zai fara gyara abun da ya bata, tun da bata ba shi hadin kai, kamata yayi ace Aliyu yayi masa wannan yakin tun kamin ranar yau wata kila da abubuwa sun zo masa da sauki, tun da gashi ya san har da ya a tsakanin su amman be masa ba sai ma kokarin boye masa yake yana munafurtarsa, a yanzu ya kara gane Aliyu ba abokin kwarai ba ne, ta ina ma ya gane ta? Ina ya hadu da ita taya suka kulla alaka abu ne da yake bukatar ya sani.. Ya dauki wayarsa ya kira layi Ammy ta amsa kiran ya gaisheta ta amsa, kasancewarta uwa sai ta fahimcin canjin muryar danta ta yanayin yadda yake amsa mata magana alamar akwai abu a kasan halshensa. "Ammy ina Fatima?" "Tana can falo tana cin abinci, daker ma na samu take cin abincin, babu wanda take kira sai Aliyu da Aisha, gaba daya ta ki yarda da mu, na fada mata ni ina matsayin kakarta ne amman ta ki karbar hakan tace mahaifiyarta bata da kowa, ita kuma bata da uba, ban san yadda zan yi na fada mata kai ubanta ba ne, Turhan ka lalata abubuwa da yawa" Ya sauke ajiyar zuciya yana taba hancinsa da har yanzu yake masa ciwo. "Na sani Ammy zan yi kokarin gyarawa kamar yadda kika ce, ba za su karbe ni da sauki ba amman zan... Zan jure wajen ganin komai ya tafi daidai, wata kila shiyasa Allah ya kawo ciwon nan naki yasa na zo abubuwan nan suke ta faruwa" "Kana ina? Ina Aisha take?" "Ina asibiti, na kwana a gidan Aliyu jiya saboda ina tsoron kar na tafi tayi tafiyarta ban san inda zan same ta ba, kuma yanzu ta zo asibiti ban san wa take nema ba, amman dai kuka kawai take" "Ka tambaye ta mana" "Ba zata min magana ba, na gwada yin hakan ban dace ba, amman dai ko minene yana da muhimmancin sosai a gurinta domin kuka take sosai kuma hankali a tashe ta zo nan" "Duk yadda zaka iya idan ka gano matsalar ka taimaka mata, kuma ka fada min ta hakan za mu yi ta yakin har mu yi nasara In Shaa Allahu" "Okay" Ya sauke wayar, ya sake fita motar jiki a sanyaye ya fara zagayawa ta asibitin har ya samu inda take zaune ya zauna nesa da inda ba zata ganshi ba yana ta kallonta, ta ya ta canja haka? Ina wacan yaron? Yaushe da bar addinin Musulunci ya yi ma kansa tambayoyin a take, tun yana tsayuwa da dadi har kafafuwansa suka yi tsayi domin yayi awa daya da rabi tsaye a gurin yana ganin Emily, a tsawon awa daya da rabin babu abin da Emily take sai kuka domin jikinta na raya mata ko dai Aliyu ya mutu ko kuma yana cikin mummunan hali bata san me zata yi a yanzu ba. Sau goma sha daya yana yunkurin tafiya ya sameta ya sake tambayarta damuwarta sai kalamanta na dazun su rike masa kafa, sai dai kuka yana jin wani iri kamar dai babu dadi tana kukan ko ba komai kukanta na yanzu yana tuna masa da kukanta da ta yi a wacan lokacin har take rokon ya dawo da ita gida ya ki. Ya shafa kansa yana jin babu dadi, lokuta da dama
Chapter 108 · 0% Book details