Sashe 69
Abokin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... FOLLOW ME ON FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3 ONE WEEK LATER... Ba zata iya musa masa ba, dan haka ta amsa bukatarta ta dora tata bukatar akai. Tun a washe garin wacan ranar ta cigaba da zuwa aikin, sai dai a tsawon zuwan da take bata fada ma Tasmia cewar ta koma aikin ba duk kuwa da irin dukan ruwan cikinta da Tasmia take na son ta ji labarin Aliyu ta, tana yawan tambayarta ya kira ki? Kun yi waya? Emily ta ce mata aa saboda gudun kar Tasmia tace bata dauki shawararta ba, ba kuma dan bata gamsu da shawarar ba, sai dan Tasmia ta bata ba sai dan bata son musawa Aliyu ne. Kusan tun da ta koma aikin bata hadu da Aliyu ba, ko a hanyar shiga Office dinta ko nashi, hakan kuma sai ya kara mata kwarin guiwa da natsuwa, da fari ta yi tunanin ko zai takura mata ne ko dan neman jin karashen labarinta da Turhan, ko kuma ya nemi wani abu a gurinta ko da yake Tasmia ta fada mata bata gama karantarta namiji ba ne, wata kila haka ne wata kila kuma ita din wawuyace shiyasa ta kasa son mai sonta tsakani da Allah, amman kuma idan bata so Vito ba wa zata so? Ai bata isa ta bude zuciyarta ga wani ba. Ta gama saka dankunnenta ta dauki jakarta ta fito tana tafiya a hankali, tun da ta fito Chidimma ta hade rai saboda yadda Vito yake kallonta har ta iso gurin dinning din ta dora jakarta ta fara zubawa kanta abinci. "Good Morning Beautiful" Ta juya ta kalli Chidimma dake kujera biyu kamin tata. Hakan kuma ba karamin bakantawa Vito rai yayi. "Why would I called Chidimma Beautiful?" Chidimma ta ji kamar an tsomata a ruwa tsabar muzantata da yayi agaban Emily, ba kuma dan bata da kyaun ba, sai dan a gurinshi babu wata mace mai kyau sai Emily. Emily ta kalleshi. "Because she is pretty, isn't she?" Ta fada tana kai abinci a bakinta, da ido Vito yayi ma Chidimma magana sai ta tashi ta dauke abincinta ta bar dinning din. Ya dora hannayensa kan dinning din "Miyasa kike tunanin zan ga kyaun wata mace idan kina nan?" "Da bata da kyau ai ba zaka sakata a matsayina har ka ci abinci a teburi daya da ita ba, har ka nemi ta dafa maka abinci, ko ba haka ba VITO" Ta ambaci sunansa da babban baki, madadin yaji haushi sai yayi murmushi, bukatarsa ta biya daman makasudin yin hakan saboda ya gani idan zata ji kishi ne, idan har ta ji kishin hakan ya nuna tana son shi kenan. Ya jimgina da kujerar dinning din yana cigaba da kallonta, kamin ya ciro wayarwa dake vibration ya duba sannan ya amsa kiran. Yayi shiru na dakiku yanayin fuskarsa ya sauya zuwa bacin rai. "Ganin nan zuwa" Ya mike tsaye sai ta kalleshi tana kai lemu a bakinta. "An sake kama kayanka ne?" Har yayi gaba sai kuma ya juya ya kalleta. "Nope wani ne yake wasa da rayuwarsa, someone set me up" Ta aje glass cup din. "Me kake nufi?" "NDLEA aka turo su bincike gidana daga Abuja" Ta mike tsaya da sauri ta karasa inda yake tsaye. "Kuma zaka tafi" "Yes ina bukatar na tafi" "Aa karka je dan Allah bamu san manufarsu ba, gashi kana da saurin fushi ba mu san abun da zai faru ba" Ya shafa fuskarta. "Babu abun da zai faru" Ta rike hannunsa tana girgiza masa kai idonta har ya fara tara hawaye. "Ya kamata na tafi ko dan na nunawa wanda ya turo su wanene ni" "Be zama lallai turowasu aka yi ba, sana'ar da kake yi ba mai kyau bace kana jefa rayuwarka be kawai cikin hadari, daman dole wata rana za a iya bincike za a iya ganeka" Tana maganar tana kuka jikinta na rawa gaba daya ta tsorata. "Set up ne, NDLEA da suke da nan ko jami'an tsoron duk mutanenmu ne, shiyasa ba ayi amfani da su ba aka turo baki daga Abuja, amman ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru" Ta girgiza kai. "Aa karka je" "Dole sai na tafi ai, suna bukatar ganina" "Kace musu baka nan" "Ina nan" Ya amsa mata yana kai hannanyensa ya rika fuskarta. "Toh ka aje bindigarka karka je da ita" "Zata min amfani" "Idan zaka je da bindiga ba zan bari ka tafi ba" Ta rumgume shi tana kuka, sai yayi murmushi ya dago ta daga jikinsa. "Ba zan je da ita ba" Ta fara lalaben aljihunsa. "No idan kika taba zata samu shatin hannunki, idan na aikata wani laifi da ita aka yi bincike za a samu shattin hannunki kai, ba ni bukatar haka" Ya cire bindigar da kansa ya nufi Kitchen ya dauko wata madaidaiciyar cooler ya saka bindigar ciki sannan ya fito rike da wuka ya nufi gurin da Swimming pool dinta yake yayi gina a inda kasa take ya saka cooler ya rufe sannan ya janyo daya daga cikin kujerar da suke aje a gurin ya dora a sama, sannan ya kalleta ya ce. "Ko da bincike ya biyo ta nan baki da matsala babu wanda zai san da wannan you're safe" Ya rika hannunta ya jimke ya saki sannan ya fice daga gurin zuwa gurin motarsa. Biyo shi ta yi ta tsaya tana kallonsa cikin tsoro da tashin hankali, shikam damuwa data nuna masa a yanzu ta gusar masa da duk wani bacin rai da ya ji a lokacin da aka sanar da shi abun da yake faruwa a gidansa. Dawowa ta yi falon ta doshi gurin da jakarta take ta bude ta dauko wayarta, number Aliyu ta fara kira domin shi zuciyarta ta raya mata, wayar ta yi ringing har ta katse be daga ba, ta sake kiransa be daga ba ta sake kira be daga ba, sai da ta jera masa miss calls kusan tara sannan ta maida wayar ta dauki jakarta ta fice daga gidan zuwa gurin aikinta cause she want to see him badly... ALIYU POV. Tana kallon yadda ya saka wayar da ake ta kira tun dazun a aljihu ya ki ya amsa kiran sai ma saka wayar da yayi a silent kuma ya ki ya aje a inda zata ga sunan mai kiran zuciyarta ta raya mata ba kalau ba, amman bata nuna masa ba da ya gama saka turare ta mika masa agogon da ke aje, ya karba ya fara sakawa. "Yaushe ka siya agogon nan Honey?" "Wannan agogon ina da shi, bata yayi sai yanzu na ganshi" "Da alama yana da muhimmanci a gareka kusan tun da na dawo kullum shi kake sakawa idan zaka je aiki" Ya kalleta da dan mamakinsa domin be yi zaton ta maida hankali a gurin ba. "Toh har kin saka min ido kenan, yana da tsada ne shiyasa duk wanda zai gan ni da shi zai san babban agogo ne" "Hmmm" Ta furta sannan ta mike tsaye ya kama hannunta suka fito seating room, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna ya ciro wayarsa gudun ya zaune ta domin ya sakata aljihun bayan wandonsa ne, sai ya ci karo da sakon Emily. "Na zo baka shigo ba, ka yi sauri ka shigo akwai matsala" A take ya mike tsaye ya fasa cin abincin Kameela ta daga kai tana kallonsa. "Lafiya" "Lafiya kalau, wani uzuri ne ya taso zan tafi Office yanzu" "Abincin fa" "Ki ci zan samu wani abu a can na ci" Ya sumbance ya sannan ya fice da sauri tana kallonsa. Ya shiga motar sa yana karanto addu'o'i yana tukin har ya isa gurin aikin, kusan al'adarsa karanta addu'a idan ya shiga motar da safe, ya faka a inda ya saba fakawa ya fito ya nufi cikin ma'aikatar, sai da yayi kamar ya fara shiga office din Emily saboda ta fada masa akwai matsala sai kuma ya yanke shawarar fara tafiya Office dinsa albashi ita sai ta same shi a can. Ya shiga office dinsa bayan ya gaisa da sakaterinsa Nick ya shiga cikin Office din ya zauna, sannan ya kira wayar Emily bata daga ba, ya sake kira bata daga ba, sai ya aje wayar yana mamakin matsalar me aka samu? Tana office dinta ko kuma ta wuce gida? Ya sake daukar wayar ya sake kiranta bata daga ba, ya sake kira sai ya ji user busy alamar tana waya, wannan karon be aje wayar ba sai da ya tura mata sako cewar ya shigo ta same shi a office dinsa sannan ya aje wayar ya nufi fridge dinsa ya bude ya dauko gorar ruwa ya rufe, ya murda murfin ya bude ya kai gorar bakinsa, juyowar da zai yi sai aka turo kofar Office din aka shigo ya cika bakinsa da ruwa yana kallon Kameela dake sanye da green Hijab har kasa hannunta rike da bracket. Ya hade ruwan yana kallonta da mamaki. "Me kike yi a nan?" "Kana ta sauri ka fita baka yi breakfast, ni kuma hankalina ba zai kwanta ba idan ka wuni da yunwa shiyasa na biyoka da abun karyawa a nan" Ta karasa kusa da shi ta dora bracket din kan teburinsa tana kallonsa da murmushi a fuskarta. "Okay Thank You Dear, amman Baki fada min zaki zo ba, kin san bana son ana fita ba da izinina ba ko?" "Haka ne am sorry" "Me kike hau kika zo nan" "Taxi" Ya dauki wayarsa da nufin turawa Emily sako sai ga Emily ta turo kofar office din ta shigo, daga Aliyu har Kameela juyowa suka yi suna kallon Emily da ta yi tsaye ta kasa karasa inda suke tsaye, Aliyu ya dauke idonsa daga kallon Emily ya kalli Kameela, to his greatest surprise ever sai ganin yayi Kameela na murmushi kamar babu komai. "Karaso mana Emily shigo" Ta fada sannan ta juyo ta kalli Aliyu. "Ashe nan take aiki? Maa Shaa Allah tana da kyau gaskiya" Ta sake duban Emily tana danne wani turnukun fadan ibilisan dake kirjinta. "Toh bari na tafi na barku ku yi aikinku, daman na kawo masa abun karyawa ne, idan ke ma baki karya